Sirrin mallakar miji: kissar wata mata
Assalmu Alaikum. Yau ma kamar kowane lokaci ina dauke da wannan maudu’i wanda ya zama wajibi a gare mu, mu fadakar da mata a kan hakkokin mazansu da ke kansu wadanda tsare su ne babbar hanyar mallakar miji ba tare da boka ko malam ba. A kowane lokaci na fuskanci mata a kan wannan gaba […]
Assalmu Alaikum.
Yau ma kamar kowane lokaci ina dauke da wannan maudu’i wanda ya zama wajibi a gare mu, mu fadakar da mata a kan hakkokin mazansu da ke kansu wadanda tsare su ne babbar hanyar mallakar miji ba tare da boka ko malam ba.
A kowane lokaci na fuskanci mata a kan wannan gaba nakan fada musu cewa “Kyautatawa gami da tsare wa maza hakkokinsu ne babbar hanyar mallake miji.”
Wata mata ce ta je wajen wani malami (mai tsoron Allah) ta ce masa “Allah Ya gafarta Malam so nake ka yi min aiki domin in mallake mijina.”
Sai malamin ya girgiza kai yana mai nuni da jan aikin da ke akwai. Ya ce mata zai yi mata aiki amma da sharadin in za ta kawo masa nonon barewa wanda ta tatso da hannunta.” An ce sa kai ya fi bauta ciwo.
Matar nan ta yi shirya ta nufi dokar daji kuma ta yi sa’a ta iske wata barewa ta yi sabuwar haihuwa, sai ta samu wata itaciya ta haye sama ita kuma barewar da ’ya’yanta suna kasa.
Sai ya kasance duk lokacin da barewar nan ta tafi neman abinci sai matar nan ta sauka ta dauke ’ya’yan nan daya bayan daya ta aje su gefe guda ta share musu wurin, ta dauke su ta mayar da su wurinsu na asali.
Duk lokacin da uwar ta dawo sai ta iske an share wajen sai ta yi mamaki, har ta kai matar nan tana jinkirta sharar nan har barewar ta dawo ta iske ta tana wannan aiki, haka za ta sa mata ido sai ta gama ta mai da su inda suke.
Yau da gobe har ta kai matar nan tana shafa ’ya’yan barewar nan in suna shan nono har tana iya cire wani daga jikin nonon ta sanya wani.
In gajarce muku labari saboda kyautatawa har matar nan ta zama tana sarrafa barewar nan duk yadda ta ga dama. A karshe ta dauko ’yar gorarta ta kara jikin nonon barewar nan ta tatsa ta cika ta tattara kayanta sai gida.
Bayan ta koma gida sai ta shirya ta nufi wajen malamin nan rike da gorar nono ta mika masa.
Koda ya amsa sai mamaki ya kama shi ya tambaye ta yaya aka yi kika same shi? Matar nan ta share wuri ta fada masa duk hanyoyin da ta bi har ta samu ta cimma burinta. Sai malamin nan ya gyara zama ya ce ta saurare shi da kyau da kunnen basira. Ya ce “Har ga Allah duk abin da zai yi mata ba zai yi tasiri ba matukar ba ta bi mijinta ba ta kuma kyautata masa kamar yadda ta yi wa wannan barewa.”
Sai mamaki ya kamata ta ce “Ka fa san maza yadda suke da wuyar sha’ani.” Sai malamin ya ce “Ta je ya ba ta nan da wata guda idan har ta aikata kwatankwacin abin da ta yi wa barewar nan ba, ta samu kan mijinta ba to ta dawo shi kuma zai yi mata aikin da za ta mallake shi har abada.” Suka yi ban-kwana ta yi masa godiya ta koma gida.
Bayan tsawon wata guda sai ta koma wajen malamin nan rungume da jaka wadda ta shake da kayan arziki ta mika masa kuma ta nuna farin cikinta ganin mafarkinta a yau ya zama gaskiya.
Daga karshe Malam ya ce mata “Wannan shi ne asirin da har abada ba zai kare ba, sai ma karin tagomashi na yardar Allah da za ki samu.” Domin Annabi (SAW) ya ce “Duk matar da ta mutu alhali mijinta yana mai yarda da ita to za ta shiga Aljanna.”
Da wannan nake kira ga matanmu su ji tsoron Allah. Wallahi zuwa wajen boka kafirci ne kuma duk wacce ta mutu a wannan tafarki wuta ce makomarta.
Allah Ya tsare mana imaninmu, Allahumma amin.
Sanusi Hashim Abban Sultana, Jihar Katsina. 08065507271.