Shugabannin siyasa ba sa karbar shawararmu – Sheikh Dahiru Bauchi
Sheikh Dahiru Usman Bauchi jagora ne a Darikar Tijjaniyya , kuma shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), masanin Alkurani da Tafsiri ya jagoranci addu’o’in shiga sabuwar Shekarar Musulunci na Kasa da aka gudanar a Jihar Bauchi. Malamin wanda aka haife shi ranar 2 ga Muharram […]
Sheikh Dahiru Usman Bauchi jagora ne a Darikar Tijjaniyya , kuma shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), masanin Alkurani da Tafsiri ya jagoranci addu’o’in shiga sabuwar Shekarar Musulunci na Kasa da aka gudanar a Jihar Bauchi. Malamin wanda aka haife shi ranar 2 ga Muharram 1346 Bayan Hijira kimanin shekara 95 da suka wuce ya zanta da ’yan jarida kan rayuwarsa da kuma kira ga shugabannin siyasa da su ji tsoron Allah su cika alkawarin su:
Ko za ka ba mu takaitaccen tarihin rayuwarka?
Alhamdulillahi ni Bafulatani ne gaba da baya, dukkan kakannina hudu Fulani ne daga Jihar Bauchi, a lokaci guda kuma mu Fulanin Jihar Gombe ne. Ta wajen mahaifina ni Bafulatanin Jihar Bauchi ne, ta wajen mahaifiyata ni Bafulatanin kauyen Nafada ne da ke Jihar Gombe. An haife ni ranar Laraba 2 ga Al-Muharram 1346 Bayan Hijira wanda ya yi daidai da 28 ga Yunin 1927, Mahaifina sunansa Alhaji Usman dan Alhaji Adamu wanda mahaddacin Alkur’ani ne mutumin kauyen Konkiyel ne Karamar Hukumar Darazo. Na rayu a hannunsa shi ya koya mini karatu har na haddace Alkur’ani. Sunan mahaifiyata Hajiya Maryam Sulaiman mutuniyar Nafada a Jihar Gombe. Bayan na haddace Alkur’ani a hannun mahaifina ne ya tura ni duniya domin in je in gyara tilawata ta Alkur’ani. Na shiga duniya Allah Ya taimake ni na gyara tilawar tawa, lamarin da ya sanya wadansu kan ce mini Gwani na Alkur’ani, wadansu mutanen kuwa kirana suke yi da sunan Gangari a fagen haddar Alkur’ani. Bayan nan sai, mahaifina ya ce zai tura ni duniya in je in sake nemo ilimi, daga nan aka tura ni Bauchi domin neman ilimi. Na fara neman ilimi ban riga na samu ilimin da yawa ba, sai Allah Ya sa Failar Shehu Ibrahim Kaulaha din nan ta bayyana. Dama shi baban nawa dan Tijjaniyya ne Mukaddami ne ta salsalar Umarul Futi, wato Muhammadu Ghali, na soma yin tafsirin Alku’ani ne a wajajen 1950, sannan na yi aurena na farko a 1948. Cikin alherin da Allah Ya yi mini, ’ya’yana tun suna kanana suke haddace Kur’ani. Da farko ’ya’yana suna haddace Kur’ani tun suna ‘yan shekara 11, aka dawo 10, aka zo 9 har ya zamana cewa akwai ’ya’yana da suka haddace Kur’ani suna ’yan shekara bakwai-bakwai da haihuwa. Ina da ’ya’yan da suka haddace Alkur’ani sama da 70, kuma mutum uku ne kawai suka rasu daga cikinsu, wato Dokta Hadi da Ahmad da kuma A’ishatu (Yalwa) wacce ta rasu a hadarin mota a kan hanyar Yola, amma sauran duk suna raye yanzu haka.
Yaya rayuwa ta kasance tsakanin Malam da mutanen da suka taso tare?
Rayuwa dai alhamdulillahi, kusan duk mutanen da muka yi karatu sun rasu, haka ma wadanda suka koya mini karatu duk sun rasu, amma mun yi rayuwa mai albarka da su. Don ka ga yanzu ni da Allah Ya ba tsawon rai cikinsu ina tunkarar shekara 100 ne.
Ko akwai wani abu da Shehi yake so a rayuwa bisa la’akari da shekarunsa?
Duk jin dadin da mutum yake so ya yi a rayuwarsa, idan shekarun mutum suka kai kamar nawa rayuwa kam sai dai lallabawa. Don ina ganin kaina kamar mutum ne da kayansa yake a daure yana jiran motar da za ta dauke shi. Idan lokacin Sallah ya yi ya je ya yi, idan lokacin cin abinci ya yi ya ci, shi dai yana jiran motar da za ta dauke shi, har zuwa lokacin da Allah zai yi hukuncinSa komai naSa ya koma ga Allah baki daya.
Ka ga gwamnatoci daban-daban a kasar nan ko yaya dangantaka take tsakaninka da gwamnatocin da suka gabata da na yanzu?
Na gode wa Allah da Ya yi min tsawon rai don tun lokacin Turawan mulkin mallaka ina da wayona, na ga karbar mulkin kai na Nijeriya da aka yi. Na ga mulkin Tafawa Balewa da Sardauna na ga kuma mulkin sojoji daban-daban, kuma mun samu kyakykywar dangantaka da su, don mu ’yan Tijjaniyya muna da wani abu shi ne a kullum mu kofar gidanmu a bude take, duk wanda yake son zuwa ya zo ya shiga cikin aminci, wanda kuwa yake son wucewa shi ma ya wuce cikin aminci.
Ko akwai shawarar da za ka bai wa Gwamnatin Tarayya da sauran gwamnatoci?
Matsalarsu ita ce ba sa jin shawara, duk shawarar da za mu ba su a ganinsu ba ta da amfani a gare su, inda a ce za su saurare mu da sai mu ba su shawara. Sun riga sun dauki siyasa ita ce abar da za ta kawo musu girma, alhali ita kuma siyasa wata aba ce da ke karrama dan Adam don dan siyasa yana kawo wa mutane ne alherin da ba za su iya kawo wa kansu ba, kuma yana tunkude musu sharrin da ba za su iya tunkude wa kansu ba. Wasu matsalolin al’umma kudi ma ba ya iya ture su sai dai gwamnati, ’yan siyasar nan sukan tafi yakin neman zabe su yi damara su yi alkawarin kyautata rayuwar al’umma da kuma samar musu da kayayyakin more rayuwa, idan aka zabe su bayan shekara hudu mutane sai su duba su gani in sun cika alkawari a zabe na gaba ko da bai fita yakin neman zabe ba, za a sake zabarsa in kuwa bai cika alkawari ba, mutane sai su canja shi su zabi wani. Wannan ita ce siyasa saboda haka nake shawartar shugabanni su ji tsoron Allah, su kuma yi wa jama’ar da suka zabe su aiki tsakani da Allah.
Wace shawara Shehi zai bai wa matasa?
Ina shawartarsu da su ji tsoron Allah su nemi ilimi su girmama na gaba da su, kuma su ji tausayin na kasa da su. Ina shawartar dukkan matasa cikinsu har da ’ya’yana da almajiraina da dukkan al’ummar Musulmi kowa ya san wanda yake gaba da shi iya girmansa ya girmama shi, kuma kowa ya san wanda ya girma ya ji tausayinsa, ba kamar irin abin da yake faruwa yanzu ba. Sai ka ga yadda za ka ga matasa da suke kiran kansu da sunan malamai amma suna zagin wadanda suka girme su suka fi su ilimi da tsoron Allah cikin Musulunci.
Ga shi an gabatar da taron zikiri da addu’o’in zaman lafiya na sabuwar shekara wane sako ka bayar a taron?
Alhamdulillahi mun yi taron zikiri na wannan wata na farkon Shekarar Musulunci na Al-Muharram. Juma’ar farko mukan fara yi a nan Bauchi, Juma’a ta biyu muna yi a garin Dass, ta uku za mu yi a Fadar Sarkin Lafiya a Jihar Nasarawa, Juma’ar karshe ta hudu kuma mu yi a Birnin Tarayya, Abuja. Domin Ubangiji Yana cewa ‘La’ilaha illahu Babbar KatangaTa ce duk wanda ya shige ta ya huta da azabaTa.’ Za mu gabatar da wannan La’ilaha Illallahu mu sa Najeriya a cikin wannan Babbar Katanga. Allah Ya kiyaye mu Ya kiyaye mana kasarmu daga dukkan fitina. Kuma za mu fuskanci Sabuwar Shekara da La’ilaha Illallahu sannan mu roki Allah Ya yafe mana zunubban da muka aikata a shekarar da ta wuce, abubuwan da muka yi na lada kuma Allah Ya karba. Sabuwar Shekarar da muka shiga kuma Allah Ya sa mun shige ta da alheri ta zama shekarar alheri, shekarar zaman lafiya da kwanciyar hankali. A lokacin taron muna gayyatar dukkan Musulmi domin La’illaha Illallahu kayan dukkan Musulmi ne mu zo mu yi zikiri tare aji jawabai kuma a roki Allah tare, Allah Ya ba mu alheri Ya kiyaye sharri. Fitinun da suke faruwa Allah Ya yi mana maganinsu, bala’o’i duka Allah Ya kiyaye mana su. Kamar na su Boko Haram da satar mutane a nemi kudin fansa da satar dabbobi da dukkan bala’o’i, Allah Ya yaye mana su. Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya da kwanciyar hankali.