Sirrin samun nasarata -Ali Nuhu
Ali Nuhu jarumi ne wanda ba ya bukatar wata gabatarwa, musamman saboda shahararsa a fagen shirin fina-finan Hausa. Ta kai ana yi masa kirari da ‘Sarki.’ Ya kuma kasance zakaran da za a iya cewa ya fi kowane jarumi samun nasarar daukar kambu a duk wani nau’in gasa da ya shiga. Ali ya samu nasara […]
????????????????????????????????????

Ali Nuhu jarumi ne wanda ba ya bukatar wata gabatarwa, musamman saboda shahararsa a fagen shirin fina-finan Hausa. Ta kai ana yi masa kirari da ‘Sarki.’ Ya kuma kasance zakaran da za a iya cewa ya fi kowane jarumi samun nasarar daukar kambu a duk wani nau’in gasa da ya shiga. Ali ya samu nasara a gasar Afro-Hollywood Award da aka yi a Landan da AMMA Award da Arewa Mobies Award da sauransu. A tattaunawarsa da wakilinmu Jarumi Ali Nuhu ya bayyana sirrin daukakarsa da wasu batutuwa da suka shafi sana’arsa ta fim.
Kana daya daga cikin mutanen da suka fara yunkurin hade masana’antar shirya fina-finai ta Arewa ko ta Hausa da aka fi sani da Kannywood da takwararta ta Kudu wato Nollywood. Me ya sa ka yin wannan yunkuri?
Kamar yadda kowa ya sani ne, Kannywood na da tsari irin na masana’antar shirya fina-finai ta Bollywood da ke Indiya, yadda Bollywood ke daukar kamanni irin na Hollywood da ke kasar Amurka. Bisa wannan doron, dole ne ka ga bambance-bambance a yadda kowane ke gudanar da ayyukansa. To amma abin da muka manta a nan shi ne, Kannywood ko Nollywood duk dai masana’antu ne na Najeriya.
Idan aka duba za a ga cewa akwai bukatar a hadu a hada karfi da karfe don a fitar da wani abu kwakkwara.
Saboda haka ne muka ga ya dace mu bijiro da wannan yunkuri don a hada karfi wuri guda a samar da wani sabon yanayi wanda zai haifar da hadin kai da fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu. Alhamdulillahi, wannan yunkurin namu ya samu karbuwa daga ’yan kallo sosai, kuma ana nan ana ta kwaikwayar irin wannan aikin.
Yaya aka yi aka samu nasarar wannan yunkuri duk da irin wadancan bambance-bambancen da ka lissafa a baya?
Na farko dai a matsayina na jarumi na yarda da kwarewa a duk wani fanni da mutum ya zaba wa kansa. Saboda haka, kamar yadda na sha fada ne cewa dole a jinjina wa masa’antar Kannywood bisa jajircewarta wajen ganin an dabbaka wannan sana’a duk da cewa ba mu da kwarewa da samun horo a kan aikin musamman idan aka kwatanta mu da takwararmu da ke Kudu.
Na biyu, mu dai burinmu shi ne a samar da wani sabon tsari da zai tafiyar da wadannan masana’antu biyu mabambanta bisa gwadabe daya.
Tabbas, akwai bambance-bambance, to, amma mu dai burinmu shi ne mu samar da wani sabon salon kaiwa ga gaci a cikin tsarin sana’armu ta fim, sai kuma ga shi ga dukkan alamu hakarmu za ta cimma ruwa.
A da Ali Nuhu ne a Nollywood amma sai ga shi yanzu ’yan Nollywood ne ke shigowa Kannywood. Ko dai abin cude-ni-in cude-ka ya koma?
Komai a wannan rayuwar sai da gwaji, bisa dubi da muka yi da yadda al’amura ke tafiya a masana’antar fim, sai muka ce to me zai hana mu gwada wannan gamin- gambizar mu gani.
Cikin ikion Allah sai ga shi bisa irin fahimtar juna da ke tsakanin masana’antun biyu, al’amura sun wakana yadda muke zato. A gaskiya wannan yunkuri ya samar mana da samun alheri a wannan tafiyar. Kuma ga dukkan alamu masu kallo sun gamsu da wannan alakar.
A kwanakin baya kamfanin wayar sadarwa na Samsung ya nada ka jakadansa. Bayan wannan kamfani akwai wasu kamfanonin da kake musu yi wannan jakadanci. Ya kake hada wannan aikin na jakadanci da kuma sana’arka ta fim ba tare da daya ya tagayyara ba?
A gaskiya abin ba sauki, domin (dukkansu biyu) abubuwa ne masu bukatar lokaci sosai. Saboda haka ya zama dole mutum ya rika tsara yadda yanayin ayyukansa zai rika gudana. Koda yake akwai fahimtar juna tsakaninmu da masu shirya fina-finai wanda hakan ke sawa su rika daga mana kafa idan an samu cinkoson bukatu tsakaninsu da mu.
Babban abin damuwar shi ne yadda al’amuran iyalanmu ke samun tangarda, ta yadda za su shafe kwanaki ba su gan ka ba, ko kuma ka fita tun safe sai kusan tsakar dare za ka dawo. To Amma, mun gode wa Allah da yake akasarin matanmu sun fuskanci irin yanayin aikin namu.
Ka zama zakaran gwajin dafi a wannan sana’ar ko mene ne sirrin?
Babu wani sirri wanda ya wuce ikon Allah, haka Ya tsara kuma hakan ake yi. Ni kaina ban taba tunanin zan kai matakin nan da Allah Ya sa na taka ba, domin ban shigo wannan harka da zimmar ta zame min sana’a ba. Kai har mahaifina ya taba nema min aiki da Gwamnatin Tarayya, to, amma harkar fim ita Allah Ya nufa zan yi har in kai ga wannan matsayi.
Kana daya daga cikin jaruman da ke sa ’ya’yansu cikin wannan harka ta fim. Shin wanna bukatarsu ce ko bukatarka?
Ni dai ’ya’yana suna wannan haka ne don suna da ra’ayin harkar. Bugu da kari, dukkansu karatu suke yi a halin yanzu.
Ba ka ganin tunda karatu suke yi harkar fim na iya durkusar da karatun nasu ko ya zamanto sun samu takura?
Tabbas al’amarin akwai takura kawarai, musamman daga ’yan kallo masoya wadanda ke kallon wadannan yara a matsayin jaruman gobe. Misali, ’yata wacce take mai matukar kunya takan samu kanta cikin yanayin takura a duk lokacin da masoya fina-finan Hausa suka ritsa ta da tambayoyi, a wasu lokutanma sai kanenta Ahmad ne ke zame mata tamkar lauya don ya fi ta surutu.
To amma ta fannin harkar karatunsu, ba na bari sha’anin fim ya ratsa ciki. Saboda haka ne ma ba sa yin fim in ba hutun makaranta ake yi ba. Saboda haka duk wanda yake son za su yi masa aiki, to, sai ya bari in an yi hutu sai ya zo da labarinsa ni kuma in duba, in kuma shawarce su a kai, duk da cewa sai na amince da labari kafin su yi aikin wannan labarin. A wasu lokutan ma da kansu suke cewa ba za su iya yi ba, saboda suna ganin bai dace da su ba.
Ka kasance gaba-gaba wajen bijiro da sababbin fuskoki a cikin wannan sana’ar. Ko me ya sa hakan?
To idan ba mu ba sababbi dama ba, mu za mu zauna ne har abada? Ai dole ko muna so ko ba ma so mu sani cewa tabbas wata rana ba mu, imma tsufa ko mutuwa ko kuma ma tsarin ya sauya ya ajiye ka. Saboda haka dole ne mu nemi yadda wannan masana’anta za ta zama mai gudana ta yadda kowane mai fikira da fasaha da kuma ra’ayi zai iya zuwa don neman na kalaci.
Misali, dubi babban jarumin nan Adam A. Zango wanda zan iya cewa ni na kawo shi da’irar fina-finan Hausa; da farko ya fara a matsayin mai buga kida, to, amma sai na fuskanci cewa yana da waat fikira wacce ta wuce harkar kida kawai. Domin na lura cewa baiwar da Allah Ya yi masa ba ta bayan kyamara ba ce, baiwa ce wacce ya kamata a ce tana gaban kyamara. Saboda haka na tuntube shi da wannan maganar ya kuma amince. A yau ga inda Adamu ya kai, saboda haka dole mu rika surkawa har mu samu magada a harkar.
Ko Ali yana goyon bayan yunkurin tsabtace masana’antar Kannywood na baya-bayan nan?
Gyara fa ka ce? Tabbas ina bayan duk wani yunkuri da zai kare mana kima, mutunci da kuma darajarmu dari bisa dari.
Wasu na ganin zafin matakin da aka dauka a kan Jaruma Nafisa Abdullahi sakamakon laifin da ta yi. Me ra’ayinka a kan wannan batun?
Abin da ya sa aka ga na yi shiru a kan wannan maganar shi ne, ni dai kusan a iya cewa uban gida nake ga wannan jaruma kuma uba a wannan masana’anta. To, amma duk abin nan da ake yi babu wani ko wata a kungiyan ce da ya taba tuntuba ta da wannan magana. Hakazalika ita kanta yarinyar ba ta taba koda a waya ta bayyana min abin da take fuskanta ba; saboda haka ni ma na ja bakina na yi shiru.
Mene ne gaskiyar maganar samun nasararka na shiga gasar Nigerian Entertainment Award wanda za a yi a New York da ke kasar Amurka?
Wannan magana haka take, ina kuma fatan masoyana za su taya ni da addua’ar Allah Ya ba ni nasara. Domin nasarata ba tawa ba ce ni kadai, nasara ce ga Arewa ga kuma Najeriya baki daya.