Sitiyari a hannun mahaukata?
daya daga cikin jawaban da mai bayar da lasisin tukin mota ko kuma wani abin hawa ke yi wa wanda aka tabbatar da cewa ya cancanta a ba shi lasisi, bayan duk an bi matakan koyar da shi ko ita, shi ne; “a kula, ka dauki kanka a matsayin kai kadai ne MAI HANKALI a […]
daya daga cikin jawaban da mai bayar da lasisin tukin mota ko kuma wani abin hawa ke yi wa wanda aka tabbatar da cewa ya cancanta a ba shi lasisi, bayan duk an bi matakan koyar da shi ko ita, shi ne; “a kula, ka dauki kanka a matsayin kai kadai ne MAI HANKALI a bisa titi, sauran direbobi da ke kan hanya kuma ka dauke su a matsayin duk MAHAUKATA ne. Idan dukkan dirobobi suka amince da haka, wato kowane direba shi ne MAI HANKALI, wancan da ba ni ne ba, MAHAUKACI ne, to za a samu kula da tsaro a lokacin tuki.”
Babbar manufar wannan huduba da ake yi wa sababbin direbobi ita ce, idan mai tuki ya dauki kansa a matsayin shi kadai ne mai hankali, sauran direbobi kuwa duk mahaukata ne, to an bi matakin bin doka da oda. Ma’ana, kowane direba da ya dauki gaskiyar batun da ke nuna shi ne kadai mai hankali, to da zarar ya ga wani direba na tahowa, ya dauke shi a matsayin mahakaci, to da alama zai rika yin taka-tsantsan, bisa wannan yanayi, an kawar da tunanin mugun tuki ko ganganci ko wasa ko son nuna iyawa ko kuma tukin da zai iya kai ga hadari ko makamancin haka.
Irin wannan tunani shi ne ke sa kowane direba ya san abin da yake yi, yakan kuma kasance mai kula da lura da kokarin ganin bai saba ko karya dokokin tukin abin hawa ba. Ke nan idan na amince cewa ni mai hankali ne, shi ma wancan direba ya amince shi ma mai hankali ne, haka kuma duk mun yarda cewa abin nan da muke yi shi ne a’ala, to samun barin mota ko hadari ko kauce ka’idojin tafiya bisa tituna zai ragu.
To, amma shin abin da ke faruwa ke nan yanzu a tsakanin matukan abin hawa a kasar Nan? Shin mun yarda cewa mu masu hankali ne a lokacin da muke tukin abin hawa ko kuwa mun amince da cewa sauran mutane su ma masu hankali ne da muke cin karo da su a lokacin tukin abin hawanmu? Ko kuwa dai abin da ke faruwa a halin yanzu abin nan ne da za mu iya cewa sitayari ne a hannun mahaukata ba masu hankali ba?
Kafin mu samar da amsoshin wadannan tambayoyi da ma wasu irin su, ya dace mu fahimci cewa shi mai bayar da lasisin tukin motar can da muka ambata, yana magana ne da wadanda suka yarda aka gwada su, aka nuna masu dokoki da ka’idoji da nusar da su game da alamomi da isharori na tuki da wadanda ke kan hanya. Shi wannan jami’i da ke wannan jawabi, a tuna yana magana ne da wadanda suka koyi mota a bisa tsari da yadda doka ta tanada ba wai wadanda suka yi wa harkar haye ba. Saboda haka bisa wannan yanayi ne ya dace mu dubi maganar direba MAI HANKALI da direba MAHAUKACI.
Ke nan dukkan direbobin da suka dace su tasirantu da wannan huduba su ne wadanda suka san kan tuki da ka’idoji da dokoki, ba wai kowane karabitin direba ba. Ashe idan mun ce wancan jawabi ba ga kowane direba ya kamata ya fada ba, ba mu yi laifi ba, domin ana magana da direbobin gaskiya ne, ba je-ka-na-yi-ba!
A cikin irin halin da muke ciki a yau, idan aka ce direbobin da muke da su a kan tituna ba masu hankali ba ne, ba a shara ta ba. Ta yaya za su kasance masu hankali, alhali ba su bi matakan koyon tukin kamar yadda doka ta tanada ba! Ta yaya za su kasance masu hankali alhali ba su san bambancin tuki hannun dama ko na hagu ba! Ta yaya za su kasance masu hankali, alhali ba su san gwadaben da ya dace su bi domin gudanar da tukin nasu ba, ganin cewa ba kowa ya san bambancin mai tafiya da shiga ta hannun hagu ko akasin haka ba? Ta yaya za mu samu direbobi masu hankali alhali kuwa direban nan da ke fama da sitayari bai kai ko shekara 18 ba, bai mallaki hankali ba, bare ya kasance direban kwarai, uwa-uba kuma wanda ya koya masa motar ko babur din ko keken hawan shi ma wani ‘tababben’ ne ya koyar da shi daga cikin gidansu, wani ko kan titi bai taba fita, sai ranar da aka ce da shi zo ka hau, ai ka iya? Ta yaya za mu samu direbobi masu hankali alhali masu tukin su kansu, ba su dauki abin hawan nasu ai yana da hankali ba, balle a yi masa yadda ya dace don samun sa’ida! Ta yaya?
Saboda haka abin da ke faruwa a cikin kasar nan dangane da ababen hawa bai wuce abin nan da Bahaushe ke cewa kura ta gudu daga hannun gardi, baki bude ba! Ma’ana makasa ne ke yawo a cikin titunan al’umma. Mafasa ke kai hari a cikin shaguna ko gidajen al’umma. Mahaukata ne ke yawo da sitiyari a hannu domin tattake duk wanda tsautsayi ya kasance zai fada kansu, a zo kuma ana cewa ai abin daga Allah ne, alhali mu ne da kanmu muke daukar wuka muke soka wa kanmu, mu koma gefe guda muna ihun mun yi abin a zo, a gani!