Sinadaran soyayya (2)
Assalamu alaikum wa rahmatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah SWT Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan sinadaran da suke gina soyayyar ma’aurata. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani Ya isa ga duk masu bukatarsa ya kuma amfanar da […]
Assalamu alaikum wa rahmatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah SWT Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan sinadaran da suke gina soyayyar ma’aurata. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani Ya isa ga duk masu bukatarsa ya kuma amfanar da su, amin.
2. Sha’awa
A dangantaka ta tsakanin ma’aurata, komai karfin shakuwarsu, idan ya kasance babu cikakkiya kuma daidaitacciyar sha’awa a tsakaninsu, to shakuwar nan za su ji ta salam ne, domin sha’awa itace gishirin rayuwar aure. Kamar yadda shakuwa ke rike aure ya yi tsawon rai da inganci, to haka ma sha’awa ke iya rike aure ya yi tsawon rai ko da babu inganci sosai a cikinsa; domin akwai ma’auratan da babu shakuwa da fahimtar juna tsakaninsu, kullum suna cikin yin jayayya da juna, amma sai aurensu ya dade saboda akwai daidaitacciya kuma cikakkiyar sha’awa a tsakaninsu.
Matsalar sha’awa tsakanin ma’aurata na daya daga cikin ‘yan gaba-gaban abubuwan da ke saurin kawo mutuwar aure, musamman idan ya kasance namijin ne ba ya samun yadda yake so daga wajen matar, saboda yanayin karfin bukatuwar sha’awar da namiji; mafi yawan mata kuwa na tsananin hakurin jure wa matsalar sha’awa da suke fuskanta daga mazansu.
Fuskokin Sha’awa Cikin Rayuwar Aure
1. Wasu ma’auratan tun farkon haduwarsu suka kasance cikin tsananin sha’awar junansu, kila ma sha’awar ce ta yi dalilin kulluwar soyayyarsu; irin wannan sha’awa takan kasance mai karfi kuma mai wuta-wuta, sannan ma’auratan na yawan jin maganadisunta na giftawa a tsakaninsu; don haka abu kadan zai sa su rika jin son kasancewa da juna, wannan shi ke sa su rika kwakwar juna su ji ba su son rabuwa da juna. Sai dai irin wannan sha’awa ba ta tsawon rai cikin rayuwar aure, nan da nan take mutuwa murus a neme ta a rasa, musamman idan wasu abubuwa suka shigo cikin rayuwar aure, wadanda da can babu su, abin da kadai zai iya hana irin wannan sha’awa mutuwa murus shi ne, idan ya kasance lokacin da suke cikin magagin sha’awa, ma’auratan sun yi kokari wajen kulla aminta tsakaninsu; sun yi kokarin bude hanyar sadarwar da za ta kai su ga samun fahimtar juna; haka kuma sun yi kokarin shiga ran juna ta hanyar kyautatawa da kokarin faranta wa juna rai, wanda zai sa su shaku sosai; to a irin haka ko wutar sha’awarsu ta mutu, to ba za ta mutu murus ba, kuma akwai yiwuwar ta sake ruruwa nan gaba, amma in babu irin haka, to in ta mutu ta mutu ke nan har abada.
A. Sai kuma yanayin sha’awar da ke girma tare da nunar dangantakar da ke tsakanin ma’aurata; watau ma’aurata na kara shakuwa, sha’awar da ke tsakaninsu na kara tsima da dumama. To irin wannan haka za su girma su tsufa da sha’awarsu, sai dai idan wani gawurtaccen abu da ya fado cikin rayuwar aurensu, wanda ke ruguzar soyayyar da ke tsakaninus gaba daya, to wannan na iya sa su ko wani daga cikinsu ya ji ya daina sha’awar dayan, kamar yadda takan faru ga wasu matan yayin da mazansu suka kara aure.
B. Wasu kuma ma’aurata sukan samu bambancin sha’awa tun farkon aurensu, misali:
• Wani lokacin yakan kasance maigida yana da sha’awa mai karfi, kuma mai yawa, ita matar tana da ‘yar kadan, idan ya kasance matar ba ta fuskantar wata matsala a cikin wannan auren sai wannan kadai, to yawanci sukan yi hakuri su daure, amma duk da haka abin na damunsu.
• Ko maigida yana tsananin sha’awar matarsa, yana kwakwar kasancewa da ita, ita kuwa kwata-kwata ba ta sha’awar mijin, kuma tana bari ya kusanceta ne kadai a kan ya zama mata dole; ba wai don ba ta da sha’awa ba, kawai shi din ne ba ta sha’awa. Yawanci irin haka ya fi faruwa ga matan da aka yi wa auren dole, kuma ya kasance ko bayan auren sun ci gaba da tsanar mazan da suke aure, to a irin haka mawuyacin abu ne su ji suna sha’awar mazan nasu.
• Yana iya kasancewa maigida sha’awarsa ‘yar kadan ce kuma marar karfi, ita kuma matar ya kasance tana da sha’awa mai yawa; a irin haka yawanci mata suna hakuri su zauna in dai auren ya kasance ba shi da wata matsala sai wannan kadai.
• Ko ya kasance uwargida na tsananin sha’awar da kwakwar maigidanta, amma shi sai ya ji ba ta burge shi ta fannin sha’awarsa, to a irin haka idan ba an sami namiji mai zurfin tunani da hangen nesa ba, nan da nan zai rabu da ita.
Zan dakata a nan, sai mako na gaba idan Allah Ya kai mu. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.