Siasia ya yi bikin cika shekara 30 da yin aure
Kocin kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 23 (U-23) Samson Siasia ya yi bikin cika shekara 30 da yin aure. Tsohon kocin Super Eagles a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2011, ya ba mutane da dama mamaki a lokacin da ya sanar da cewa yana bikin cika shekara 30 da yin aure alhali yanzu […]

Kocin kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 23 (U-23) Samson Siasia ya yi bikin cika shekara 30 da yin aure.
Tsohon kocin Super Eagles a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2011, ya ba mutane da dama mamaki a lokacin da ya sanar da cewa yana bikin cika shekara 30 da yin aure alhali yanzu yana da shekara 47 da haihuwa.
Masu shakkun suna ganin da wuya a ce kocin ya yi aure ne a lokacin da yake shekara 17. Hakan ta sa wasu suka shiga shafin abota na facebook da na twitter da sauransu kuma suka rika bayyana shakkunsu a kan batun.
Sai dai a hirar da jaridar Daily Trust ta ranar Asabar 28 ga watan Maris din wannan shekara ta yi da matarsa mai suna Eunice, an samu mabambantan bayanai. Yayin da matar ta kafe cewa sun shekara 30 da yin aure shi kuma mijin nata watau Siasia ya ce yanzu shekararsu 27 da yin aure ba 30 ba. Ya ce sun yi aure ne a shekarar 1988 a lokacin yana dan shekara 20 ba a shekarar 1985 ba a lokacin da yake dan shekara 17, kamar yadda matarsa ta kafe ba.
Ita kuma matarsa Eunice ta kafe ne a kan cewa sun yi aure ne tun cikin shekarar 1985 a lokacin da suka hadu a Benin a lokacin da yake buga wa kulob din Flash Flamingoes kwallo kuma kawo yanzu suna da ’ya’ya bakwai, biyu mata biyar maza.