Shugabar karamar hukuma ta rushe gidajen Gala 39 a Yobe

Shugabar Karamar Hukuma Fika a Jihar Yobe ta jagoranci rushe gidajen giya da na rawan Gala masu dakuna 140

Shugabar karamar hukuma ta rushe gidajen Gala 39 a Yobe

Wata shugabar karamar hukuma ta jagoranci rusa gidajen giya da na rawan Gala masu dakuna 140 a Jihar Yobe.

A ranar Asabar ne Shugabar Karamar Hukumar Fika, Hajiya Halima Kyari Joda ta jagoranci rusa wasu gidajen giyan da na rawan guda 39 a Garin Ngalda.

Halima Kyari ta dauki matakin ne da rakiyar jami’an tsaro da ’yan Hisbah wakilan sarakunan gargajiya ne, bayan haramcin da ta ya sanya wa gidajen rawan Gala da na sayar da barasa a karamar hukkumar.

A yayin aikin na rusau, an yi nasarar kama wasu masu gidajen gala tare kuma da farfasa tuluna da kwalaben giya a gidajen galan.

Mazauna Garin na Ngalda sun yaba dangane da daukar wannan matakin, sannan suka yi kira ga gwamnati da gina musu  wasu abubuwa da za su amfanesu a wajen da aka rusa gine-gine da ake aikata ayyukan masha’a a baya.

Shugabar karamar ta shaida wa Aminiya cewa sai da ta zauna da wasu alkalai masana shari’a suka ba ta shawarar a rubuta wa masu wadannan gidaje wa’adin kwanaki uku su tashi, lokaci na cika ta aka gudanar da rusau din.

A cewarta  kasancewar an rusa illahirin wuraren badala a garin na Ngalda, “na kudiri aniyar zuwa wurin mai girm Gwamna don neman a gina makaranta a wajen don al’umma su amfana.”

Ta ce rushe wannan wuri ya sa rundunar ’yan sandan Jihar Binuwa ta samu nasarar cafke wani kasurgumin mai laifin da take nema ruwa a jallo, wanda a da yana boye ne a wannan wuri wanda sansani ne na masu aikata muggan laifuffuka.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja