Siyasa ba za hana ni shiga fim ba – Bello BMB
Jarumi Bello Muhammad Bello ya dade a harkar fina-finan Hausa, a yanzu dai fastocin takararsa ta cika mazabar Bassa da Jos ta Arewa a karkashin Jam’iyyar APGA. A hirar da ya yi da Aminiya ya bayyana dalilin da ya sa ya fara siyasa da kuma dalilin ya sa ya zabi Jam’iyyar APGA maimakon sauran manyan […]
Jarumi Bello Muhammad Bello ya dade a harkar fina-finan Hausa, a yanzu dai fastocin takararsa ta cika mazabar Bassa da Jos ta Arewa a karkashin Jam’iyyar APGA. A hirar da ya yi da Aminiya ya bayyana dalilin da ya sa ya fara siyasa da kuma dalilin ya sa ya zabi Jam’iyyar APGA maimakon sauran manyan jam’iyyu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Daga Ibrahim Musa Giginyu da Bashir Liman
A ’yan kwanakin nan fostocinka na fitowa takarar Majalisar Tarayya a mazabar Jos ta Arewa sun cika gari, da gaske ne ka fada harkar siyasa gadan-gadan har za ka tsaya takara?
Da gaske ne a yanzu na fada harkar siyasa gadan-gadan. Na fito takarar Majalisar Wakilai a mazabar Bassa da Jos ta Arewa, wato a Jihar Filato. Na kuma fito takarar ne a Jam’iyyar APGA, na yi hakan ne don in nuna wa jama’a samun nasarar dan siyasa ba ta ta’allaka ga jam’iyya mai ci ko rinjaye ba ne. Gaskiya da kwarin gwiwar dan takara hade da kudirori da manufofi masu kyawu su ne tushen da za su kai shi ga nasara.
Me ya sa ka zabi Jam’iyyar APGA bayan akwai wadansu kananan jam’iyyun?
Ni cikakken dan Najeriya ne wanda ya yarda da Najeriya ta kasance kasa daya, don haka Jam’iyyar APGA da ta PDP da ta APC da ma sauran jam’iyyun siyasa babu wacce ta fi wata, musamman idan manufofin jam’iyyar ba ta saba wa kundin tsarin mulki ba, sannan zan fi samu nasara a Jam’iyyar APGA saboda babu matsalolin siyasar cikin gida cikinta, duk da cewa a yanzu jama’a da dama suna so in koma wadansu jam’iyyun. Ina tare da jama’a, kuma don su zan tsaya takara.
Kana daya daga cikin manyan Kannywood, me ya ja hankalinka ka shiga siyasa?
Na taso a wurin da ba a san adalci da sanin ya kamata ba, kowane lokaci ina kallon yadda ake azabtar da jama’a, ina ganin yadda ake take hakkin mutane. Nakan ji takaici idan na ga matasa majiya karfi suna gararamba a kan tituna ba tare da aikin yi ba, sai na fada wa kaina: “Ka bar Najeriya sakamakon wani dalili, sannan ka dawo saboda wani dalili, shin za ka ci gaba da zuba idanu?” Wannan ita ce tambayar da ta rika kara-kaina a kwakwalwata, ana cikin haka sai gungun matasan mazabata suka same ni, suka fada mini suna so in tsaya takara a mazabar Bassa da Jos ta Arewa. Na so in ki amincewa saboda a lokacin ban shirya ba, duk da na amince amma ban mayar da hankalina sosai ba, bayan dattawan mazabar sun kira ni sun bukaci in tsaya takarar ne sai na ce lallai wannan batu ba na wasa ba ne, daga nan na fada harkar siyasa gadan-gadan.
Idan ka samu nasara za ka daina fitowa a fina-finai ke nan?
Wannan bai shafi fitowa a fina-finai ba, ya shafi yi wa al’umma hidima ne, don haka ba zan daina fitowa a fim ba, zan ma kara daga darajar masana’antar fina-finai ne. Idan har na zama dan majalisar tarayya babban aikina shi ne in kare al’ummar mazabata, zan kuma yi hakan da dukkan basirata.
Yawancin siyasa a Najeriya ta ubangida ce, ko kana da wani ubangida?
A’a, ba ni wani ubangida, jama’ata su ne iyayen gidana, saboda su ne suke da uwa da makarbiya a takarata, kuma su nake so in yi wa hidima, idan haka ne to jama’ata su ne iyayen gidana, ba wai wani mutum daya ba.
Baya ga haka, matasa ma suna tare da ni ba wai a mazabata ba har da jiha gaba daya. Sannan ina da kyakkyawar alaka da matasa ’yan Najeriya mazauna kasashen waje.
An ce ’yan fim suna shiga harkar siyasa ne saboda ta fi kawo kudi da sauri, shin kai ma saboda wannan dalili ya sa ka fara siyasa?
Komai dan Adam ya ce zai yi sai ka samu wadanda za su yi maka mummunar fahimta, na shiga siyasa ba don kudi ba ne, na dai gaji da kallon yadda ake danne hakki da ’yancin mutane ne, jama’a sun gaji da yadda al’amura ke tafiya, don haka ana bukatar canji mai ma’ana, sun kuma yi amannar za su samu canji ta dalilina.
A matsayinka na jarumi kuma darakta idan ka samu nasara wane ci gaba za ka samar a Kannywood?
Idan har na samu nasara zan bunkasa masana’antar, zan kuma mayar da ita ta zamani ba wai don ina harkar ba kawai, a’a, saboda tana daya da cikin masana’antu a Najeriya da ke samar da aikin yi. Idan muka bunkasa ta matasa za su samu aikin yi, sannan abinci zai wadata a kasar nan, inda zan bar wani abu da mutane ba za su taba mantawa da shi ba, al’umma mai zuwa za ta rika alfahari da ni.
Wadannan canje-canje za ka samar idan ka samu nasara?
Babban kudirina shi ne in samar da zaman lafiya ga al’ummata, ina so in ga jama’a suna zaune lafiya, su rika son juna da kuma kaunar juna, ina so a samu zaman lafiya da kuma hadin kai da kaunar juna da kuma hakuri da juna a mazabata da jihata da kuma yankina. Bayan nan sai in samar da abubuwan more rayuwa ga al’umma.