Shu’umcin da ke tattare da rayuwa

Kamar kullum, ina yi muku sallama, Assalamu alaikum. Ina fatan Allah Ya ci gaba da yi mana jagora bisa al’amuran rayuwarmu ta yau da kullum. Ina fatan mun karu da maudu’inmu na makon jiya, inda muka yi wa juna tambihi game da mutum. A yau kuma za mu duba wani sabon maudu’in ne, kamar yadda […]

Shu’umcin da ke tattare da rayuwa
Shu’umcin da ke tattare da rayuwa

Kamar kullum, ina yi muku sallama, Assalamu alaikum. Ina fatan Allah Ya ci gaba da yi mana jagora bisa al’amuran rayuwarmu ta yau da kullum. Ina fatan mun karu da maudu’inmu na makon jiya, inda muka yi wa juna tambihi game da mutum. A yau kuma za mu duba wani sabon maudu’in ne, kamar yadda yake zayyane a sama. Abin da za mu duba shi ne yane-yane da shu’umcin da ke tattare da rayuwar yau da kullum, musamman abin da ya danganci fadi-tashin da ke dabaibaye da al’amuranmu na rayuwa. Shin me ke tsanin kaiwa ga nasara kuma idan an samu nasarar ta yaya za a rike ta ta ci gaba da tabbata? Wadannan tambayoyi, dukkansu abin dubawa ne kuma abin nazari ne domin gane yadda rayuwa ta kasance wata shu’uma, mai wuyar sha’ani kuma mai wuyar gudanarwa.
Idan na tuno da hikimar wani mawakin Hausa da ya yi waka game da duniya, sai in kara sakankancewa, lallai rayuwa shu’uma ce. Kamar yadda mawakin ke cewa: “Duniya da wuyar zama. In kai kirkin ba ka tsira ba, in kai rashin kirkin ba ka tsira ba. Da kudinka anai maka dariya, wanda bai da kudin bai tsira ba…”
Wannan batu na wannan mawaki na kara nuna mana karara yadda rayuwa take shu’uma, yadda kuma ta kasance wata karkatattar gora mai wuyar fafewa. Domin kuwa, idan za mu duba ma’anar abin da mawakin nan ya ambata, yana nufin cewa lallai kam mutum ba ya da kwanciyar hankali a duniya, muddin dai yana raye, koda kuwa wane irin yanayi yake ciki. Idan ma shi mawadaci ne, wato attajiri, to ba zai tsira daga shu’umancin duniya ba, domin kuwa zai fuskanci kalubale da yawa daga bangarori daban-daban. Misali, zai fuskanci kalubale daga wadanda ba su da wadata irin tasa, zai fuskanci kalubale daga kininsa masu wadata irin tasa da kuma wadanda ma ba su kai shi ba. Wani kalubalen da kuma zai fuskanta daga rayuwa shi ne, ta yaya zai ci gaba da kasancewa mawadaci, watau ya tabbata a cikin wadatarsa? Wannan ma wani shu’umanci ne na rayuwa.
Idan ka kasance mai kirki, ba ka tsira ba daga wurin wasu a cikin duniya, haka kuma idan ka kasance tantiri, marar kirki, ba za ka tsira ba daga kwangwarar makwangwara. Domin kuwa a lokacin da wani zai kalle ka a matsayin mai kirki, to shi wani zai kalle ka ne a matsayin mugu, azzalumi, kasancewar masu iya magana sun ce, mai kirkin wani shi ne karkataccen wani. Wannan shi ne ake kira rana zafi, inuwa kuma kuna. Dalili ke nan ya sanya muka ce rayuwa na cike da shu’umanci da kalubale.
Nasara, abin da kowa ke bukatar samu ke nan a rayuwarsa ta duniya. Sai dai wani abin da ya kamata mu sani shi ne, ita nasara, kamar yadda masu hikimar magana suka fadi, balaguro take, ba zango ce ba; domin da a ce nasara zango ce, da mutum sai ya cin ma ta ya zauna durshan a cikinta, ya kwanta shame-shame a cikinta, ya tabbata a ciki. Sai dai kuma ita balaguro take, yawo take kamar iska, daga nan zuwa can. Wannan dalili ke nan ya sanya za ka ga cewa mutum na fadi tashi a cikin rayuwarsa. Idan ka samu nasara a wannan bangaren, sai ka ga ka rasa a wancan bangaren, don haka dole ne ka fita nema. Misali, idan ka kasance hamshakin attajiri, wanda ya yi nasarar samun wadatattar dukiya, dole kuma za ka fita neman ilimin yadda za ka gudanar ko ka tafiyar da al’amuranka.
Don haka, nasara dai balaguro ce, yau kana iya samun ta, gobe kuma ta kaurace maka, sai ka fita neman ta. Dalili ke nan a kullum dan Adam ke fafutukar neman nasara a bangarorinsa na rayuwar yau da kullum, kan haka har ya kai ga komawa zuwa ga mahaliccinsa. Domin kuwa ba zai karkare samun nasarori ba a dukkan bangarorinsa na rayuwa, sai dai ya samu wasu, wasu kuma sai dai hakuri. Wannan na daya daga cikin dalilan da ya sanya aka ce rayuwarmu ta yau da kullum shu’uma ce, mai wuyar sha’ani.
Babban darasinmu na yau shi ne, mu gane cewa rayuwa dai wata makauniyar abu ce, dole ne sai mun bi ta da taka-tsan-tsan, mu yi kokarin tunkarar abin da zai amfane mu da ita, sannan mu yi watsi da abin da ba zai amfane mu da komai ba a cikinta. Haka kuma, ya kamata mu gane cewa, ita rayuwar nan, ba ’yar dolen dole ce ba, ma’ana, kada mutum ya ce zai samu wani abu ko wata nasara ta karfi da yaji. Maimakon mutum ya yi haka, sai ya yi kokarin bin hanyoyin da suka dace domin neman abin da yake son samu.
Misali, idan mutum na son ya zama ya mallaki wani nau’i na ilimi, sai ya tafi wurin ahalin wannan ilimi ya koya, bayan ya cika dukkan sharudda da ka’idojin da za su share masa hanyar samun wannan ilimi. Ke nan ya tunkari neman nasara ta wannan bangare, wacce dama an ce balaguro take yi. Cikin nemansa da yake wa nasara ta fuskar neman ilimi, sai ya yi sa’ar haduwa da ita. Caraf, sai ya damke abarsa. Wannan ita ce falsafar nema da samun nasara.
Har kullum dai dan Adam yana cikin fafutuka da hakilon tafiyar da rayuwa ne, a burinsa na samun nasara a dukkan matakan rayuwa da ya samu kansa a ciki. Sai dai kuma yana cikin tsoro, tsoro daga rashin nasara, ko tsoron rasa wani muhimmin abu na rayuwa. Wannan kuwa na faruwa ne saboda sanin cewa, idan mu ne yau, to gobe ba mu ne ba, idan jiya kana cikin nasara, kana gani sai ta guje maka, ka ga ta koma wajen wani. Idan da kai mai mulki ne, subul, sai ka ga ya subuce daga hannunka, sai dai ka ga wani yana yi. Idan da kai mai dukiya ne, wata rana sai ka ga ka koma marar ita, sai dai ka gani a hannun wasu. Rayuwa ke nan, shugabar ’yan shu’umanci! Don haka, mu bi ta a sannu, mu yi abin da za mu iya yi daga gare ta, saura kuwa mu bar wa sarautar Mai Duka. Allah Ya sanya mu dace, amin.