Shure-shure bai hana mutuwa
Ta kowace fuska dai aka kalli irin yadda al’amarin tsaro ke tabarbarewa a kasar nan sai a tabbatar da cewa abin akwai ban tsoro. Dalili kuwa shi ne babu yadda za a yi a ce a makekiyar kasa kamar Najeriya an kasa magance ta’addanci da wasu ‘yan kalilan suka haddasa, hatta ma askawarar kasar, wadanda […]
Ta kowace fuska dai aka kalli irin yadda al’amarin tsaro ke tabarbarewa a kasar nan sai a tabbatar da cewa abin akwai ban tsoro. Dalili kuwa shi ne babu yadda za a yi a ce a makekiyar kasa kamar Najeriya an kasa magance ta’addanci da wasu ‘yan kalilan suka haddasa, hatta ma askawarar kasar, wadanda suka yi fice a kasashen duniya wajen tabbatar da lumana sun shantake, sun kasa hana kasarsu fadawa hannun makiya zaman lafiyarta. Baicin nasarororin da ‘yan kungiyar da ake kira Boko Haram ke samu a yankin Arewa-maso-Gabashin kasar nan, suna kame mashahuran garuruwa, suna shimfida mulki yadda suke so, jama’ar cikinsu kuma suna tarwatse cikin rukukin dazuzzuka da garuruwan makwabta, suna zaman hijira, sai ga shi abin ya yi kamari har ma manyan biranen jihohin Yobe da Barno da Adamawa suke kokarin kakkamewa, ana ji, ana gani sun faskara, ba mai iya shawo kansu.
Abubuwa biyu ne suka janyo haka: na farko sakacin gwamnati da kuma lusarancin shugabanninta da suka kasa daukar kwararan matakan kawar da take-taken da suka gawurta da gangan, suka zame ta’addancin da ya buwayi kowa da kowa.
Na biyu kuma shi ne yadda makiya Najeriya daga kasashen ketare, wadanda suka dade suna neman ganin bayan kasar, tare da taimakon wasu gafalallun ‘ya’yanta, suka dukufa don tabbatar da bakin burin da suka dade da tsarawa, walau dai don wargaza Najeriya don kada ta ci gaba da jan ragamar sauran kananan kasashen Afrika, ko kuma don su ci gajiyar arzikin da Buwayi Ya huwace mata fiye da ‘ya’yanta. Dangane da haka makiya Najeriya da jama’arta suka yi ta janyo matsalolin da suka haddasa rikice-rikicen addini da na kabilanci don su rarraba kawunan jama’a, domin idan ba hakan ne suka yi ba to fa hakarsu ba za ta cimma ruwa ba.
To bayan sun yi nasara game da haka ne, suka kuma samu sukunin daure wa karya gindi ta hanyar daddasa shugabannin siyasar da suka tabbata lalle za su biye masu, su ki jama’arsu, sai suka nemi kirkiro abin da zai kara taimaka musu don kaiwa ga waccan kazamar bukatarsu ta tatse arzikin kasar nan. Bayan sun shimfida mummunar manufar rarraba kawunan jama’a, ta hanyar amfani da bambancin addini, sai kuma suka ci gaba da bin wannan manufa ta hanyar rungumar wata kungiyar addini da nufin bi ta kanta don wargaza mabiyanta da kuma daidaita kyawawan akidojin wannan addinin. Ta haka ne suka dinga bayar da goyon baya ga wasu gungun miyagun mutanen da suka shiga rigar ‘yan kungiyar Boko Haram da aka dade da halakawa bayan kisan shugabansu, Muhammad Yusuf, don su ci gaba da bata sunan Musulunci, suna kuma yin abubuwan da za su bayar da dama ga makiya Najeriya don samun gindin zama a wasu muhimman wurare bayan sun tsiyata mazauna can, sun kuma kuntata masu ta
yadda ba za su iya kawo masu cikas ba idan har sun fara amayar da maitarsu a fili.
Shi ya sa ake ganin cewa wannan mummunan al’amari da ke kara kamari a kullum da hannun wasu manyan kasashen duniya, musamman ma wadanda ke da alaka da kasashen da ke makwabtaka da Najeriya, kuma tun da an yi rashin sa’a, an samu gwamnatin da ba ta iya yin katabus wajen kawar da sharri da kutungwilar da suke haddasa wa kasar, sai kawai ta buge da tarairayar manyan makiya kasar, tana kuma dasawa da iyayen gidansu, wadanda kowa ya san cewa su ne ke ingiza wutar ta’addancin daga kasashensu.
Babu wani dalilin da zai sa Gwamnatin Shugaba Jonathan ta shantake dangane da wannan matsalar, domin kuwa jama’a na matukar nuna damuwarsu game da yadda ta kasa kare su daga sharrin wadannan miyagun da aka tabbatar ta san ko su wane ne su, amma ta kyale su suna ta cin karensu babu babbaka. Idan har da ta damu ai da ta yi iyakacin kokarinta wajen karfafa gwiwar jami’an tsaro don kawar da fitintinun da ‘yan ta’addan ke haddasawa, da kuma jama’a sun samu damar zama cikin lumana da kwanciyar hankali, suna gudanar da harkokinsu na zumunci da sauran mu’amalolin da za su amfani rayuwa da zamantakewarsu ba tare da fargabar komai ba. Idan kuma da jami’an tsaro sun san cewa da gaske gwamnatin Shugaba Jonathan ke yi wajen kawo karshen wannan fitinar wacce a wajensu ba ta taka kara ta karya ba, ai da sun dage wajen ba shi shawarwarin shawo kan ta’addancin cikin ruwan sanyi, a kuma magance ta kafin kiftawa da bisimilla.
Amma, kash! Ba haka nan al’amarin ya kasance ba, gwamnatin ce ba ta son kawo karshen wannan ta’addancin domin kuwa akwai masu amfana da haka, kuma ko shi kansa Shugaba Jonathan ya furta cewa ai a cikin gwamnatinsa akwai ’yan wannan kungiyar rike da manyan mukamai. To idan da ana so a kawo karshen fitinar ai da daga kansu za a fara daukan matakai, amma ina?
Yanzu ma hankalin gwamnati ya karkata ga harkokin zabe da kuma yadda za a yi amfani da al’amuran da ke wanzuwa sakamakon ta’addancin don murda zaben, ta yadda za ta ci gaba da bin wadancan munanan manufofi na iyayen gidan shugabanninta na wargaza kasar don kwasar garabasa. Shi ya sa aka bari ‘yan ta’adda, da sunan Boko Haram, ke ta aikata ta’asa, suna kisa ba kakkautawa a daidai lokacin da aka fara shirye-shiryen tunkarar zaben shekara mai zuwa don a hana wasu samun damar amfani da kuri’unsu don canja gwamnatin da ta ki damuwa da illolin da ta’addanci ke haddasawa, musamman a yankunan da aka fi nuna mata adawa. Wajibi ne Gwamnatin Jonathan ta kawo karshen wadanman masifun cikin gaggawa kafin zabe, idan ba haka ba kuwa wadannan masifun ne za su yi sanadiyyar faduwarta a wannan karon. Ta riga ta fahimci haka, shi ya sa kuma take dagewa don ganin ta ci gajiyar ta’addanci don ta yi tasiri dangane da haka, amma ya kamata dai ta sani cewa shure-shre ba su hana mutuwa.