Shugabar Ƙaramar Hukuma ta ƙaddamar da yaƙi da cutar Kwalara a Gombe

An buƙaci a riƙa wanke hannaye da sabulu a ruwa mai gudana bayan an yi amfani da banɗaki.

Shugabar Ƙaramar Hukuma ta ƙaddamar da yaƙi da cutar Kwalara a Gombe

Shugabar Ƙaramar Hukumar Shongom a Jihar Gombe, Hajiya Fatima Binta Bello, ta ƙaddamar da shirin feshin maganin kashe kwayoyin cuta a dukkan unguwanni 10 na karamar hukumar.

Shugabar Ƙaramar Hukumar ta ƙaddamar da wannan aiki ne da nufin magance matsalar rashin tsabtataccen ruwan sha a rijiyoyin da ke yankin domin yaƙi da cutar kwalara.

Lamarin na zuwa ne a yayin da sama da jihohi 31 daga cikin 36 na Najeriya aka sami rahoton bullar cutar kwalara, sai dai babu rahoton ɓullar cutar a Jihar Gombe.

Hajiya Binta Bello, ta tabbatar da cewa al’umma sun sami damar yin amfani da sinadarai don tsaftace ruwan rijiyar su, ba tare da tunanin kamuwa da cutar ta kwalara ba.

A wani rangadi na rijiyoyi da ya gudanar a garin Boh, Hakimin Shongom, Malam Dahiru Alfayo Yusuf, ya yaba wa Hajiya Fatima dangane da matakan da ta ɗauka na yi wa cutar kwalara rigakafi a yankin.

Rangadin feshin magani da Shugabar Ƙaramar Hukumar ta ƙaddamar

Alfayo Yusuf, ya kuma yaba wa ƙoƙarinta na kula da lafiyar al’ummar, yayin da ya buƙaci mazauna yankin da su ba ta goyo baya domin tana da kyakkyawar aniya.

Shi ma Ko’odinetan Shirin Samar da tsabtaccen Ruwan Sha na WASH a karamar hukumar, Mista Cam B. Maigari, ya bayyana cewa matakin da shugabar ta ɗauka abun a yaba ne kuma ya zo a daidai lokacin da ake da buƙata ta musamman.

Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kan al’umma, inda ya buƙaci mazauna yankin da su riƙa wanke hannayensu da sabulu a ruwa mai gudana bayan sun yi amfani da banɗaki saboda kiyaye lafiyarsu musamman wajen sarrafa abinci.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos