Sirrin soyyar talakawa ga Shugaba Buhari?

So Wani nau’in sinadarine da Allah Madaukakin Sarki kan sanya a zukatan masoya, ba tare da la’akari da kudi ko rashin kudi wanda kake so ba. A nan ina maganar irin soyayyar da ke tsakanin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma talakawa, wanda talaka ke nuna masa tsintsar so, so da suke ba don komai […]

Sirrin soyyar talakawa ga Shugaba Buhari?

So Wani nau’in sinadarine da Allah Madaukakin Sarki kan sanya a zukatan masoya, ba tare da la’akari da kudi ko rashin kudi wanda kake so ba. A nan ina maganar irin soyayyar da ke tsakanin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma talakawa, wanda talaka ke nuna masa tsintsar so, so da suke ba don komai ba, sai ganin ya kasance, zaki a wajen fada da masu yi wa kasa zagon kasa, ya kuma zama zomo a wajen guje wa rashin gaskiya da wawurar dukiyar kasa.

Tun bayan sanarwar da mai magana da yawun Shugaba Buhari, kan kafafen yada labarai Femi Adesina ya fitar cewa, ranar Asabar 19 ga watan Agustar shekarar 2017, ranar ce Shugaba Buhari zai dawo daga jinyar da yaje a Landan, ranar takasance cikin kundin tarihin miliyoyin masoya, inda masoyansa musamman talakawa, suke zumudi tare da gudanar da addu’oin ganin saukar jirgin da ya dauko masoyinsu ya saukar da masoyinsu lafiya. 

Daga nan talakawa suka rika aiwatar da shagulgula da bukukuwa a sassa daban-daban na fadin Najeriya, domin murnar dawowar Shugaban kasa Muhammad Buhari daga jinyar da yaje a Landan, galibi suka aiwatar da bukukuwa na kade-kade da raye, yayin da wadansu suka rika sadaukar da sana’o’in su kyauta, ga jama’a, duk a shagulgulan dawowar Shugaban kasa Muhammad Buhari, misali a Jihar Bauchi, an yanka rakumi, Jigawa wasu direbobi sun rika jigilar fasinjoji kyauta, a Kaduna wani asibiti ya dauki nauyin yi wa marasa lafiya tiyata a kyau, da sauran masu kananan sana’oi da kafofin yada labarai suka rika ruwaito irin yadda dimbin masoya Buhari suka rika gudanar da shagulgulan dawowar sa lafiya.

Haka zalika ranar Litinin 21 ga watan Agusta, ita ma wata muhimmiyar rana ce da ta kasance abin alfahari ga dimbin masoya cigaban Najeriya, domin a ranar ne Shugaban kasa Muhammad Buhari ya gabatar da jawabin farko tun bayan dawowar sa daga london, inda a cikin takaitaccen jawabi amma mai muhimmanci, ya soma da godiya ga Allah (S.W.T) da ya ba shi lafiya, tare da ikon dawowa gida Najeriya, tare da dubban ‘yan kasa da suka rika yi masa addu’oin samun zaman lafiya, a lokacin da yake jinya a london, kana ya tabo lamarin da ya shafi maganar raba kasa, inda ya yi tsokaci kan zaman da suka taba yi da jagoran kafa Biafara na wancan lokaci a wata ziyarar da ya kai masa a shekarar 2003, inda suka tattauna muhimman lamurran kasa, tare da amincewa da Najeriya ta zama dunkulalliyar kasa,  wanda idan muka duba ko shakka babu maganar na da muhimmanci, musamman a yadda aka san Najeriya, da ‘yan Najeriya da hadin kai, da kuma kokarin ganin Najeriya ta kasance a matsayin dunkulalliyar kasa, kuma uwa daya uba daya, kamar yadda wani mawaki ke fada a wakarsa a matsayin:

“Hausa, Igbo, Yoruba, a Najeriya kasa daya, uwa daya uba daya, mu hada kai mu bar kabilanci na addinin ko na siyasa”. 

A nan yana da kyau, dukkan kabilun Najeriya musan muhimmancin kasancewar Najeriya a matsayin kasa daya domin samar da cigaba da za mu iya gogayya da takwarorin mu (Sauran kasashen duniya). Duk a cikin jawabinsa ya tabo abin da ya shafi tsaro, wanda muhimmancin tsaro ba ya misaltuwa ga duk dan kasa nagari, da ke son ganin cigaba da kuma samuwar ci gaba da kwanciyar hankali, inda ya yi jinjina ga Jami’an tsaron Najeriya, bisa irin gagarumar gudunmuwar da suke bayarwa na tabbatar da tsaro a Najeriya, tare da tsokaci kan abin da ya shafi masu satar shanu da kuma garkuwa da mutane, wanda yana da kyau, gwamnati ta yi kokarin ganin ta samo mafita game da matsalar.

A nan dukkan jawabansa na da matukar muhimmanci ga cigaban kasa da kuma ‘yan kasa, musamman Shugaba Buhari da ya zama gwarzo, masoyi, kana abin koyi ga talakawa, bisa irin jajircewar sa na ganin cewa talaka ya dara, kuma najeriya tayi bankwana da cin hanci da rashawa. Shugaba Buhari ya zamo Ikon Allah, ganin irin yanda a wannan lokaci da muke ciki, ba wani shugaba da ya samu soyayyar talakawa kashi 100% cif, tun lokacin da yake takarar son zama shugaban Najeriya a 2003 har izuwa 2015, da Ubangiji mai bayar da mulki ga wanda ya so a kuma lokaci da ya so, ya ba Shugaba Buhari, dama da ikon jagorantar ‘yan Najeriya a matsayin shugaba, har lokacin da Allah ya jarabe shi da rashin lafiya har zuwa wannan lokaci da, Allah ya ba shi lafiya ya kuma dawo cikin iyalansa, mosoya, da ma makiyansa. 

Tun bayan karbar ragwamar mulki da ya yi a shekarar 2015, Shugaba Buhari ya samar da cigaba musamman ta fannin tsaro, da kuma kokarin da yake na yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, dake zama ciwon da ya dabaibaye cigaban Najeriya, ganin irin illolin da ya yi ga kasar mu Najeriya.

A nan nake janyo hankalin shugabanni da ke son samun soyayyar talakawa, da su yi koyi da halayen Shugaba Buhari, tare da rike sirrin cewa, ita soyayyar talakawa a kyauta ake samunta, sai dai samun ta, sai dai makaman samun ta dinne ke da matukar daci, ta hanyar kasancewa masu gaskiya da adalci, a sha’anin shugabanci, da kuma kokarin kyautawawa talakawa, ta haka ne za ka samu soyayyar talakawa, ba ta hanyar wawure dukiyar talakawa ba.

Comred Aminu Dankaduna Amanawa. 09035522212./07065654787. [email protected] Aminu Dankaduna Amanawa [email protected]