Shugabannin PDP sun ba wa hamata iska a Kano
Rikici ya kaure kan zargin bangaren uwar jam’iyyar da shirya cuwa-cuwa a zaben daliget na gundumomin
An ba wa hakamta iska tsakanain wakilan shugabannin jam’iyyar PDP reshen Jihar Kano da kuma wakilan da uwar jam’iyyar ta tura daga Abuja domin gudanar da taron jam’iyyar na jihar.
An ba wa hamata iska tsakanin banganorin ne a otal din Tahir Guest Palace, inda aka sauke daya daga cikin wakilan uwar jam’iyyar ta PDP da ya zo daga Abuja domin gudanar da taron zaben daliget ne gundumomi.
- 2023: Gwamnan Jigawa ya sayi fom din takarar Shugaban Kasa a APC
- Sojoji sun yi raga-raga da sansanonin Boko Haram 24 a Borno
Aminiya ta gano cewa bayan an ba wa hamata iska, ’yan sanda sun yi awon gaba da wakilan shugabancin jam’iyyar a jihar, wato Dahiru Haruna da kuma Idi Zare Rogo.
Shugaban PDP reshen Jihar Kano, Shehu Sagagi, ya shaida wa wakilinmu cewa an yi damben ne bayan shi wakilin uwar jam’iyyar da aka sauke shi a otal din, Barista Ekwudile, ya bukaci abin da zai sha, su kuma Dahiru Haruna da kuma Idi Zare Rogo suka je su sayo mishi.
“Amma da suka dawo dakin sai ba su same shi a ciki ba, sai daga baya suka gano shi a wani daki mai lamba 811, a nan ne rikici ya kaure a tsakaninsu”, inji Sagagi.
Da aka tambaye shi game da musabbabin rikici, Sagagi ya ce ba zai rasa nasaba da mutanen da aka ga ni tare da Barista Ekwudile a dakin ba, wanda ya sa Haruna da Rogo zargin akwai wata kullalliya a kasa.
A cewarsa, shugabancin jam’iyyar ba ya goyon bayan a gudanar da zaben wakilan gundumomi a otal din, sun fi su so a gudanar da shi a ofisoshin jam’iyyar PDP da ke gundumomin.
Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani game da abin da ya faru daga kakakin ’yan sandan Jihar Kano, SP Haruna Kiyawa, amma bai same shi a waya ba.
Amma wakilin namu ya samu bayani cewa an tisa keyar wakilan jam’iyyar ne zuwa babban ofishin ’yan sanda da ke Badawa.