Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe
Kwamandan ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu.
Hukumar Tsaron Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Gombe, ta kama mutum 10 kan zargin aikata laifuka daban-daban, waɗanda suka haɗa da lalata kayayyakin gwamnati, sata, tserewa daga hannun hukuma, da kuma luwaɗi.
A yayin gabatar da waɗanda ake zargin ga manema labarai, Kwamandan NSCDC na jihar, Gyama Gyawiya, ya bayyana cewa an kama su ne a lokuta daban-daban, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gurfanar da su a gaban kotu.
Kwamandan, ya ce a ranar 20 ga watan Disamba 2024, an kama wani mutum da ake zargi da lalata kayayyakin Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC).
An kama shi da mita da da ya sato daga ofishin hukumar, kuma ya amsa cewa ya aikata irin wannan laifi sau da dama, inda yake satar wayoyi tare da sayar da su a Ƙaramar Hukumar Akko.
A wani lamari, an kama wani matashi mai shekara 19, a Ƙaramar Hukumar Kwami, bisa zargin satar wayar lantarki da ke bai wa wasu garuruwa wutar lantarki.
Matashin ya amsa cewa ya sayar da kayayyakin da ya sata a unguwar Yelenguruza, a birnin Gombe.
Haka nan, a ranar 14 ga Janairu 2025, rundunar ta an kama wasu matasa uku — Mohammed Adamu mai shekara 21, Usman Mu’azu mai shekara 17, da Al-Hassan Mohammed mai shekara 17 — a unguwar Abacha Road, Jekadafari, kan satar buhun masara.
Hukumar ta ce an dawo da wani kaso na kayan da aka sace yayin da ake ci gaba da neman sauran abokan laifin su.
Hukumar ta kuma kama wani mutum mai suna Muhammad Abubakar, wanda aka fi sani da “Alhaji.”
A shekarar 2023, Muhammad ya tsere daga hannun jami’an NSCDC yayin da ake tuhumarsa da aikata laifun luwaɗi.
Sai dai a watan Janairu 2025, an sake kama shi bisa zargin yin fashi tare da ƙwacen wayoyi da kuɗi daga hannun wasu mutum biyu.
A wani lamari na cin zarafin yara, an kama wani mutum mai shekara 30, Dantala Babaniya, bisa zargin yi luwaɗi da wani yaro mai shekara 13.
Bincike ya nuna cewa wasu yara biyu da suka haɗa da Victor Clement da Abdurrahman Ukasha, dukkaninsu masu shekara 11, suna da hannu a laifin.
Bugu da ƙari, a ranar 13 ga watan Janairu 2025, an kama wasu matasa biyu, Babangida Mohammed da Mubarak Mohammed, dukkaninsu masu shekara 18, bisa zargin satar awaki biyu a unguwar Kagarawal.
Sun yanka ɗaya daga cikin awakin yayin da ake ƙoƙarin gano ɗayar da kuma kama sauran waɗanda ake zargi.
Kwamandan NSCDC, Gyama Gyawiya, ya tabbatar wa jama’a cewa duk waɗanda ake zargin za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani abu da ba su gamsu da shi ba ga hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.