Shugabar matan PDP ta bayyana shakku game da sace ’yan matan Chibok

Shugabar mata ta jam’iyyar PDP ta kasa, Misis Kema Chikwe ta bayyana shakku game da sahihancin labarin da ake ta yayatawa cewa an sace ’yan mata a wata makaranta da ke Chibok ta Jihar Borno.Da take jawabi a yayin wata addu’a ta musamman da jam’iyyar PDP ta shirya a sakatariyarta ta kasa da ke Abuja […]

Shugabar matan PDP ta bayyana shakku game da sace ’yan matan Chibok
Shugabar matan PDP ta bayyana shakku game da sace ’yan matan Chibok

Shugabar mata ta jam’iyyar PDP ta kasa, Misis Kema Chikwe ta bayyana shakku game da sahihancin labarin da ake ta yayatawa cewa an sace ’yan mata a wata makaranta da ke Chibok ta Jihar Borno.
Da take jawabi a yayin wata addu’a ta musamman da jam’iyyar PDP ta shirya a sakatariyarta ta kasa da ke Abuja shekaranjiya Laraba, Misis Chikwe ta ce akwai tambayoyi da yawa da suke bukatar amsa game da sace ’yan matan da aka ce an yi.
Daga cikin wadannan tambayoyin, a cewarta, akwai, “Yaya aka yi lamarin ya faru? Wane ne ya gani? Wane ne bai gani ba? Wane ne ya aikata wannan danyen aikin?”
Domin samun amsoshin wadannan tambayoyin sai ta bukaci shugabar makarantar ta fito da sunaye da hotunan ’yan matan da aka sace.
Kafar watsa labarai ta Sahara Reporters ta ruwaito cewa, Misis Chikwe ta bayyana shakkun nata ne a daidai lokacin da dimbin ’yan asalin yankin Chibok da suka hada da iyaye mata da suke cikin  damuwa kuma suke bukatar bayani daga gwamnati, suka gudanar da zanga-zanga a Abuja domin a hanzarta sako ’yan matan da aka ce ’yan Boko Haram ne suka sace su kwanaki 18 da suka gabata.
A lokacin zanga-zangar, matan, wadanda mafi yawansu ’yan kungiyar cigaban Chibok ne, sun taru ne a dandalin Eagle da ke Abuja, daga nan suka taka zuwa majalisar tarayya, inda suka mika takardar  korafinsu.
Shugabar mata ta PDP din ta cigaba da cewa, “Babu wata jarida da ba ta taba bayar da rahoton fyade ba a kasar nan, mummunan abun da ya faru shi ne sace ’yan matan makarantar Chibok”.
Ta ci gaba da bayyana shakkunta game sahihancin sace ’yan matan, inda take ganin wata makarkashiya ce aka shirya, wadda gwamnatin PDP har yanzu ba ta ce komai ba game da hakan.
Duk da haka Misis Chikwe ta bayyana wadanda suka aikata wannan mugun aikin a matsayin,  “Masu kaunar duhu fiye da haske”, tare da rokon Allah Ya taba zukatansu.
Kwanaki 18 ke nan da aka sace ’yan mata a makarantar ’yan mata ta gwamnati da ke yankin karamar Hukumar Chibok a Jihar Borno a cikin dare. Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton ba a sako su ba, duk da kiraye-kirayen da iyayen yaran suka yi wa ’yan bindigan da su yi wa Allah su sako su. Gwamnatin Jihar Borno har alkawari  ta yi na bayar da ladar Naira miliyan 50  ga duk wanda ya taimaka aka sako su.
 kungiyoyin mata daban-daban irin su kungiyar kare hakkokin mata ta WRAPA da ta Musulmi mata FOMWAN, da dai sauransu, sun yi Allah wadai da garkuwa da ’yan matan da aka yi, har suka yi yunkurin shiga dajin Zambisa domin kwato wadannan ’yan matan, kamar yadda Farfesa Hauwa Abdu Biu da Hajiya A’ishatu Ngulde  suka fada a wani taron manema labarai a garin Maiduguri.
An yi hasashen cewa, ’yan bidigar sun aurar da ’yan matan a tsakaninsu ta hanyar biyan kudin sadaki Naira dubu biyu, suka kuma ketara da su kasashen Kamaru da Chadi. Shaidun gani da ido sun ce sun ga jerin gwanon motoci kirar bas-bas da a-kori-kura cike da ’yan matan da kuma ’yan bindigar suna ketarawa kasashen makwabta na Kamaru da Chadi.
A lokacin da ’yan bindigar suka kutsa makarantar sakandare ta ’yan mata na gwamnati da ke Chibok din sun kona daukacin azuzuwa da ofisoshi da kuma dakunan kwanan daliban, sannan kuma suka yi awon gaba da ’yan mata sama da 200. Kodayake daga baya an gano ’yan mata 44, bayan da suka samu nasarar kubucewa a motar da aka sace su.