Sinawa sun dauki hoto da jaririn biri don neman sa’ar sabuwar shekara
Wani kyakkyawan jinijirin biri ya dauki hankalin mutanen Sin, inda suka rika daukar hoto tare da shi, don neman sa’ar sabuwar shekarar “biri,” da suka shiga.Ranar 8 ga Fabrairun bana, aka shiga sabuwar shekarar biri a kidayar lissafin gargajiyar al’ummar kasar Sin. Mutane da dama sun yi faman samun sa’a idan suka dauki hoto da […]
Wani kyakkyawan jinijirin biri ya dauki hankalin mutanen Sin, inda suka rika daukar hoto tare da shi, don neman sa’ar sabuwar shekarar “biri,” da suka shiga.
Ranar 8 ga Fabrairun bana, aka shiga sabuwar shekarar biri a kidayar lissafin gargajiyar al’ummar kasar Sin. Mutane da dama sun yi faman samun sa’a idan suka dauki hoto da dabbar da ke nuni da martabar sabuwar shekarar. Suna da tabbacin cewa, dabbar za ta kawo musu sa’a har zuwa karsahen shekarar.
Jaririn birin an haife shi ne a wajen shakatawa da kallon namun daji da ke Hangzhou, inda haihuwarsa ta kasance kwanaki 17 kafin sabuwar shekarar, a cewar mai kiwonsa, da ya yi bayanin yadda mutane ke nuna zakuwar son daukar hoto da shi a farkon sabuwar shekara.
Mafi yawan masu ziyartar wurin shakatawar da sun kalli birin, sai furta Kalmomi ne da a harsunan Mandarin da Cantonese na kasar Sin, cewa, Hou Meng! Kalmar da ke ishara da wasan nishadantar da jiki, kodayake a harshen Mandarin ana nufin “kyakkyawan biri,” kuma a harshen Cantonese ma ana nufin mai tsananin kyau.
Saboda tsananin sanyi sai da aka boye birin a wani wurin dumama jiki.