Sin da Rasha sun jajirce kada a dauki tsauraran matakai kan Koriya ta Arewa
Shugaba bladmir Putin na Rasha da takwaransa na kasar Sin di Jinpin sun soki lamiri daukar mataki a kan kasar Koriya ta Arewa kan takaddamar gwajin makamin nukiliyarta, al’amarin da suka ce zai haifar da matsala a fadin duniya, don haka ba su yarda da takunkumi ba, sai dai a sasanta ta fuskar difulomasiya. Shi […]

Shugaba bladmir Putin na Rasha da takwaransa na kasar Sin di Jinpin sun soki lamiri daukar mataki a kan kasar Koriya ta Arewa kan takaddamar gwajin makamin nukiliyarta, al’amarin da suka ce zai haifar da matsala a fadin duniya, don haka ba su yarda da takunkumi ba, sai dai a sasanta ta fuskar difulomasiya. Shi kuwa shugaba kasar Sin cewa ya yi ba zai yarda a kai yaki kasar Koriya ba.
Matsayin shugaba Putin ya ci karo da matsayin Majalisar dinkin Duniya, inda Mosko da Beijing suka hade wa Washington da kawayenta.
Litinin din da gabata Amurka ta gabatar da bukatar “daukar tsauraran matakai” kan Koriya ta Arewa saboda harba makami mai linzami da Gwamnatin Pyonggyang ta ce bom din Hydrogen ne da ake makalawa a a na’urar cilla makami mai linzami.
Wannan lamari dai ya haifar da takaddama a tsakanin manyan kasashen kan hana aiwatar da shirin kera irin wadannan makamai, ala’amarin da ke gaban kwamitoci bakwai karkashin kulawar Majalisar Tsaro ta Majalisar dinkin Duniya. kasashen da suke kalubalantar shirin nukiliyar Koriya ta arewa sun hada da Amurka da Koriya ta Kudu da Japan, tare da hadin gwiwar kasashen Faransa da Birtaniya masu kujerar dindindin a Majalisar tsaro ta Majalisar dinkin Duniya, wadanda daukacinsu suka bukaci a dauki tsauraran matakai kan kasar, inda mafi yawansu k eta cdacar baki kan yadda za a sanya kasar takunkumin sayen mai.
Takunkumin da ake son kakaba wa kasar ya hada da hana kai ziyarar bude ido. Sannan Gwamnan Koriya ta Kudu ta ce akwai yiwuwar Koriya ta Arewa ta sake kaddamar da wani maklamin mai linzami.
Shi dai Jakadan kasar Sin a Majalisar dinkin Duniya Mista Liu Jieyi ya jajirce kan cewa, lallai a amince da matsayin kasarsa ta Sin da Rasha, inda ya yi kira ga Koriya ta Arewa ta dakatar da daukacin gwaje-gwajen nukiliyarta, sannan Amurka da Koriya ta Kudu su daina gudanar da atisayen soja na hadin gwiwa.