Siyasa da matsayin malamai a Musulunci (1)
Huduba ta Farko: Hamdala da Taslimi da Mukaddima: Bayan haka! Ya ku bayin Allah! A ’yan kwanakin nan Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi (Hafizahullah) ya yi rubutu da tsokaci game da siyasar Najeriya, inda ya ba da shawarwari da nasihohin da za su kawo wa kasar nan zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya yi kira […]
Huduba ta Farko:
Hamdala da Taslimi da Mukaddima:
Bayan haka! Ya ku bayin Allah! A ’yan kwanakin nan Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi (Hafizahullah) ya yi rubutu da tsokaci game da siyasar Najeriya, inda ya ba da shawarwari da nasihohin da za su kawo wa kasar nan zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya yi kira tare da jan hankali ga manyan jam’iyyun siyasar kasar nan wato PDP da APC da wasu daga cikin ’yan takararsu, Janar Buhari da Shugaba Jonathan cewa, domin maslahar Najeriya, ya kamata Janar Buhari da Shugaba Jonathan su hakura da takara. Domin takararsu na iya jefa Najeriya cikin hadari na tashin hankali da rudani. Ya kawo dalilansa na yin tsokacin da har ya kai ga rubuta budaddiyar wasika zuwa ga Janar Buhari da Shugaba Jonathan. To, amma fitar wannan bayani ke da wuya, sai wasu magoya bayan Janar Buhari da wasu mabiya son zuciya suka yi ca a kan Malam, mai zagi na yi, mai zambo na yi, mai habaici na yi. Har da masu tsinuwa da la’ana duk na gani kuma na karanta kuma na saurare su. Ba ma wannan kadai ba, wasu marasa kunya har cewa suka yi wai Sheikh Ahmad Gumi sai da ya sha ya bugu sannan ya rubuta wannan wasika zuwa ga Janar Buhari. Wasu kuma har tsagerancinsu da rashin tarbiyyar ya kai su ga cewa wai, Dokta Ahmad ba dan Sheikh Abubakar Gumi ba ne na halak. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Wannan wane irin zance ne na jahilci? Wannan wace irin al’umma ce muke rayuwa a cikinta da ba ta san inda ke yi mata ciwo ba?
Ya ku bayin Allah! In takaice muku labari, wallahi a cikinsu har da masu cewa wai Atiku ne ko Kwankwaso ko PDP ko Yahudawa ne suka saye Malam ya yi musu aiki. Da masu cewa wai, kuskure ne malamai su tsoma baki cikin siyasa, kamata ya yi su zuba ido su yi kallo su kame bakinsu game da siyasar kasar nan. Maganganu iri-iri na shirme da wawanci wallahi da ka saurare su, ka san mai yin su kodai jahili ne, ko mabiyin son zuciya.
Ba wani abu ya sa na zabi wannan maudu’i domin yin huduba a kai ba, illa domin in yi wa al’umma saiti a kan abin da ya kamata mu sani, shin haram ne malami ya sa baki a cikin siyasa? Shin laifi ne malamai su ba ’yan siyasa shawara a kan samar wa kasa maslaha a siyasance?
Ya ku bayin Allah! Akwai wani muhimmin bayani da wani bawan Allah Injiniya Abu Amina bin Khamis ya yi cewa:
“Wani rashin adalci sai talaka dan uwana! Wani rashin baiwa malami uzuri sai talakan Arewacin Najeriya!! Allahu Akbar!
-A lokacin da Amurka ta bada umurnin kama Dokta Ahmad Gumi a Saudiyya ta ce dan ta’adda ne, yawancin mutane sun ce malamin Allah ne shi ya sa aka yi masa wannan sharri.
-A lokacin da Dokta Gumi ya ce da a zabi Jonathan gwanda a zabi kare, kowa kabbara ya rika yi yana sa masa albarka.
-A lokacin da Dokta Ahmad Gumi yake ta nema wa Arewa mafita daga rikicin Boko Haram, duk Arewa ba mai magana sai shi, kowa na kabbara yana yaba masa yana jin dadi da farin ciki a kan abin da yake yi.
– A lokacin da Gwamna yazo masallacin Sultan Bello, Sheikh Ahmad Gumi ya gaya masa gaskiya gaba-da-gaba, a kan ya ji tsoron Allah ya sa a cire wa jama’a sojoji a titi, lokacin kowa kabbara ya rika yi yana jin dadi.
-A lokacin da Dokta Ahmad Gumi ya ce Fasto Ayo Oritsejafor dan ta’adda ne kuma ya yi kira da a kama shi, kowa murna ya rika yi yana jin dadi.
Allahu Akbar!
– A yau Dokta Ahmad Gumi ya hango wani abu mai hadarin gaske ga Arewa ya bayyana ra’ayinsa don samun maslaha, amma jama’a idonsu ya rufe saboda son Buhari! Kai, wasu ma cewa suke yi wai PDP yake yi wa aiki, duk da yace Jonathan ma bai cancanci ya fito takara ba. To, mu dai muna son Buhari, amma mun fi son malamai a kansa, domin sune suke haskaka mana hanyar da za mu samu mafita a ranar gobe kiyama.”
Ya ku ’yan uwana! A gaskiya a cikin wadannan bayanai na Injiniya Abu Amina, za mu fahimci halin mu ’yan Najeriya musamman ’yan Arewa. Kullum abin da muke so kuma muke tsammani daga malamin addini, shi ne ya fada mana abin da muke so, ya yi mana wa’azi da nasiha a kan abin da muke son ji. Duk yadda malami ya yi iyakar kokarinsa ya yi wa al’umma bayani game da addininsu da tattalin arzikinsun da siyasarsu da duk abin da ya shafi rayuwarsu tsakaninsa da Allah, matukar ba abin da suke so ba ne, to wannan malamin banza ne a gurinsu, mutumin banza ne ko ma su kira shi jahili ko malamin gwamnati ko an saye shi da kudi! To lallai maganar gaskiya ita ce, mu sani, wallahi! Babu masu cin mutuncin malamansu sai mutanen da suke sakarkaru. Sannan ya kamata mu sani, duk al’ummar da ke cin mutuncin malamanta ba za ta taba rabauta ba duniya da Lahira, Allah Ya kiyashe mu, amin.
Ya ku bayin Allah! Lallai mu sani, malamai magada Annabawa ne, kuma cin mutuncinsu ba alheri ba ne. Malamai aikinsu shi ne, su isar da nasiha da sakon Allah da ManzonSa zuwa ga jama’a game da duk abin da ya shafi rayuwarsu. Addini ne, tattalin Arziki ne, siyasa ce kai da duk abin da ya shafi mu’amalolinsu da rayuwarsu. Kuma wannan sako, za su isar da shi ne ta hanyar da duk take daidai, ba yadda mutane suke so ba. Ya yi wa mutane dadi ko bai yi musu ba, in dai har gaskiya ne to magana ta kare. Kada malami ya yi la’akari da zagin da za a yi masa a kan gaskiyar da zai fada, ko kisa ko dauri. Duk wannan abu ne da zai iya faruwa a gare shi kamar yadda ya faru ga Annabawa da Manzanni (AS)B da malamai salihai da suka gabace mu. Malamai sun kasance magada Annabawa ne ba domin komai ba sai don ilimin da suka gada daga Annabawan da isar da ilimin zuwa ga al’umma da daukar dukkan wahalhalun da za su biyo bayan isar da ilimin.
Babban malamin tauhidi da akida mujaddadi Sheikh Muhammad Bin Abdulwahab, ya yi wani bayani da yake kunshe da dimbin ilimi a littafinsa mai albarka, Al-Usulus Salasa inda ya ce:
“Ka sani – Allah Ya tausaya maka ya kai dan uwa! – Lallai yana wajaba a gare mu mu san wasu mas’aloli guda hudu. Na farko: Ilimi. Na biyu: Aiki da shi. Na uku: Yin kira da ilimin zuwa ga Allah. Na hudu; Yin hakuri da duk abin da zai same ka a cikin da’awar nan da yada ilimin.”
Ya ku bayin Allah! Wannan shi ne tafarkin Annabawa da Manzanni da duk malaman da suka amsa sunansu na agada Annabawa.
Kuma lallai ku sani, wallahi zancen cewa wai kada malamai su tsoma baki cikin siyasa, wannan zancen banza ne, wannan maganar ba masu fadarta sai jahilai. Kuma wallahi ba ta da tushe, ba ta da asali balle makama. dan uwa, bari in tambaye ka, shin don Allah ka taba jin wani Kirista ya ce da Fasto, ko Bishop ko wani Rabaran fada, ya cire bakinsa cikin siyasa da al’amurran da suka shafi rayuwar mutanensa? Wannan na daya daga cikin makirce-makircen Turawan mulkin mallaka da suka yi sanadiyyar mayar da malamai saniyar ware suka zama kaskantattu a cikin al’umma. Annabi (SAW) da Sahabbansa sun koyar da al’umma siyasa. Sannan a nan yankinmu na kasar Hausa da kewaye, Mujaddadi Shehu Usman dan Fodiyo da kanensa Abdullahin Gwandu da dansa Muhammadu Bello, sun yi siyasa kuma sun bar mana taskokin rubuce-rubuncensu na ilimin siyasa. Amma don rainin hankali sai mu Musulmin Najeriya mu ce da malamanmu ai babu ruwanku da siyasa, kada ku sa kanku cikin siyasa. Domin mu a nan kasar har fastoci da bishop-bishop da rabaran fada muke da su wadanda suka yi takarar Shugaban kasa da Gwamna da shugaban karamar hukuma da kansiloli. Akwai wadanda suka yi takara kuma suka ci zabe. Amma ba za ka taba jin Kiristoci ’yan uwansu sun ce musu su cire hannu cikin siyasa ba. Idan ka ji wannan rainin wayon, to daga Musulmi ne, kuma jahilai daga cikinsu da ba su fahimci addininsu da rayuwarsu ba.