Shugabar Jamus ta zama malamar tarihi

Shugabar kasar Jamus, Angela Merkel, wadda ke yakin neman zabe a karo na uku, ta kwaikwayi zama malamar makaranta, inda ta shiga wani aji ta karantar da dalibai tarihi, a ranar bikin kafuwar bangon Berlin a shekara 52.Merkel, wadda masu nazari ke ganin ita ce kan gaba a zabe mai karatowa nan da wata mai […]

Shugabar Jamus ta zama malamar tarihi

Angela Markel tana koyarwa a cikin ajiShugabar kasar Jamus, Angela Merkel, wadda ke yakin neman zabe a karo na uku, ta kwaikwayi zama malamar makaranta, inda ta shiga wani aji ta karantar da dalibai tarihi, a ranar bikin kafuwar bangon Berlin a shekara 52.
Merkel, wadda masu nazari ke ganin ita ce kan gaba a zabe mai karatowa nan da wata mai kamawa, tana dawowa daga hutun makonni biyu sai ta zarce cikin aji, inda ta koyar da ’yan aji shida a tsohuwar makarantar da ta halarta a Gabashin Berlin.
A shekarar 2005, ta zama shugabar Jamus ta farko, wadda ta girma a Gabashin kasar, inda ’yan kwamunisanci suka yi mulki. Don haka ta koya wa dalibai tarihi kan abin da ta sani ya auku a lokacin da take yarinya, karkashin mulkin hukumomin gabashin Jamus.
 “A shekarar 1961, Shekarar da na fara karatu,” a cewarta, lokacin da ta isa makarantar sakandiren Heinrich Schliemann