Sinadaran Soyayyar Ma’aurata (4)
Assalamu Alaikum wa rahmatullah! Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatan Allah SWT Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin. Ga karashen bayani kan sinadaran da suke gina soyayya ta tsakanin ma’aurata. Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatar shi kuma ya zan ya […]
Assalamu Alaikum wa rahmatullah! Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatan Allah SWT Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin. Ga karashen bayani kan sinadaran da suke gina soyayya ta tsakanin ma’aurata. Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatar shi kuma ya zan ya amfanar da su, amin.
4. Kyakykyawar Niyyar Zaman Aure:
Shi ne ya kasance tun farkon aurensu, ma’aurata sun kulla kyakykyawar niyyar yin kwakkwaran riko ga igiyar aurensu; ya kasance tun fil’azal sun yi kudurin, komai zai faru, ba za su taba bari aurensu ya mutu ba. Watau ya kasance ma’aurata na muradin cigaban rayuwar aurensu, komin runtsi, komin tsanani. Wannan sinadari shi ne mafi alfanu ga dadewar rayuwar aure tsakanin ma’aurata. Ko babu sauran sinadaran can ukku da bayaninsu ya gabata, wannan shi kadai yana iya tallabar aure har ya yi tsawon rai na ban mamaki. In ma’aurata suka kuduri aniya, kuma suka sa a ransu cewa za su kasance ma’auratan juna na har abada, komin wuya komin dadi, to wannan zai sa su yin tsananin taka-tsan-tsan wajen kiyaye duk wani abu da zai kawo cikas a rayuwar aurensu kuma zai sa su yi nisan hakuri da juna, a mafi yawan al’amura. In ma’aurata suka sa muradin kasancewa tare na har abada, sama da komai a matsayin burinsu, to za su yi komai na ganin cewa aurensu ya ginu sosai kuma ya kafu sosai; za su dage komin wahala su rike igiyar aurensu, ba za su yi sakaci da ita ba.
Aure ibada ce kamar sauran ibadu, don haka babban abin da ke sa aure ya yi albarka shi ne in ya kasance tun farko an kyautata niyyar cewa za a yi ne don Allah kadai da fatan samun lada daga gare Shi, ba don wata manufa ba. Yin haka samun karin karfin gwiwa ne wajen daure duk wasu matsaloli, wahalhalu da jarabobin da ka iya fadowa cikin rayuwar aure. Kamar yadda komin wuya komin dadi, duk musulmin kirki, zai yi riko ga ibadarsa, kamar Sallah da azumi, to haka ma komin wuyar zaman aure, sai a daure a rike shi gam. Wannan shi zai sa a dace duniya da lahira.
Amma abin takaicin shi ne irin wannan kyakyawar niyya ta yi karanci sosai a irin aurarrakin wannan zamanin. Kwata-kwata ba a bin dokokin addini wajen neman auren da kulla auren da kuma wajen zaman aure. Wannan ya haifar da yawaitar mutuwar aure a wannan zamani. Da yawan ma’aurata ba don kwadayin bautar Allah suke yin auren ba. Suna yi ne don kwadayin wasu abubuwan bukatun duniya.
Raunin wannan sinadari a cikin zuciyar ma’aurata shi ke kawo yawan mutuwar aure, tun farko in ma’aurata sun yi niyyar yin aure na har abada, to komai zai faru za su cigaba da yin riko ga igiyar aurensu. Aure ana yin sa ne har abada ba don a yi a rabu ba, amma da yawan ma’aurata suna aure ne da wata manufa daban a zuciyarsu, wacce ba ita ce ta ‘mutu ka raba’ ba. Wannan shi ke sa matsaloli su yi ta bulluwa cikin zaman aurensu har abin wata ran ya kai su ga rabuwa.
Muradun Da Ke Sa Ma’aurata Yin Riko Ga aure
1. Ingantaccen Muradi: Shi ne muradin son kasancewa tare don Allah kadai da niyyar kyautata ibada ba don wata bukatar duniya mai karewa ba; shi ne ma’aurata su ba rayuwar auratayyarsu muhimmanci sama da komi a rayuwarsu; ta haka ne za su iya dukkan sadaukarwa domin ganin ta ginu, ta kafu kuma ta dore har abada. Ingantaccen muradi ya kasu biyu: akwai masu yin kyakykyawan riko ga aurensu saboda da Allah da girmama ibadar auren da suke yi, kuma suna yin hakan ne cikin dadin rai, ba a kan dole ba, watau ba wata bukatar da ta sa su dole su yi haka din. Akwai kuma masu riko ga aurensu saboda Allah, amma a kan dole, misali ma’auratan da ya kasance sun sami babbar baraka cikin aurensu, amma suna zaune tare zaman hakuri saboda Allah, ba don wata bukatarsu ba, ko kuma irin wadanda iyaye suka tilasta su zama a auren da ba su so, suka daure don yin biyayya ga iyayensu; Maigida ko uwargidan da ake muzguna wa cikin rayuwar aure amma suka daure suna zaman hakuri ko zaman ’ya’ya, saboda Allah.
2. Muradi Na Dole: Shi ne in ya kasance ma’aurata na muradin kasancewa tare kawai don wata bukata tasu, wadda in ba ta, ba za su yin wannan muradin ba. Kamar wadanda suke tare kawai don ’ya’ya, ko don tsoron abin da rabuwarsu za ta haifar cikin danginsu; ko don tsoron surutun mutane; wasu matan na zaune da mazansu ne kawai saboda abin hannunsu ko matsayinsu; wasu kuma mazan suna zaune da matan da ba su jin dadin zama da su, amma ba su jin iya rabuwa da su saboda kyawonsu ko asalinsu.
3. Muradi Na Bogi: Shi ne in ya kasance ma’aurata na muradin kasancewa tare ne kawai lokacin da suke cikin jin dadi da juna, amma da wata ’yar matsala ta taso, ba tunanin da zai fado musu sai na rabuwa da juna. dan abin da bai kai ya kawo ba, sai ya sa uwargida na fadin ‘ni na gaji da wannan aure!’ Ko maigida ya ce ‘meye amfanin zama da ke?’ …da ire-iren wannan. Ma’auratan da suke da irin wannan muradi na bogi da wuya aurensu ya kai labari.
4. Rashin Muradi: Haka kuma akan samu ma’auratan da komai ya ji a rayuwar aurensu, ga soyayya, ga abotayya, ga kuma fahimtar juna, amma saboda ba su ba auren nasu muhimmanci sama da sauran abubuwan rayuwarsu ba, hakan na iya sa aurensu ya kasa tsawon rai; misali: kamar mijin da zai ce dole, sai matarsa ta bar aiki ko wani abu makamancin haka: in ta ki bari har hakan ya kai ga mutuwar auren, wannan ya nuna su duka ba su da muradin auren ke nan. Ita ta ba aikin da take yi muhimmanci sama da aurenta; shi ma mijin ya kasa sadaukar da bukatarsa don dorewar rayuwar aurensu.
Sai sati na gaba, inshaAllah. Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.