Shugabar Sakandaren Tondi-Yauri ta nemi agajin gwamnatin Kebbi
Shugabar Makarantar Sakandaren Tondi-Yauri a Jihar Kebbi, Hajiya Assibi S. Kamba ta roki gwamnatin jihar ta gaggauta agaza wa makarantar da karin ajujuwa da kwararrun malamai.Hajiya Assibi Kamba ta bayyyana haka ne lokacin da wakilinmu ya ziyarci makarantar domin ganin halin da makarantar ke ciki. Ta ce, matsalolin da suka fi damun makarantar su ne […]
Shugabar Makarantar Sakandaren Tondi-Yauri a Jihar Kebbi, Hajiya Assibi S. Kamba ta roki gwamnatin jihar ta gaggauta agaza wa makarantar da karin ajujuwa da kwararrun malamai.
Hajiya Assibi Kamba ta bayyyana haka ne lokacin da wakilinmu ya ziyarci makarantar domin ganin halin da makarantar ke ciki. Ta ce, matsalolin da suka fi damun makarantar su ne rashin malamai da rashin kammala katangar makarantar da rashin wutar lantarki da karancin funfunan tuka-tuka da lalacewar ajujuwan da iska ta kware.
Hajiya Assibi S. Kamba ta roki Ma’aikatar Ilimi ta jihar ta mika koke-kokensu ga gwamnatin jihar a kan matsalolin makarantar, ta kuma yi kira ga iyayen yara su rika kula da karatun ’ya’yansu tare da tabbatar da suna komawa makaranta a ranar da hutu ya kare, ba sai bayan mako ko mako biyu ba.
Shugaban ta ce duk dalibin da bai dawo makaranta a kan lokaci ba, sai ya zo da iyayensa domin a ji dalilin rashin dawowa da wuri.