Sifaniya ta lashe Kofin Duniya na 2026
Sifaniya ta zama zakara bayan doke Argentina da ci ɗaya mai ban haushi.
Tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Sifaniya ta lashe Gasar Kofin Duniya ta 2026, bayan doke Argentina da ci ɗaya mai ban haushi.
Ferran Torres ya zura wa Sifaniya ƙwallo ɗaya tal a minti na 106.
- Gidaje da gonaki sun lalace sakamakon mamakon ruwan sama a Filato
- Amurka za ta koyi darussan da ba za ta taɓa mantawa ba — Mojtaba Khamenei
Sifaniya ta mamaye wasan tun da minti farko har zuwa lokacin da aka tashi.
Ta dinga kai hare-hare masu hatsari, lamarin da ya sanya har aka tashi Argentina ta gwada jefa ƙwallo ko ɗaya ba.
Ɗan wasan tsakiyar Argentina, Enzo Fernandez ya samu jan kati, bayan an ba shi katin gargaɗi har sau biyu, lamarin da ya sa ƙasarsa ta ƙare wasan da mutane 10 a fili.
Argentina ta lallasa Ingila da ci 2-1 a wasan kusa da na ƙarshe, wanda hakan ya ba ta tikitin zuwa wasan ƙarshe.
Ita kuwa zakarar gasar ta bana, da aka buga a ƙasar Amurka, Canada da Mexico, Sifaniya ta doke ƙasar Faransa da ci 2 da babu a wasan kusa da na ƙarshe.
Sifaniya ta kafa wani tarihi inda ya aka zura mata ƙwallo ɗaya tal a raga tun daga farkon gasar har zuwa ƙarshenta.
Ƙasar Belgium ce ta jefa wa Spain ƙwallo ɗaya a raga a wasan da suka buga a matakin kwata-fainal.