Siyasa da matsayin malamai a Musulunci (2)
Su ne wadanda suke yi wa malamai kallon gidadawa, jahilai da ba su san komai ba. Masu irin wannan gurgun tunani da gurguwar fahimta, su sani karyarsu ta sha karya. Malamin Musulunci a yau, ya canza daga inda suke kallonsa a da, domin shi ilimi ba kayan gadon gidansu kowa ba ne, kowa na iya […]
Su ne wadanda suke yi wa malamai kallon gidadawa, jahilai da ba su san komai ba. Masu irin wannan gurgun tunani da gurguwar fahimta, su sani karyarsu ta sha karya. Malamin Musulunci a yau, ya canza daga inda suke kallonsa a da, domin shi ilimi ba kayan gadon gidansu kowa ba ne, kowa na iya yin sa. Ilimin addini da na zamani kai har da ilimin siyasar da ake cewa kada malamai su sa baki a ciki, malamin addini shi zai fahimci siyasa iri biyu ce, ta shari’a da ta zamani. Saboda haka, duk wani mai ilimi da ya san abin da yake yi, ya san cewa abin da Dokta Ahmad Gumi ya yi, abu ne da ke kan hanya. Babu wani kuskure a cikinsa, sai fa idan mutum zai bi son zuciyarsa ne ba gaskiya ba. Shi dai Malam ya yi nasa, nasiha ce ya riga ya yi, shawara ce ya riga ya ba da, ya rage namu ko mu dauka ko mu yi watsi da ita.
Hakika a kasar da ba a san Allah ba, a kasar da ba a san darajar Allah ba ne, za ka ji tsagera suna cewa, shugaban addini daya bai isa ya yanke hukunci a kan wasu ba. Bai isa ya yi magana da yawun mutum sama da miliyan 160 ba. A kasar da ba a san darajar addini ba ne, ba a san darajar malami ba ne a kasar da ba abin da ake bi sai son zuciya, kasar da shugabannin addini suka zama ba su da wani girma da daraja, za a wayi gari har shugabannin addinin Musulunci da Kiristanci su kasa haduwa domin samar wa kasar shugabanni nagari.
Ya ku bayin Allah! Lallai wannan aiki da Dokta Gumi ya yi na yin nasiha ga al’umma da fada wa shugabanni gaskiya komai dacinta, aiki ne da ya gaje shi daga mahaifinsa Sheikh Abubakar Muhmud Gumi. Idan za mu iya tunawa ya ku ’yan uwa, babu wata gwamnati da aka kafa a kasar nan face da hannun mahaifin Dokta Ahmad Gumi wajen kafa ta. Tun daga mulkin Tafawa balewa da Sardauna a Arewa har zuwa lokacin da Allah ya karbi ransa, babu wata gwamnati ta soja ko ta farar hula, Musulmi ke mulki ko Kirista, face Malam Abubakar Mahmud Gumi ya yi nasiha zuwa gare ta, ya ankarar da ita a kan kura-kuranta ko da kuwa mutane ba su so hakan ba. Sheikh Abubakar Gumi (Allah Ya gafarta masa), ya sha fada wa sardauna gaskiya, ran Sardauna ya baci ya yi fushi, jama’a su yi ca a kan Malam, amma da yake tsakaninsa da Allah yake yi, sai ya kafe ya tsaya a kan abin da ya fada. Daga baya idan Sardauna ya fahimci gaskiya, sai ya bi M,alam har gida ko ya kira shi ta waya ya ba shi hakuri. A duba littattafan: Sa Ahmadu Bello Sardauna: The touch Bearer da Ahmadu Bello – Sardauna of Sokoto, By John P. Paden da My Life, By Ahmadu Bello, Sardauna of Sokoto da Where I Stand, By Sheikh Gumi and Isma’ila Tsiga da Manufata na Sheikh Abubakar Gumi da Isma’ila Tsiga.
Ya ku bayin Allah! Ya zo a cikin tafsirin Alkur’ani Mai girma na Imam Ibnu Kasir (Allah Ya jikansa da rahama) ya ce: “Yayin da Manzon Allah (SAW) ya bayyana a Madina, sai wasu daga cikin malaman Yahudawan Sham suka same shi da suka kyalla ido suka ga garin Madina, sai dayansu ya ce wa dayan: “Kai, wannan birni ya yi kama da birnin da Annabin karshen zamani zai bayyana!” Bayan sun shiga wurin Annabi (SAW), nan take suka gane shi da siffofinsa da alamominsa. Suka tambaye shi, shin kai ne Muhammad? Sai ya ce eh. Suka sake cewa kai ne Ahmad? Ya ce eh. Sai suka ce to za mu tambaye ka a kan wata shaida, idan har ka ba mu amsa daidai, za mu yi imani da kai kuma mu gaskata ka.” Sai Annabi (SAW) ya ce ba komai ku tambaye ni. Sai suka ce: “Ka ba mu labari game da mafi girman shaida a cikin Littafin Allah. Nan take Allah (SWT) Ya saukar da cewa: “Allah Ya shaida cewa; lallai ne babu abin bautawa da gaskiya face Shi, kuma mala’i ku da ma’abuta ilimi sun shaida, cewa, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa da gaskiya face Shi, Mabuwayi, Mai hikima.” (Ali-Imran, 3:18). Da Annabi (SAW) ya karanta musu wannan aya, nan take suka musulunta, kuma suka gaskata Manzancinsa (SAW)”.
Ya ku Musulmi! Wallahi matsayin ilimi mai girma ne, kuma ilimi ba abin wasa ba ne, sannan malamai, ma’abuta ilimin, falalarsu da daukakarsu da matsayinsu mai girma ne. Wannan aya ta isa ta nuna mana matsayi da darajar malamai. Sannan game da tafsirin wannan aya, Imam Ibnu Kasir (RH) ya ce: “Allah Madaukaki Ya shaida – kuma Ya isa Ya zama mai shaida, shi ne mafi gaskiyar masu shaida kuma mafi adalcin masu adalci, kuma mafi gaskiyar zancensu – cewa, babu abin bautawa da gaskiya sai Shi. Sannan Ya gwama shaidar mala’ikunSa da ta malamai. Saboda haka wannan wani matsayi ne na musamman mai girma mai daraja da Allah Ya yi wa malamai.”
Ya ku bayin Allah! Yana daga hikimar Allah (SWT) domin Ya nuna mana matsayi da daukakar ilimi, Ya umarci AnnabinSa (SAW) cewa ya roke Shi kan Ya kara masa ilimi: “Kuma ka ce, “ya Ubangiji! Ka kara mini ilimi.” (k:20:114)
Malamai suka ce; “Da da abin da ya fi ilimi daukaka, da Allah Ya umarci ManzonSa ya roke shi wannan abin don ya kara masa.”
Malamai sai su gode wa Allah, domin shaidar da Ya yi a kansu cewa, su ne suka fi kowa tsoronSa a cikin mutane, wallahi ta ishe su abin alfahari: “Malamai ne kawai, masu tsoron Allah daga cikin bayinSa. Lallai, Allah, Mabuwayi ne, Mai gafara.” (Fadir:28).
Ya ku bayin Allah! Wallahi ku sani, Musulunci addini ne da ba ya wasa da ilimi da masu ilimi. Domin ilimi, musamman na addini, shi ne tafarkin sanin Allah. Ta hanyarsa ne dan Adam zai san yadda zai kadaita Allah a cikin bautarsa, ya san yadda za a bauta maSa. Bayan haka ilimi shi ne tushen daukakar al’ummomi da ci gabansu da wayewarsu. Kuma ilimi shi ne hanyar samun arzikin dan Adam a nan duniya da kuma Lahira.
Saboda wannan matsayi da ilimi ke da shi, aya ta farko da ta fara sauka a cikin Littafin Allah, tana kira ne zuwa ga ilimi da bincike da neman sani da baiwa karatu muhimmaci. Allah Madaukaki Ya ce: “Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, Wanda Ya yi halitta. Ya halicci mutum daga gudan jini. Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne mafi karimci. Wanda Ya sanar (da mutum) game da alkalami. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.” (k: 96:1-5)
Kuma hakika Allah (swt) ya daukaka matsayin ilimi da malamai a cikin al’ummah. Allah madaukaki yace:
“…Allah Yana daukaka wadanda suka yi imani daga cikinku da wadanda aka bai wa ilimi (malamai da) darajoji masu yawa, kuma Allah Mai kididdigewa ne ga abin da kuke aikatawa.” (k:58:11)
“…Ka ce, “Ashe, wadanda suka sani, (malamai) suna daidai da wadanda ba su sani ba?” Lallai masu hankali kawai ke yin tunani”. (k: 39:9)
Sannan Annabi (SAW) ya kwadaitar da mu a kan neman ilimi kuma ya sanya shi ya zama daya daga cikin hanyoyin zuwa Aljanna. Ya zo a cikin Sahihu Muslim, Manzon Allah (SAW) ya ce:
“…Kuma duk wanda ya bi hanya domin neman ilimi, Allah zai saukake masa da shi hanyar zuwa Aljanna. Kuma mutane ba za su taru ba a cikin daki (masallaci) daga dakunan Allah, suna karanta Littafin Allah, suna yin darasinsa a tsakaninsu, face natsuwa ta sauka a gare su, rahama ta lullube su kuma mala’iku su yi musu inuwa, kuma Allah Ya ambace su a cikin wadanda suke wurinSa…” (Hadisi ne ingantacce).
Ya ku bayin Allah! Ku kalli yadda Annabinmu kuma Manzonmu abin kaunarmu, mai gaskiya abin gaskatawa (SAW) yake suranta mana matsayin ilimi da malamai, wanda rashin fahimtar wannan ne ya sanya har wai a cikin al’umma za ka iya samun masu batanci da habaici da zambo da cin mutunci da zagin malami don kawai ya yi wa al’ummarsa ko wasu shugabanni nasiha, ko ya yi wa wani nasiha a kan abin da ya fahimta na siyasar kasarmu mai albarka Najeriya. Wace irin al’ummahce wannan muke rayuwa a cikinta?