Shugabar kasar Jamus ta lashe wa’adi na hudu

Shugabar Kasar Jamus, Angela Merkel ta lashe zaben kasar da aka gudanar karo na hudu. Wata cibiyar bincike ta ARD ta bayyana cewa jam’iyyarta ta masu ra’ayin rikau ta samu kashi 32 da digo biyar na daukacin kuri’un da aka kada wanda hakan ke nuna jam’iyyar ita ce jam’iyyar da tafi kowacce girma a majalisar […]

Shugabar kasar Jamus ta lashe wa’adi na hudu

Shugabar Kasar Jamus, Angela Merkel ta lashe zaben kasar da aka gudanar karo na hudu.
Wata cibiyar bincike ta ARD ta bayyana cewa jam’iyyarta ta masu ra’ayin rikau ta samu kashi 32 da digo biyar na daukacin kuri’un da aka kada wanda hakan ke nuna jam’iyyar ita ce jam’iyyar da tafi kowacce girma a majalisar kasar.
Jam’iyyar da ta kulla kawance da ita ta SPD ta samu kashi 20 daga kuri’un da aka kada a kasar.