Sinawa sun kwace wa ’yan kasa harkar ma’adinai – Mahaqa Ma’adinai

 A tattaunawar da Aminiya ta yi da Shugaban Kungiyar Mahaka Ma’adinai ta Kasa Kwamared Hamza Muhammad ya yi tsokaci a kan manufar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen farfado da bangaren hakar ma’adinai, sai dai ya koka kan abin da ya kira irin koma bayan da kamfanonin ma’adinai na ’yan kasa suke fuskanta bayan shigowar na […]

Sinawa sun kwace wa ’yan kasa harkar ma’adinai – Mahaqa Ma’adinai

 A tattaunawar da Aminiya ta yi da Shugaban Kungiyar Mahaka Ma’adinai ta Kasa Kwamared Hamza Muhammad ya yi tsokaci a kan manufar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen farfado da bangaren hakar ma’adinai, sai dai ya koka kan abin da ya kira irin koma bayan da kamfanonin ma’adinai na ’yan kasa suke fuskanta bayan shigowar na kasar China (Sin):

 

Aminiya: Mene ne tarihin kafuwar kungiyarku kuma su wane ne mambobinta?

 

Kwamared Hamza: Tarihin kafuwar wannan kungiya ya fara ne tun 1913, tana daga cikin tsofaffin kungiyoyi a kasar nan da aka kafa su kafin samun ’yanci. Sai dai bayan Najeriya ta samu ’yancin kai an sauya mata fasali don ta dace da kasa mai ’yancin kai tare da sauya mata suna zuwa “Nigerian Mine Workers Association,” wato Kungiyar Masu Aikin Hakar Ma’adinai Ta Najeriya. Mambobinta sun kunshi dukan masu aikin da ke da nasaba da ma’adinai kama daga masu hakarsa a tudu ko a ruwa da kuma masu san’anta shi kamar masu nika dutse da abin da ya yi kama da hakan sai kuma masu safararsa kamar direbobi.

Aminiya: Gwamnatin Buhari ta kudiri aniyar farfado da harkar ma’adinai da inganta shi wane tsokaci za ka yi a kai?

Kwamared Hamza: A gaskiya mun ji dadi a lokacin da muka ji labarin, saboda tsari ne da zai samar da dimbin aikin yi ga jama’a sannan ya rage dogaro a kan man fetur wajen samar da kudin shiga ga gwamnati a nan gida da waje. Sai dai kash har yanzu ba a fara tuntubar kungiyarmu ba a matsayinmu na ma’abuta lamarin, bare aji ta bakinmu a kan wuraren da muka fi bukatar dauki. Ba a wuce kamar mako biyu ba muka rubuta takardar koke a kan hakan ga Ma’aikatar Ma’adinai ta hannun Babban Sakataren Ma’aikatar tare da neman a yi gyara a kai, a rika tuntubar koda wakilan kungiyar ne a wajen tsara manufofi ko yin tarurruka don bayyana musu irin abubuwan da suka fi damunmu da yadda za a inganta harkar gaba daya.

Aminiya: Mene ne matsalolin da kungiyarku take fuskanta da kuke bukatar gwamnati ta kawo maku dauki?

Kwamared Hamza: Muhimmai a ciki su ne kutse da kuma babakere da kamfanonin kasar China ke ci gaba da yi kusan a dukan ayyukanmu, wadanda suka bambanta da na kamfanonin waje na baya inda suke gudanar da kusan komai a wannan sana’a da ya hada da sarrafa na’urori da motocin gudanar da aikin a wuren hakar ma’adinai. Abu guda da suke barin ’yan kasa su yi a kamfanoninsu bai wuce aikin leburanci ba. Sannan kasancewar sun shigo da kayan aiki na zamani masu tasiri suna samun saukin gudanar da ayyukansu fiye da masana’antun gida ga kuma rashin bai wa ma’aikatansu cikakken hakkoki irin na sauran masana’antu na ’yan kasashen waje da ke da hadin gwiwa da ’yan kasa. Hakan ya sa yawancin wadannan masana’antu wadanda su suke bai wa ’yan kasa ayyuka masu gwabi kusan duk sun durkushe a yanzu. Wani abin kuma da ya sa kamfanoninmu ba za su iya gogayya da nasu ba shi ne: Kasashensu na bai wa kamfanoninsu da ke aiki a kasar nan tallafin da ya hada da na rancen kudi da kudin ruwansa bai wuce kashi biyu a cikin 100 ba, ga kuma  ba su damar daukar dogon lokaci kafn a biya bashin. Ga tallafin horo da na kayan aiki kamar yadda bincikenmu ya tabbbatar mana. A nan Najeriya kuma mafi saukin bashi da mai gudanar da kamfani irin namu zai samu a wajen gwamnati shi ne rancen kashi tara cikin 100, bayan wannan babu wani tallafi na horo ko makamancinsa da ake tallafa mana da shi, to wannan ya sa kamfanonin ’yan kasa da dama suka durkushe.

Wata matsalar da muke fuskanta da su kuma ita ce yadda kamfanoninsu suke  tauye hakkookin mambobinmu da suka baiwa kananan ayyuka. Sai da muka yi da gaske kafin suka amince suka bar su shiga kungiyarmu bayan mun tilasta musu hakan ta hanyar rufe duk wani kamfani da ya hana ma’aikaci shiga kungiyar, sannan suna kauce wa biyan haraji ga gwamnati, sabanin kamfanonin farko na Turawa da suke da hadin gwiwa da ’yan kasa.

Aminiya: Wane darasi kake ganin kasar nan za ta koya daga gare su domin inganta harkar?

Kwamared Hamza: Abu guda da dole ka yaba wa kamfanonin na China shi ne jajircewarsu a aiki da kuma sanin makamarsa. Kirana ga ’yan kasa da suke da sha’awar kafa kamfanin hakar ma’adinai shi ne su dauki kwararrun mutane da suka san aikin a wajen jagorantar kamfanonin, maimakon abin da ke faruwa a mafi yawansu da suke daukar ’yan uwansa da ba su san aikin ba. Sannan ba za su nuna kwazo ba a kai sabodaa babu mai tsawatar musu idan suka yi ba daidai ba, a sakamakon wadannan dalilai sai ka ga kamfanin ya durkushe bayan ’yan shekaru kadan da bude shi.

Aminiya: A karshe wane irin ci gaba za ka ce wannan kungiya taku ke samarwa ga mambobinta?

Kwamared Hamza: Muna tilasta wa kamfanonin hakar ma’adinai samar da matakan kariya ga ma’aikatansu kamar ba su abubuwan da za su sanya a lokacin aiki da ake kira “Safety Wares” a hanci ko a hannu ko a kai da kuma ba su madarar-ruwa bayan sun tashi daga aiki. Sannan idan tsautsayi ya rutsa da su mu tabbatar da an dauki dawainiyar jinyarsu ko kuma biyansu diyya. Sannan tsare-tsare sun yi nisa wajen sama wa kungiyarmu hedkwata ta dindindin a nan Abuja, saboda a baya hedkwatar tana garin Jos ne sannan bayan a dawo da ita nan Abuja har yanzu ba mu samu wuri na kanmu ba.

Martanin Ma’aikatar Bunkasa Sha’anin Ma’adinai

Yunkurin jin ta bakin Ma’aikatar Bunkasa Sha’anin Ma’adinai kan zargin kungiyar game da ayyukan kamfanonin China da kuma ikirarinta na mika takardar koke da neman sanya kungiyar a tsara al’amuran ma’adinai ga ma’aikatar bai samu nasara ba. Lokacin da wakilinmu ya nemi jin ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar Alhaji Muhammad Abbas, an nemi ya bi ta hannun Babban Jami’in Hulda da Manema Labarai na Ma’aikatar inda shi kuma ya bukaci a rubuto masu wasika a kan hakan tare da ba su lokacin bayar da nasu bahasi.

Sai dai wata majiya a ma’aikatar da ta bukaci a sakaya sunanta ta gaskata zargin da a ke yi wa kamfanonin na China na kin biyan haraji da kuma babakere a aiki a dukan al’amura, inda ta ce yawancin masu aikin kwadago da kamfanonin suke kawowa wadanda aka sake ne daga kurkuku kuma tsofaffin masu laifi. Sai dai majiyar ta ce shugabannnin kamfanonin na sayen lasisin hakar ma’adinai ne daga ’yan kasa sannan su zuba na’urorinsu na aiki inda suke ba su kamar kashi 30 cikin 100 na ribar da suka samu sannan su kwashe ma’adinansu cikin dare zuwa bakin ruwa ba tare da hukumar ta karbi harajinta ba, kuma daga can su kai kasarsu inda a ke sarrafa shi.