Siyasa ce ta hana tantance Amaechi – Sanata Muhammed Muhammed
Ranar Larabar nan ne Sanata Muhammed Muhammed, wanda ya taba wakiltar Bauchi ta Tsakiya a Majalisar Dattawan kasar nan ya bayyana rashin tantance tsohon Gwamnar Jihar Ribas Rotime Amaechi a matsayin salo ne na siyasa da aka sanya cikin lamarin. A cewarsa, zargin da ’yan adawa ke yi wa Rotimi Amaechi siyasa ce, kuma majalisa […]
Ranar Larabar nan ne Sanata Muhammed Muhammed, wanda ya taba wakiltar Bauchi ta Tsakiya a Majalisar Dattawan kasar nan ya bayyana rashin tantance tsohon Gwamnar Jihar Ribas Rotime Amaechi a matsayin salo ne na siyasa da aka sanya cikin lamarin.
A cewarsa, zargin da ’yan adawa ke yi wa Rotimi Amaechi siyasa ce, kuma majalisa za ta wanke shi.
Sanata Muhammed, wanda tsohon dan majalisar dattawa ne ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a Kaduna.
“ kalubale da Amaechi ke fuskanta ai siyasa ce. Kuma ita majalisar dattawa ba za ta karya dokokinta ba. Tunda dai a doka ba za ka iya hukunta mutum ba, har sai ka same shi da laifi. Saboda haka wannan sha’ani na Amaechi ai zargi ne wanda siyasa ta shigo ciki.
“Na kuma tabbatar idan aka zo majalisa za a wanke shi. Idan kuma kotu ta same shi da laifi shi ke nan sai shugaban kasa ya janye shi, ya kawo wani. Amma mu kam a wajen mu ’yan jam’iyar APC ba shi da wani laifi siyasa ce kawai ake yi, kuma za a ga bayan wannan abin insha Allahu,” inji shi.
Game da jan kafa da majalisar ke yi wajen tantance Amaechin sai ya ce “ idan kana bibiyar abin za ka ga cewa kwamitin da aka bai wa aikin binciken sun kasa zama, ma’ana sun kasa samun yawan mutanen da suke bukata domin zama, har su zauna su tattauna.
“Kuma ina zaton a cikin ’yan kwamitin akwai yan jam’iyyar adawa da ba su son a zauna, domin kada a warware. Sannan kuma ’yan majalisa ba su zauna ba a ranar Larabar nan, saboda shari’ar Shugaban Majalisa Bukola Saraki. Wannan ne ya sa ba a tantance shi ba,” inji shi.
Game da sabon Shugaban Hukumar Zabe ta kasa da Shugaban kasa ya nada, wato Farfesa Yukubu Nuhu, Sanata Muhammed ya yi masa fatan Allah ya sa zai iya rike wannan matsayi.