Shugabannin Tarayyar Turai sun yi taro kan bakin-haure

Shugabannin kasashen Tarayyar Turai wato EU sun yin taro jiya (Alhamis) a birnin Brussels na kasar Belgium domin tattaunawa a kan kiran da kasar Italiya ta yi na daukar matakin soji a kan masu safarar mutane daga kasar Libiya zuwa nahiyar Turai. Firaministan Italiya, Matteo Renzi, ya bukaci da a samar da wata doka wacce […]

Shugabannin Tarayyar Turai sun yi taro kan bakin-haure
Shugabannin Tarayyar Turai sun yi taro kan bakin-haure

Shugabannin kasashen Tarayyar Turai wato EU sun yin taro jiya (Alhamis) a birnin Brussels na kasar Belgium domin tattaunawa a kan kiran da kasar Italiya ta yi na daukar matakin soji a kan masu safarar mutane daga kasar Libiya zuwa nahiyar Turai.

Firaministan Italiya, Matteo Renzi, ya bukaci da a samar da wata doka wacce za ta ba da damar lalata jiragen ruwan da ake daukar bakin-hauren daga Libiya tun ma kafin su taso daga kasar.
Ministan harkokin kasashen wajen Italiya, Paolo Gentiloni, ya shaida wa BBC cewa akwai bukatar kasashen nahiyar Turai su dauki matakan kare rayukan bakin-hauren.
Tarayyar Turai tana tsara wani shiri da zai ba ta damar mayar da bakin-haure zuwa kasashensu na asali.
Bakin-hauren dai na ci gaba da mutuwa a tekun Bahar Rum a yunkurin da suke yi na tsallaka wa nahiyar Turai, inda ko a makon jiya sai da mutane fiye da 800 suka mutu lokacin da jirgin da suke ciki ya nitse a teku.