Simintin kamfanin dangote ya yi farin-jini a kasuwar baje kolin Kano
Gamayyar kamfanonin kasuwanci na dangote, a fannin siminti ya yi wata gagarumar nasara a farfajiyar kasuwar duniya da aka gudanar a Kano, inda aka sayar da lodi-lodin manyan motoci da kuma dubban buhuna na daidaiku. Wata sanarwa da ta fito daga kamfanin na dangote ta bayyana haka. Wakilin kasuwancin siminti na yanki, Mista Obashola Alao, […]

Gamayyar kamfanonin kasuwanci na dangote, a fannin siminti ya yi wata gagarumar nasara a farfajiyar kasuwar duniya da aka gudanar a Kano, inda aka sayar da lodi-lodin manyan motoci da kuma dubban buhuna na daidaiku.
Wata sanarwa da ta fito daga kamfanin na dangote ta bayyana haka. Wakilin kasuwancin siminti na yanki, Mista Obashola Alao, ya bayyana gamsuwarsa dangane da hakan, kuma ya jinjina wa sashen sadarwar kamfanin da ma’aikatan sashen siminti da cibiyar harkokin kasuwanci ta Kano da sauran wadanda suka yi hulda da su dangane da nasarar da aka samu.
Ya ce ya lura mahalarta hada-hadar kasuwancin sun bukaci a kara lokacin baaje kolin, saboda jama’a su sami damar cin moriyar ragin da aka yi kan simintin a lokacin da aka gudanar da shi.
In dai ba a manta ba, kasuwar ta tashi ne a shekaranjiya Laraba, bayan ta yi makonni biyu tana ci.
Shugaban cibiyar kasuwanci ta Kano (KACCIMA), Alhaji Umar Faruk Rabi’u dansukeka, ya ce kasuwar baje kolin da aka gudanar ita ce gangaran kan duk sauran da aka taba gudanarwa a tarihin Kano.
Ya ce masu sunsunen zuba jari daga kasashen waje goma sha biyu ne suka halarci kasuwar, ciki har da Amurka. “Irin kiran da jama’a ke yi na a kara lokacin kasuwar ya zama shaida kan nasarorin da aka samu dangane da baje kolin. Kuma kokarin da sashen sadarwa na kamfanin dangote ya yi wajen kwarzanta lamarin ya kara karfafa dankon kasuwanci a Kano”.
Yayin da yake jawabi a ‘Ranar Kamfanin dangote’, Darakta-janar na KACCIMA, Alhaji Ibrahim Tukur Barau, ya ce jama’ar Kano su miliyan 16 suna tare da kasuwar dangote.
Sanarwar ta bayyana cewa gasar kacici-kacici ta dangote ta ga jama’a da dama wadanda sami kyaututtuka daban-daban.
Gwamna Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya ziyarci rumfar baje koli ta dangote ya ce yana alfahari shugaban kamfanin wato Alhaji Aliko Dangote, wanda ya bayar da gwaggwabar gudunmawa wajen habaka tattalin arzikin Kano da Najeriya da ma Afirka baki daya.