Shure-shuren mutuwa ya sa PDP ke cewa APC jam’iyyar Musulmi ce – Matawellen Toro

Wani tsohon dan siyasa kuma Matawellen Toro, Alhaji Baban Iya Umar Muhammad ya ce shure-shuren mutuwa da Jam’iyyar PDP  ke yi ne ya sa manyan jami’anta suke cewa Jam’iyyar APC jam’iyya ce ta Musulmi. Alhaji Baban Iya Muhammad ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce Jam’iyyar […]

Shure-shuren mutuwa ya sa PDP ke cewa APC jam’iyyar Musulmi ce – Matawellen Toro

Wani tsohon dan siyasa kuma Matawellen Toro, Alhaji Baban Iya Umar Muhammad ya ce shure-shuren mutuwa da Jam’iyyar PDP  ke yi ne ya sa manyan jami’anta suke cewa Jam’iyyar APC jam’iyya ce ta Musulmi.
Alhaji Baban Iya Muhammad ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce Jam’iyyar APC ba ta Musulmi kadai ba ce haka ita ma PDP ba ta Musulmi kadai ba ce.  Ya ce a Najeriya kowace jam’iyya dole ne a samu Musulmi da Kirista da wanda ba ya da wani addini. “karya ce mutum ya ce zai kafa jam’iyya ba tare da hada Musulmi da Kirista da wanda ba ya da addini a Najeriya ba,” inji shi.
Alhaji Baban Iya ya ce tuni suka bayyana cewa Jam’iyyar PDP za ta wargaje domin ba ta dauko matakin kyautata wa ’yan Najeriya ba. Ya ce talakan Najeriya bukatarsa ita ce gwamnati ta samar masa da abubuwan kyautata rayuwa kamar ruwan sha da samar da ilimi da hanyoyin mota da asibitoci da kyautata tsaro da sauransu.
Ya ce PDP ba ta dauki wannan hanya ba, domin duk jami’anta kansu kawai suke so ba al’ummar Najeriya ba. Ya ce wannan ya sa kowa a Najeriya yana ta gunaguni kan yadda suke mulkin kasar.
Alhaji Baban Iya ya ce mun yi tsammanin za su gyara, amma suka ki gyarawa suna ganin da karfi ne za su sake samun mulkin Najeriya. Ya kamata su yi hakuri kawai domin jama’ar Najeriya canji suke bukata. Kuma ina kira ga al’ummar Najeriya su kwantar da hankalinsu su zabi mutanen kirki idan lokacin zabe ya zo,” inji shi.