Sinadarai da sirrikan samun nasara a rayuwa
Gabatarwa: Assalamu alaikum, gaisuwa ga dimbin masu bibiyar jaridar nan, musamman masu bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa. Da farko muna ba ku hakuri saboda dogon nukusanin da filin ya yi. Wannan kuwa ya faru ne saboda wasu matsaloli da suka faru da mu, amma a yanzu da ikon Allah za mu ci gaba da […]
Gabatarwa:
Assalamu alaikum, gaisuwa ga dimbin masu bibiyar jaridar nan, musamman masu bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa. Da farko muna ba ku hakuri saboda dogon nukusanin da filin ya yi. Wannan kuwa ya faru ne saboda wasu matsaloli da suka faru da mu, amma a yanzu da ikon Allah za mu ci gaba da gabatar da filin a kowane mako kamar yadda muka saba. Kamar yadda kuka sani, filin nan ya kware ne wajen sharhi da nusarwa dangane da rayuwarmu ta yau da kullum, inda muke zakulo sinadaran da ke zizara mana gishiri a yadda rayuwar tamu take gudana da nufin samun nasara da kauce wa akasinta. Muna fatan za a ci gaba da bibiyarmu tare da hakuri da juriya. Muna maraba da shawarwari, karin bayani, korafi ko gudunmawa dangane da filin nan daga dukkan masu bibiyarmu.
A yau za mu fara warware jigon maudu’inmu mai taken: Sinadarai da sirrikan samun nasara a rayuwa.
1-Ka yi aiki ba surutu ba
Kamar yadda muka sani dai rayuwa na gudana ne daga abin da muke aikatawa a kullum. Misali, manomi dole ya tashi ya tafi gona ya aikata abin da ya dace, kafin ya girbi hatsin da ya noma. Haka dan kasuwa dole ya tafi kasuwa ya baza hajarsa, kafin masu saye su gani su saya. Dalibi dole ya tafi makaranta domin neman ilimi, kafin ya samu damar sanin abin da bai sani ba.
Ke nan idan kana son cimma nasarar duk wani abu da ka tunkari yi, ya alla aiki ne ko sana’a ko kasuwanci, ya zama dole ka mike tsaye ka tunkari abin gadan-gadan ka aikata shi bisa tsarin yadda ake aikata shi, sannan za ka samu nasara. Kamar yadda wani masani mai suna Walt Disney ya ce: “Ta hanya daya kawai za ka cimma nasara, ka kaurace wa surutu, ka kama aiki kawai.”
Kai manomi ne? To da gari ya waye, kada ka bata lokacinka kana hira da abokai ko makwabta, ka sungumi fartanyarka kawai ka tafi gona ka kama aiki. Idan ka tsaya surutu da labari, aikinka jibge yana can gona. Idan kai dan kasuwa ne, kana zaton idan ba ka dauki hajarka zuwa kasuwa ba, za ka sayar da ita, alhali kana dandali kana ta surutai?
2-Himma ba ta ga rago
Shin da gaske kake, cewa kana son cimma nasara a rayuwa? To ya kamata ka sani cewa, masu iya magana sun ce himma ba ta ga rago. Ya zama wajibi ka zage damtse ka tunkari al’amuranka da gaske cikin himma ba da kasala ba.
Tsohon Firayi Ministan Birtaniya Winston Churchill ya taba cewa: “Ga rago, duk wata dama da zai gani, wahala da kunci yake hangowa a cikinta. Shi kuwa mutum mai himma, yakan hango nasara da albarka a duk cikin wani al’amari mai wahala da tsanani.”
Me Churchill ke son nuna mana a wannan batu? Yana son ya nuna mana cewa, duk sai an shiga rana sannan ake samun maganin rana. Sai an yi zufa sannan ake samun nasara. Ke nan kada mutum ya zauna cikin inuwa, sannan ya yi tsammanin cewa arziki zai zo ya iske shi.
Marigayi Dokta Mamman Shata Katsina, a wata wakarsa mai taken: “Gumina nake ci” ya bayyana cewa “Sai an sha wuya akan sha dadi.” Don haka duk wani aiki da kake yi, sai ka yi da gaske, sai ka sanya kwazo da himma sannan ka samu nasara.
3-Ka mance da jiya don ka rayu a yau
Wani abu da ke kawo wa mutane tarnaki shi ne yadda suke yawan tunanin wani rashin nasara ko wani abu marar dadi da ya faru da su a baya. A kullum suna cikin bibiyar wannan faduwa da suka yi, sun kasa tashi domin tunkarar al’amarin da suka sanya a gaba.
Wani masani mai suna Will Rogers ya ce: “Kada ka bari tunanin jiya ya mamaye zuciyarka, ya hana ka sukunin tunkarar al’amuranka na yau.” Abin da yake nufi a nan shi ne, idan ka tuno da wata faduwa ko rashin nasara da ka yi a jiya, ka yi nazarinta a matsayin misali kawai, domin gano hanyoyin da za ka kauce wa sake faduwa. Amma kada tunanin ya aure ka har ya zama barazana ga abin da za ka yi a yau. Idan an fadi, mikewa ake yi da karfi a ci gaba da tafiya tare da daukar matakan magance abin da ya faru a jiya.
Babban darasin da za mu dauka daga maudu’inmu na yau shi ne, aiki a zahiri ya fi surutu, himma ba ta ga rago, mu kiyayi bibiyar rashin nasararmu ba domin gyara ba. Duk abin da muka sanya gaba za mu yi, mu yi shi gadan-dagan, tare da tsammanin nasara.
Za mu ci gaba