Sinadaran Kamalar ’Ya Mace (3)

Assalamu Alaikum; Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban misalai daga mata ma gabata da yadda suka aikatar da kowane daya daga cikin wadannan sinadaran kamala; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga […]

Sinadaran Kamalar ’Ya Mace (3)
Sinadaran Kamalar ’Ya Mace (3)

Assalamu Alaikum; Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban misalai daga mata ma gabata da yadda suka aikatar da kowane daya daga cikin wadannan sinadaran kamala; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.

 

3. “…Ya Ubangijina! Lallai ni na zalunci kaina; kuma na sallama al’amari tare da Sulaiman ga Allah Ubangijin Halittu.”

Wannan shi ne kalaman Salihar Baiwa Sarauniyar Saba, duk da girman ikonta a matsayinta na Sarauniyar wacce jama’arta ke tsananin ji da ita, sannan ga shi ta mallaki komi na jin dadin rayuwar duniya, ga makeken gadon sarauta da babu irinsa a lokacin, amma duk wannan ba su sa tayi girman kai ba lokacin da gaskiya ta bayyana gareta. Dubi hikimar da ke cikin zancenta, sai da ta fara bayyana nadamarta a kan bautar wanin Allah sannan kuma ta nuna sallamawa da da’a ga Allah. Duk da girman mulki da izza da Allah Ya bai wa Annabi Sulaiman, ba shi ne dalilin imanin ta ba illa fahimtar sakon Allah da Annabi Sulaiman din ya isar gareta. A dalilin haka ta kaskantar da kanta ta koma karkashin mulkin Annabi Sulaiman ta hakura da nata mulkin domin nuna cikakkiyar da’a da sallamawa ga Allah.

Akwai darussa abin koyi da yawa ga uwargida cikin labarin Sarauniyar sabah, da yawa matan wannan zamani in ya kasance sun fi mijinsu samu ko matsayi ko daraja, sai ka ga sun mayar da mijin ba a bakin komi ba, ba su ba shi cikakken iko a kansu ko bin umarninsa ko aiki da haninsa wanda ya kamata su ba shi in da a ce shi ne yake da samu matsayi ko daraja sama da nasu. Haka kuma wasu matan girman matsayi mulkin ko arziki na sanya musu girman kai su rika ganin  sun fi karfin su yi ibada kaza da kaza, ko su rika jin su na musamman ne ko ya sa masu kedaranci su mai da aikata manyan zunubbai abu mai sauki a garesu. Girman kai da jin ni na fi kowa ko ni na musamman ne dabi’un shedan ba tabewa kuwa kamar mutum ya yi kamanceceniya da shedan. Sannan komin jin dadi da more rayuwar duniya, har in ba zakin imani a zuciyar bawa to wanna dadin ragagge ne kwarai da gaske.

4. “Allah Ba zai taba wulakantaka ba; domin ka kasance mai zumunci, mai taimakon talakawa da masu rauni, kana kyautata wa bakinka kuma kana taimakon wanda ya fada cikin musiba.” Wadannan kalamai masu cike da taushi da karamci sun fito ne daga bakin Babbar Salihar da babu kamarta cikin Duniyar Musulunci; ta furta su ga Masoyinta kuma mijinta Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su kara tabbata a garesa don kwantar masa da hankali lokacin da yake cikin tsananin firgitar farkon saukar wahayi. Kalaman masu cike da hikima da fasaha sun fi kowane irin dadi dadadawa. Yana daga cikin da’a ga Allah fahimtarSa da kyautata zato a gareSa. Kalaman Sayyada Khadijah na nuna lallai tana da hakikanin sani game siffofin Ubangijinta tun kafin zuwan Musulunci, a cikin wannan zababbun kalamai ta yabi Allah da nuna Shi Mai karamci ne kuma Yana karrama masu karamci, ta yabi Allah da nuna cewa Shi mai son kyawawan halaye ne musamman in suka yi alaka da kyautatawa da kawo sauki ga masu bukata, sannan kuma ta yabi kyawawan halayen mijinta ta tunasar da shi cewa shi fa mutumin kirki ne don haka Allah ba Zai kunyata shi ba sai dai Ya karrama shi da kara daga darajarsa.

Akwai darussan dauka da dabbakarwa da yawa ga uwargida a cikin rayuwar Sayyada Khadijah Radhiyallahu Anha. Musamman in aka yi la’akari da cewa ta kasance attajira mai kddi kuma mai matsayi a cikin al’umma, amma wannan bai sa mata girman kai da nuna isa ba, sai dai tsarki da taushin zuciya da kaskan da kai ga Ubangijinta Allah Madaukakin Sarki da kuma mijinta Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi. Wannan Ya sa ta iya sadaukar da dukiyarta da karfinta ga kafuwar addinin Allah wanda har Ya kai ta ga matsayin Allah Ya aiko da gaisuwa musamman zuwa gareta kuma bayan rasuwarta Manzon Allah Ya kasance kullum yana cikin kewarta da yaba mata.

Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawara a kodayaushe, amin.