Sibil Difens ta cafke barayin waya 5 a Kano

A baya-bayan nan dai an samu rahoton yadda mutane ke fusata suka daukar hukunci kan masu kwacen waya.

Sibil Difens ta cafke barayin waya 5 a Kano

Jami’an Civil Defence suna atisaye

Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta NSCDC a Jihar Kano sun kama wasu mutane biyar da ake zargin barayin waya ne.

Kakakin rundunar, Ibrahim Abdullahi, ya sanar a ranar Laraba  cewa an kama wadanda ake zargin ne a unguwar Sabon Gari da ke Karamar Hukumar Fagge ta jihar ranar Talata.

Sanarwar ta bayyana cewa, “Sun kasance suna gudanar da ayyukan ta’addanci a kusa da Sabon Gari, cikin karamar hukumar Fagge inda suke kwace wayoyin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.”

Kakakin ya bayyana cewa jami’an hukumar na leken asiri ne suka gano barayin, inda ya jaddada hukumar na ci gaba da yaki da duk wani nau’in aikata laifuka a jihar.

A baya-bayan nan ana kara samun karuwar matsalar fashin waya a cikin birnin Kano, amma ya tabbatar da aniyar hukumar na dakile wannan lamari.

Ya bayyana cewa, a ranar Talata wasu fusatattun mazauna garin suka kone wani babur mai uku da ake zargin wasu masu kwace waya ke amfani da shi.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan