‘Siyasa da auratayya suka hada Hausawa da Yarbawa’
Sarkin Hausawan yankin Odi-Olowo da ke karamar hukumar Mushin a jihar Legas, Alhaji Muhammadu Sani Sa’idu Lambu, ya ce jam’iyyar APC da Hausawa ke yi tare da Yarabawa da kuma auratayya da ta shiga tsakaninsu, sun sanya Hausawa da Yarabawa sun zama tamkar jini da soka a jihar Legas. Alhaji Sani Lambu, wanda dan asalin […]
Sarkin Hausawan yankin Odi-Olowo da ke karamar hukumar Mushin a jihar Legas, Alhaji Muhammadu Sani Sa’idu Lambu, ya ce jam’iyyar APC da Hausawa ke yi tare da Yarabawa da kuma auratayya da ta shiga tsakaninsu, sun sanya Hausawa da Yarabawa sun zama tamkar jini da soka a jihar Legas.
Alhaji Sani Lambu, wanda dan asalin kauyen Lambu ne da ke karamar hukumar Tofa a Jihar Kano ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a gidansa da ke cikin yankin Mushin a Jihar Legas a karshen makon da ya gabata.
‘A da wasu sun so su kawo mana ’yar tangarda tsakaninmu da Yarabawa, amma daga bisani da kowa ya gane tashin hankali ba shi da riba, sai aka samu zaman lafiya a junanmu, kuma babban abin da ya kawo mana fahimtar juna da kauna da zaman lafiya a tsakaninmu, shi ne, siyasar jam’iyyar APC da Hausawa ke yi tare da Yarabawa. Kuma auratayya ta shiga tsakaninmu, domin akwai Hausawan da suka auri Yarabawa sannan akwai Yarabawan da suka auri ’ya’yan Hausawa. Wannan ya sa mun zama daya, komai tare muke yi ba wani bambanci,’ inji shi.
Ya ci gaba da cewa ‘Idan da a ce a sauran jihohi haka sauran kabilu suke yi da an samu zaman lafiya a kasar nan babu maganar rikicin addini da na kabilanci. Ai idan kana so ka zauna lafiya a garin da kake to ka tabbatar ka shiga jam’iyyar da mutanen garin suke yi kuma ka tabbatar ka hada auratayya da kabilar da kake zaune a cikinsu’.
Alhaji Sani, wanda ya ce ya kai kimanin shekaru 45 a yankin Odi- Olowo, ya bayyana cewa ya hau kan karagar mulki kimanin shekaru 25 da suka gabata.
A cewarsa, babbar nasarar da ya samu ita ce kawo zaman lafiya tsakanin Hausawa da Yarabawan yankin. Sai dai ya nuna takaicinsa dangane da rashin hadin kai a tsakanin Hausawa a Jihar Legas.
‘Wannan rashin hadin kan na ci mana tuwo a kwarya, domin shi ya janyo wasu suka rika yada jita-jita dangane da taron da Jonathan ya yi da sarakuna a Jihar Legas. Sarki Kabiru bai ce sarakunan Hausawa suna goyon bayan Jonathan ba, magana ya yi ta hadin kai da zaman lafiya a lokacin zabe. Saboda haka ya kamata mutane su iya bakinsu, su nisanci yada jita-jita,’ inji shi.