Siyasa ba hauka ba ce
Siyasa ba hauka ba ce, siyasa da ita ake samar da masu mulki, adalai a danka musu amanar dukiyar kasa da kiyaye rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addini na kowane dan kasa da wadanda suke zaune a cikinta da masu shigowa su fita. Shugaban Kasa shi ne wuya ko kan gwamnati kasancewar […]
Siyasa ba hauka ba ce, siyasa da ita ake samar da masu mulki, adalai a danka musu amanar dukiyar kasa da kiyaye rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addini na kowane dan kasa da wadanda suke zaune a cikinta da masu shigowa su fita.
Shugaban Kasa shi ne wuya ko kan gwamnati kasancewar duk hukumomi suna karkashinsa yayin da shi kuma yake karkashin ’yan kasa baki daya, ba iyali ko ’yan uwa ko abokai ko ’yan jam’iyyarsa ba ko wadansu tsirarun jam’iyyu abokan gwamnati. Kowane dan kasa yana da hakki daidai da kowa. Masu rike da madafun iko da masu kudi da sarakuna da malamai da talakawa almajirai da nakasassu duk daidai suke a gaban shari’a da dokokin kasa, babu wanda yake da fiffiko idan ana maganar adalci.
Sabanin yadda muke a Najeriya yanzu, wadansu sun fi karfin a bincike su ma balle a hukunta su kan laifuffukan da suka aikata, ko suke ci gaba da aikatawa. Irin wadannan mutane suna iya kasancewa a bangaren ’yan adawa da kuma na kusa da Shugaban Kasa. Kuma na kusa da kowane Shugaban Kasar da suke aikata ba daidai ba, sukan kange Shugaban daga jama’a su hana kowa isa gare shi, sai su, sai masu laifi irinsu domin kada asirinsu ya tonu, alhali duk abin da suke ciki an sani. Haka suke yi a kowane lokaci a kuma kowace gwamnati. Shi ya sa mutane da yawa irina da muka san halin da ake ciki, muke ta yin magana a madadin wadanda ba su sani ba.
Galibi makusantan shugabannin kasa sukan dauki wani salo na daukar nauyin ma’aikatan siyasa marasa ta-ido suna rika shiga gidajen rediyo suna cin mutuncin masu mutunci da suke kokarin mayar da shugabannin kan turbar kwarai. Alhali ana nusar da shugabannin ne a madadin wadanda aka zalunta da ba su da kowa da zai tsaya musu su fadi abin da ya dame su balle a magance musu. Wannan shi ne bambancin SIYASA da aikin siyasa. Dan siyasa shi ne yake neman mutane, ya san matsalolinsu ya dauki matakin magance musu ba tare da bata lokaci ba. Idan da Annabi (SAW) bai kusanci mutane ba, ko a ce wadansu miyagu sun kange shi sun hana kowa zuwa kusa da shi, mutane nawa ne za su Musulunta?
Ma’aikatan siyasa su ne ake biyansu su tallata wanda ya biya su, su kushe duk wanda yake hamayya da dan takararsu, komai laifin dan takarar nasu, kuma komai alherin mai hamayya da dan takarar nasu.
Wannan illa ta yi nisa har ta kai masu laifi su ne suka kankane harkokin siyasa da mulki a Najeriya.
Shugaban masu kama barayi, barawo (Tafa Balogun), Alkalin Kotun Koli barawo, har da fasfo na alfarma guda hudu da kudaden kasashen waje; Yuro da Fam da Dala har da baiwar Allah Naira.
Tsofaffin shugabannin barayi, gwamnoni barayi, minitoci barayi, Sakataren Gwamnatin Tarayya barawo, shugabannin majalisar dokoki barayi.
Rahotannin Hukumar EFCC tun daga farkon kafa ta da sauran rahotanni sun tabbatar da haka; kuma ga harkallar mai ta Malabu ga bankadar kudin fansho na Abdurrashid Maina da makamantansu birjik wadanda su ne shaida kan abubuwan da suka faru a kasar nan kuma suke ci gaba da faruwa.
Ta fannin tsaro rahoton rikicin Maitatsine na Mai shari’a Anyagulu da rahoton rikicin Zangon Kataf na Mai shari’a Karibi Whyte da sauransu, uwa-uba Boko Haram da aka kasa kawo karshenta duk alamu ne na cin hanci da rashawa.
Duk mai hankalin da ya san ciwon kansa ba zai zuba ido ya harde hannuwansa yana gani irin wadannan abubuwa suna ci gaba da faruwa ba, ba tare da tunanin nemo matakan da suka dace don magance su cikin gaggawa ba.
Arzikin kasa kacokan yana hannun barayi, rashin tsaro ya fi karfin jami’an tsaro.
An dauko wanda aka daure rai-da-rai daga kurkuku ya zama Shugaban Kasa har da neman tazarce kari a kan wa’adin da Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada, wadanda suka fito da shi da daya daga cikinsu lokacin da ya yi juyin mulki ya rusa kusan komai a kasar nan. Kama daga Naira da masana’antu da matatun man fetur da wutar lantarki da Kamfanin Jiragen Sama na Najeriya da na jiragen kasa da Kamfanin Karafa na Ajaokuta da sauransu birjik. Ya rusa ilimi da kiwon lafiya da tsaro da noma da harkokin shari’a. Ya mallaka wa kansa da abokansa rijiyoyin man fetur, ya tarbiyyanci miyagun iri wadanda yake amfani da su wajen jagwalgwala duk gwamnatin da ta biyo bayan nasa.
Ko a yanzu da Shugaba Muhammadu Buhari, yake mulki irin wadannan mutane sun kewaye shi suna yi masa tarnaki da dabaibayi a yanzu, ta hanyar mukamai daban-daban musamman zababbu a matakai da dama..
Don haka ina jawo hankalin duk masu hankali da mutunci da adalci da tsoron Allah, su fito su mu hadu mu dauki matakan mangace wa kawunanmu matsalolin da aka jefa mu a ciki, domin siyasa ba hauka ba ce.
Ma’aikatan siyasa da su ake amfani wajen yin tsumbure da wuce iyakar da masu mulki suke tafkawa. ’Yan siyasa ba su da ubangida sai shugabannin siyasa da masu mulki da shugabannin al’umma; sarakuna da malaman addini.
Barayin shugabanni da makusantansu ba su fitar da zakka ba sa biyan haraji balle su taimaki makwabtansu da masu tsananin bukata. Hasali ma talakawan suke yi wa sata da kisa, bayan sun kashe kanana da manyan masana’antu da noma da kiwo, maimakon su inganta mana su jama’a su samu aikin yi su dogara da kansu.
Sun mayar da mafi yawan jama’a mabarata masu yin tumasanci, wadansu suna fajirci da shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran kayan maye da shiga kungiyoyin asiri da yin garkuwa da mutane, sakamakon barnar da ’yan siyasa masu kaki da fararen hula suke yi.
Don haka lokaci ya yi da za mu fahimci siyasa ba hauka ba ce mu fito mu nemo mafi ga kasar nan. Babu wanda zai zo daga wata kasa ya gyara mana kasarmu, kuma Allah Ya daina aiko annabawa balle mu sa ran wani annabi zai zo ya cece mu. Tunda dai an kallafa mana cewa ta hanyar siyasa da zabe ne kawai za mu iya kaiwa ga madafun iko har mu iya gyara, lokaci ya yi da za mu fara zurfafa tunani mu fahimci ina ne matsalar take, yaya za a yi mua nemo wa kasar nan mafita?
Shin jam’iyyun siyasar da muke da su, suna da akida da alkibla ko dai jam’iyyu ne da suka ginu don neman mulki da mukami a rika wandaka da dukiyar talakawa?
Muna bukatar jam’iyyu masu akida da alkibla a fannin tattalin arziki ba kawai jam’iyyun neman mulki da mukami ba. Yau sanin kowannenmu ne ba mu da jam’iyya kwaya daya da ta nuna wane tsarin tattalin arziki ta ginu a kai. Shi ya sa Jari-Hujjar da muke yi a Najeriya ko a Amurka albarka, domin su ba su lalata hukumomi da cibiyoyin gwamnati balle su mallaka wa kansu dukiyar kasa ta koma tasu daga su sai ’ya’yansu.
Daga yanzu ya kamata a fara gyaran nan domin siyasa ba hauka ba ce!
Alhaji Abdulkarim Daiyabu, Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN), Tsohon Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Ayyukan Gona ta Jihar Kano, (KACCIMA)
08060116666, 08023106666