Sinawa sun shirya gasar fadan dawaki don murnar sabuwar shekara

Al’ummar Sinawa sun yi bikin sabuwar shekararsu da gasar karon battar dawakai, inda dimbin ’yan kallo suka taru a Kudancin kasar Sin suka kalli fadan dawaki. Wannan sabuwar shekarar an yi mata lakabi da shekarar doki.A wajen wasan fadan dawaki, mutanen na ganin kofaton dawakai na harbin iska. Su kuwa ’yan kallo sai su yi […]

Sinawa sun shirya gasar fadan dawaki don murnar sabuwar shekara

Al’ummar Sinawa sun yi bikin sabuwar shekararsu da gasar karon battar dawakai, inda dimbin ’yan kallo suka taru a Kudancin kasar Sin suka kalli fadan dawaki. Wannan sabuwar shekarar an yi mata lakabi da shekarar doki.
A wajen wasan fadan dawaki, mutanen na ganin kofaton dawakai na harbin iska. Su kuwa ’yan kallo sai su yi ta shewa.
Mazaunan kauyen Tiantou da ke gundumar Guangdi, sun saba gudanar da wannan al’ada kimanin shekara 500, inda dawakai ke fafatawa da juna a kan wanda zai mallaki godiya.
A cewar Mista Pan Jianming, wanda bakin dokinsa da ya make abokin karawarsa: “Idan har ba a yi fadan dawaki ba, sai mu ga kamar ba sabuwar shekara ba ce.”
 “Ya tsaya a tsaye cak, ya mangari daya dokin,” inji Mista Pan dan shekara 31, kuma mai sana’ar gyaran na’urar sanyaya daki.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan