Shugabannin PDP sun fara nuna yatsa kan Atiku da Wike
PDP dai ta shiga rikici tun kafin babban zaɓen 2023.
Shugabannin jam’iyyar adawa ta PDP, sun samu rabuwar kai a Abuja kan wa ya kamata a zarga game da rikicin da ya addabi jam’iyyar.
Jam’iyyar PDP ta shiga tsilla-tsilla tun bayan zaɓen fidda-gwani na shugaban ƙasa, kuma wannan rikici ya taimaka wajen faɗuwar jam’iyyar a babban zaɓen da ya gabata.
- Zaɓen Ƙananan Hukumomi: An girke ’yan sanda 8,000 a Filato
- DAGA LARABA: Da Gaske Ciwon ’Ya Mace Na ’Ya Mace Ne?
A wani taro da masu ruwa da tsaki na jami’yyar suka don nemo mafita a ranar Talata a Abuja, ɗan majalisar wakilai, Ikenga Ugochinyere, ya zargi Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da haifar da matsaloli a jam’iyyar.
Ugochinyere, ya ƙara zargin muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Umar Damagum, da kuma Wike a matsayin matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta.
Amma mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Ibrahim Abdullahi, bai yarda da wannan zargi ba.
Ya zargi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da haddasa rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.
Ya ce, “Kafin a iya gyara matsalolin PDP, dole ne mu fara gyara matsalolin cikin gida, musamman batun shugabanci. Idan ba mu warware wa5dannan matsaloli ba, mutane za su ci gaba da yi mana dariya.”
Ya ƙara da cewa Wike ya haɗa kansa da APC, “Wike ya karɓi aiki domin yi wa APC hidima, don haka mun san inda ya dosa.”
A gefe guda, Abdullahi ya ce shugabancin jami’yyar a yanzu, wanda ke ƙarƙashin Damagum, ba a ƙarƙashin ikon Wike yake ba kamar yadda Ugochinyere ya yi zargi.
Maimakon haka, ya ɗora alhakin matsalolin jami’yyar a kan Atiku,
“Mun gaji waɗannan matsaloli ne. Atiku ya ne kawo gwamnatin Buhari wadda ta fi kowace gwamnati muni kuma ya fice daga jam’iyyar, sai daga baya ya dawo ya domin neman tikitin takara.
’Gwamnoni biyar sun yi barazanar ficewa daga jam’iyyar a lokacin zaɓen da ya gabata, amma Atiku bai yi komai kan lamarin ba. Kwamitin Aiki na Ƙasa (NWC) yana fama da matsalolin da aka bar su a hannunmu.”