‘Sirrin Da Ke Raina’ ya hada Nafisa da Rahma Sadau kishi
Fim din ‘Sirrin Da Ke Raina’ na Kamfanin FKD Production da aka kammala daukarsa a ranar Larabar makon jiya a Abuja ya hada fitattun jarumai mata Nafisa Abdullahi (Sai Wata Rana) da Rahama Sadau (Priyanka) kishi.Labari ne a kan Fahad (Ali nuhu) da Yesmin (Nafisa Abdullahi), inda tun suna kanana suke son junansu, har suka […]

Fim din ‘Sirrin Da Ke Raina’ na Kamfanin FKD Production da aka kammala daukarsa a ranar Larabar makon jiya a Abuja ya hada fitattun jarumai mata Nafisa Abdullahi (Sai Wata Rana) da Rahama Sadau (Priyanka) kishi.
Labari ne a kan Fahad (Ali nuhu) da Yesmin (Nafisa Abdullahi), inda tun suna kanana suke son junansu, har suka girma ba su daina ba. Suna cikin tsaka da soyayyarsu sai iyayensa suka biya masa kudin karatu zuwa kasar waje, duk da haka kafin ya tafi sai da suka yi wa juna alkawarin rike soyayyarsu ko ana ha-maza-ha-mata.
Duk da cewa ya yi nesa da Yesmin amma ya rike sonta a zuciyarsa har zuwa lokacin da ya kammala karatunsa ya dawo. A ranar da ya dawo Najeriya; a ranar ya nufi gidansu, aka ce masa tana makaranta, ya tafi makaranta don nuna mata soyayyar da ya dawo mata da ita.
Ita kuma ta nuna halin ko in kula a kansa. kawarta Rumaisa (Rahama Sadau) ta ba shi kulawa. Yana son Yesmin ta ba shi dama su nuna wa kansu soyayyar da ke tsakaninsu, amma ita karatu ya fiye mata, ba ta da lokacin yin soyayya. Daga karshe ya hada baki da Rumaisa suka fara soyayyar karya.
Daga baya Yesmin ta dawo hayyacinta. Ranar da ta bukaci su ci gaba da soyayya, a ranar Rumaisa ta tabbatar masa da gaske take sonsa, ba ta kuma dauki al’amarin da wasa ba.
Daga nan rikici ya biyo baya; alaka ta lalace, aka rika artabu. Kishi mai tsanani ya wakana tsakanin Yesmin da Rumaisa. Wace ce take samun nasarar auren Fahad? Wannan sai a jira ranar da fim din ‘Sirrin Da Ke Raina’ zai fito.
Kamfani: FKD Production, Labari: Ali Nuhu; Tsarawa: Jamil Nafseen da Ali Nuhu, Furodusa: Almah Junior.