Sinadaran soyayya (3)

Assalamu Alaikum wa rahmatullah. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah SWT ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan sinadaran da suke gina soyayyar ma’aurata, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatar shi kuma ya amfanar da […]

Sinadaran soyayya (3)
Sinadaran soyayya (3)

Assalamu Alaikum wa rahmatullah. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah SWT ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan sinadaran da suke gina soyayyar ma’aurata, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatar shi kuma ya amfanar da su, amin.

3. Abotayya: Sinadari na ukkun soyayyar ma’aurata shi ne ya kasance akwai kyakykyawar abota tsakanin ma’aurata. Abotayya wata kyakykyawar zumunta ce da ke kulluwa tsakanin mutum biyu ko sama da haka wacce ke dauke da kyakykyawar sanayya da fahimtar juna; yarda da amincewa, so da kauna, da kuma mutunta juna.
Kyakykyawar Abotayya na samuwa ne lokacin da mutum biyu ma’abota kauna da amintar juna, ya kasance suna yawan haduwa akai-akai, kuma in sun hadu din nan suna sabunta sanayya ta hanyar tattaunawa game da kowane bangare na rayuwarsu da rayuwar mutane mafi kusanci da su, da hirar abubuwan da suka sa a gaba a wannan lokacin, da tattauna abubuwan da suka sha musu kai ko wasu matsaloli da suke fama da su; taimakon juna ta kowane bangare; ba juna shawara da karfafa gwiwa da bayyanar da sirrukan zuciyarsu ga junansu; da yin abubuwan yau da kullum tare kamar cin abinci, wasanni, ziyara, sada zumunci da hirar raha da sauransu.
A takaice dai Abota wata dangantaka ce mai kyau mai dadi kuma mai cike da alherai marasa iyaka. Cikakkiyar Abota ita ce wacce aka kulla saboda Allah kadai ba  don wata bukatuwa ta duniya ba; kuma sannan halayen abokan ya zo daya, hakan sai ya haifar da kyakykyawar fahimtar juna da shakuwa a tsakaninsu.
Abota mai rauni kuma ita ce wacce aka kulla a kan wata bukatuwa ta duniya kamar kudi, matsayi, daukaka ko don son burgewa.

Abotayya Cikin Rayuwar Aure
Abota tana da matukar mahimmanci cikin rayuwar aure, domin abota ita ke haifar da shakuwa tsakanin ma’aurata, don haka in ma’aurata ba su zama abokan juna ba, zai yi wuya a samu shakuwa da sabo mai kyau tsakaninsu.

Fuskokin Abotayyar Ma’aurata
1. Shakikan Juna: Su ne ma’auratan da suke da kammalalliya kuma cikakkiyar abota; sun fahimci kowane bangare na rayuwar junansu, tun daga shau’uka, halaye, abubuwan so da ki, karfi da raunin juna da sauransu. Sannan ba su shayin gaya ma junansu dukkan sirrukansu, ba su da abokin shawara da ya wuce su yi da junansu. Suna tsananin bege da kaunar junansu; ba abin da suke rabawa a cikin rayuwar aurensu, komai na kowa ne, ba mai hana daya wani abu daga cikinsu, damuwar daya damuwarsu ce su duka, ba su ware junansu a cikin komai na harkokin rayuwarsu. Akwai tsananin mutunta juna a tsakaninsu ta yadda ko sun samu sabani, bai sa su daina mutunta juna kuma nan da nan suke warware sabanin da ke tsakaninsu.
 
2. Aminan Juna: Ana samun irin wannan abotar tsakannin ma’aurata, ya kasance sun yarda da juna, sun amince ma juna, ba cin amana ba munafinci a tsakanisu, sannan ba su zaluntar juna, amma duk da haka sun sanya wasu iyakoki a cikin dangantakarsu da ba su ketarewa: misali, ba kowane irin sirri ba ne suke iya sanar ma junansu, kamar a ce miji bai san arzikin jakkar matarshi ba, ita ma ba ta san zurfin aljhunshi ba; ko ya kasance abubuwan da Maigida ya san ba su shafi Uwargidansa ba, bai sanar mata ita ma haka; ko ya kasance abokansu ko kawaye su ne abokan shawara ba ya-junansu
3. Masu Fuska Biyu: Su ne wadanda a fili kamar shakikan juna suke, ta yadda ba su iyakance mahimman abubuwa daga junansu ba, suna shawartar juna, suna tattauna abubuwan da ke cikin rayuwarsu ya-junansu, amma a zuci ba su aminta da juna ba, a zuci suna jin haushin juna, a zuci suna zaluntar juna; misali: duk matar da ke fadan laifukan mijinta ga ’yan uwa ko kawayenta, ko mai yin asiri don mallake mijinta, ko namijin da ke bin mata a waje, da sauransu, to komin kyawun dangantakarsu a zahirance, tana da babban gibi saboda wannan mummunan sirri da suke boyewa, wanda in zai bayyana gaba daya, zai share soyayyar da ke tsakaninsu.
4. Abokan Hamayyar Juna: Akwai ma’auratan da abota ta asali ’yar kadan ce cikin dangantakarsu, don haka kodayaushe ba fahimtar juna, ba aminci tsakaninsu, sun zama kamar abokan hamayya. Abin da bai kai ya kawo ba, sai ya haifar da gardandami da  jayayya tsakaninsu.

karin Bayani…
A mafi yawan auratayyun wannan zamanin, an fi samun dangatakar abota ta biyu da ta ukku; watau aminan juna da masu fuska biyu. Shakikan juna da abokan hamayya kuwa su suka fi karanci. Da son samu ne, ya fi dacewa da alfanu a ce dukkan ma’aurata su kasance shakikan abokai, don cimma wannan inganci cikin rayuwar aurensu.
Sai ma’aurata su yi kyakykyawan bincike tare da yin dogon nazari don gano ina ne dangantakar abotayyarsu take da gibi, sannan su da ke da dukkan kokarinsu wajen ganin sun cike wannan gibi don karuwar farin ciki da kwanciyar hankali cikin rayuwar aurensu.
Sai sati na gaba, inshaAllah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.