Shugabar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ta gana da Shugaban Kamaru
A karo na farko tun bayan da ta karbi mulki a watan Janairu a matsayin Shugabar wucin gadi ta Jamhuriyar Tsakiyar Afirka , Catherine Samba Panza ta gana da Shugaban kasar Kamaru Paul Biya a birnin Brussels na kasar Belgium. Shugabannin biyu sun tattauna ne game da samar da hanyoyin masu dorewa wanda za su […]
A karo na farko tun bayan da ta karbi mulki a watan Janairu a matsayin Shugabar wucin gadi ta Jamhuriyar Tsakiyar Afirka , Catherine Samba Panza ta gana da Shugaban kasar Kamaru Paul Biya a birnin Brussels na kasar Belgium.
Shugabannin biyu sun tattauna ne game da samar da hanyoyin masu dorewa wanda za su taimaka gurin shawo kan matsalar kashe-kashen
addini da ke faruwa a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka. Lamarin da ya kai ga makwabciyarta Kamaru karbar akasarin ‘yan gudun hijira da ke gujewa tashe-tashen hankulan da ke faruwa a can.
Wannan ganawar ta zo ne bayan sanarwar da kasar Chadi ta yi na janye dakarunta wanda ke aikin samar da zaman lafiya a Jamhuriyar Tsakiyar Afirkan.
kasar Chadi dai ita kasar da ta fi kowace yawan sojoji a kasar. Amma wasu na cewa wannan dalili ne ya sa Shugabar Jamhuriyar Tsakiyar Afirkan ta fara karkatowa zuwa ga Kamaru . A fatanta na ganin cewa ita ma ba ta ja da baya ba.
A jawabinta ga manema labarai bayan kammala taron, Shugabar ta ce ta ji dadin yadda kasar Kamaru ta karbi ‘yan gudun hijiran da hannu biyu-biyu kuma ta ce za ta yi iya kokarinta don ganin cewa an samar da yalwataccen zaman lafiya a kasar saboda ta haka ne kawai ‘yan gudun hijiran za su yi marmarin koma wa gida.
A nashi bangaren, Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya bayyana cewa lokaci ya yi da kasashen duniya za su tashi tsaye don ganin an maido da tsaro da kuma zaman lafiya a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, saboda a cewar shi hakan ne kawai zai tabbatar da zaman lafiyan makwabtanta da ma duniya baki daya.