Siyasa da matsayin malamai a Musulunci (3)

Daga Hudubar: Imam Murtada Muhammad Gusau, Masallacin Juma’a na Nagazi, Okene, Jihar Kogi Amirul Muminina Umar bin Khaddabi (RA) ya ce: “Gamagarin mutane da ba malamai ba, masu bautar Allah guda dubu, su mutu shi ya fi sauki a kan mutuwar malami guda daya masanin halal da haram.” (Fadlul Ilmi Wa Adabu Talabihi Wa Turuku […]

Siyasa da matsayin malamai a Musulunci (3)
Siyasa da matsayin malamai a Musulunci (3)

Daga Hudubar: Imam Murtada Muhammad Gusau,

Masallacin Juma’a na Nagazi, Okene, Jihar Kogi

Amirul Muminina Umar bin Khaddabi (RA) ya ce: “Gamagarin mutane da ba malamai ba, masu bautar Allah guda dubu, su mutu shi ya fi sauki a kan mutuwar malami guda daya masanin halal da haram.” (Fadlul Ilmi Wa Adabu Talabihi Wa Turuku Tahsilihi Wajam’ihi, na Shekh Abu Abdullah Muhammad bin Sa’id Rislan).
Game da sharhin wannan zance na Umar (RA), Imam Ibnul kayyim (RH) yana cewa: “Abin da zancen Umar (RA) yake nufi shi ne: lallai shi malami ya kasance yana rusa duk wani gini da duk wani makirci da Iblis (Shaidan) ya gina a cikin al’umma da iliminsa da jagorancinsa, amma shi mai bauta, kansa kawai yake amfana da bautarsa.” (Miftahu Daris-Sa’adah, na Ibnul kayyim, (1/398).
Ya Salam! Yanzu ’yan uwa Musulmi, mutumin da yake da irin wannan matsayi a cikin al’umma shi ne abin zagi da ci wa mutunci?
Ku duba ku gani ’yan uwa, ko kokarin da Dokta Ahmad Gumi ya yi da sauran malamai bayin Allah, na sulhunta Sheikh Sanusi Khalil da Manjo Hamza Al-Mustapha da ire-iren wadannan ayyuka wallahi ba karamin alheri ba ne ga wannan al’umma. Amma a yau an wayi gari ire-iren wadannan kyawawan ayyuka na Malam duk an manta da su. Kuma babban abin mamaki, mai daure wa duk mai hankali da tunani kai shi ne, za ka ga mafi yawan wadanda ke zagin Malam da ci masa mutunci Musulmi ne. Shin Janar Buhari ba ya da magoya baya Kiristoci ne? To me ya sa ba su zagi Malam ba? Kuma ai wasikar da Dokta Ahmad Gumi ya rubuta ba Janar Buhari ne kawai ya rubuta mawa ba, ya rubuta irin ta zuwa ga Goodluck Jonathan. Abin tambaya me ya sa magoya bayan Goodluck Jonathan Musulminsu da Kiristocinsu ba su yi irin wannan cin mutunci ga Malam ba kamar yanda magoya bayan Janar Buhari suka yi? Wannan wane sako ne suke isarwa zuwa ga al’umma? Dole ne mu fada wa juna gaskiya, in har da gaske ne gyara muke son yi a cikin al’umma. Idan kuwa dama munafunci ne ba gyara ake so na gaskiya ba, to shi ke nan. Mu dai Allah (SWT) Ya umurce mu da yin adalci koda a kan makiyi ne: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci. Kuma kada kiyayya da wasu mutane ta dauke ku a kan ba za ku yi adalci ba. Ku yi adalci, shi ne mafi kusa ga takawa. Kuma ku bi Allah da takawa. Lallai Allah Masani ne ga abin da kuke aikatawa.” (k:5:8).
Dokta Ahmad Gumi ya sadaukar da rayuwarsa yana ta maganganu da gwagwarmaya game da al’amarin Boko Haram da ya addabi Arewa ana jin dadi ana ta kabbara, amma a yau abin al’ajabi da mamaki mutane duk sun manta da wannan, Malam a yau a wurinsu ya canja daga mutumin kirki, bawan Allah mai fadin gaskiya, jarumi, zuwa mutumin banza, kawai don ya ce kada Buhari ya yi takara.
Ya ku mutane! Rashin sanin darajar malamai ce fa ta kai mu ga har za a iya samun wadanda za su iya yin karfin halin daukar bindiga su bude wa malami wuta su kashe shi! Kamar yadda ya faru ga Sheikh Ja’afar Mahmud Adam da Sheikh Muhammad Auwal Adam Albaniy Zariya da Malam Umar dan Maishiyya Sakkwato da Malam Husaini Mayo Balwa wanda ko gawarsa ba a gani ba har zuwa yau da sauran malamai da yawa da Allah ne kadai Ya san yawansu da aka kashe a jihohin Bornob da Yobe da Adamawa da sauransu.
Ya ku mutane! Na daga daraja da matsayin malamai, Manzon Allah (SAW) ya fadi a Hadisi ingantacce cewa: “Lallai Allah da mala’ikunSa da duk wadanda suke cikin sammai da kasa hatta tururuwa a cikin raminta da kifin da ke cikin ruwa suna yin addu’a ga mai karantar da mutane alheri (malami).”
Kuma Manzon Allah (SAW) ya fadi kamar yadda Buhari da Muslim suka ruwaito cewa: “Duk wanda Allah Yake nufi da alheri sai Ya fahimtar da shi addini.”
Ya ku Bayin Allah! Wallahi da a ce wannan kadai shi ne matsayin ilimi da malamai, ban da wannan babu wata darajar da falalar, to da ya isa ya wajabta mana girmama su, mu san matsayinsu da kimarsu a tsakankaninmu.
Jagoran Annabawa, Annabi Muhammad (SAW) ya fadi a wani Hadisi hasanun cewa:
“Baya daga cikin al’ummata duk wanda ba ya girmama manyanmu, kuma ba ya tausayin kananan cikinmu, kuma bai san hakkin malamanmu ba, kuma yana daga cikin hakkin malamai a kanmu, mu girmama su, mu kaskantar da kai gare su, mu zama masu tausasa magana a gare su tare da mu’amala da su da kyakkyawar mu’amala.”
’Yan uwa a Musulunci! Lallai akwai bukatar mu sake komawa a kan maganar malamai masana a kowane lokaci, musamman a lokacin fitinu da jarrabawa, musamman manyan malamai da Allah Ya hore wa ilimi, wadanda duniya ta shaidi da iliminsu.
Ya ku mutane! Ku sani, lallai malamai mutane ne kamar kowa, ba Annabawa ba ne ko Manzanni ma’asumai da ba sa yin kuskure, to sai dai wane ne zai iya gano kuskuren, ya ce lallai abin da malam wane ya fada kuskure ne? Shin kowane jaki da doki da kare ne zai yi wannan? Kuma wace hanya ce ingantacciya ya kamata a bi idan har an gano cewa malam wane ya yi kuskure a magana ko aikinsa, idan har ya yi? Shin kowa ne zai ta jefo martaninsa zuwa ga malamin har ya kai ga cin mutuncinsa, me yiyuwa ma daga cikin masu martanin akwai mabiya son zuciya da ko rubutun da malamin ya yi ba su karanta ba, amma suna cikin masu martani?
Ta yaya idan har an gano malam wane ya yi kuskure za a gyara kuskuren a magance matsalar da hikima ba tare da cin mutunci ko bin son zuciya ba?
To, duk wannan da ire-irensa mun san cewa littattafan malamai masana suna cike da martani (Ar-ruduud) tsakaninsu. A littafan fikhu da littafan hadisi da wasunsu. Amma duk a martanin da suke yi wa juna, ba za ka taba samunsu suna kiran juna batattu ba, ba za ka taba samu suna cin mutuncin juna ba. Kai, hasali ma za ka same su ne suna kare mutuncin malami da martabarsa, tare da yi masa uzuri. Domin sun san cewa lallai cin mutuncin malami, cin mutuncin addinin Musulunci ne. Sun san cewa lallai batanci ga malami, batanci ne ga Allah da ManzonSa (SAW), domin sakon Allah da ManzonSa yake dauke da shi. Wallahi haka ya kasance magabatanmu na kwarai (Salafus-Salih) da jagororinmu shiryayyu suke mu’amalantar malami. Ba kamar mu a yau ba da ba wanda muka tsana a cikin al’umma sai malami.
Imam Zahabiy (RH) ya faddi a mashahurin littafinsa – Siyaru ‘A’lamin-Nubala’- cewa:
“Idan malami yana daga cikin manyan malamai. Kuma muka san cewa daidai dinsa ya fi kuskurensa yawa. Alherinsa ya fi sharrinsa yawa. Kuma muka san cewa malami ne mai fadin gaskiya, kuma mai kokarin son a yi gaskiya. Muka san cewa malami ne masani mai kwazo mai kokari. Muka san cewa malami ne mai son a yi gyara, malami ne mai tsantseni da gudun duniya da rashin kwadayi. Muka san cewa malami ne mai mabiya, to za mu yafe kuskurensa idan har ya yi. Ba za mu ci mutuncinsa ba. Ba za mu kira shi batacce ba. Ba za mu guje shi mu manta da ayyukansa na alheri ba. Eh, gaskiya ne, ba za mu bi shi a cikin bidi’arsa ba idan dan bidi’a ne, haka kuma ba za mu bi shi a cikin kuskurensa ba idan ya yi kuskure, amma duk da haka, ba za mu ci masa mutunci ba, hasali ma za mu yi masa fatan ya tuba daga gare su.”
Ka ji maganar bayin Allah nagartattu masu yi don Allah. Ba kamar wasu ba da malamin addini ba ya da daraja kuma ba kowa ba ne a wurinsu. Wadanda a wurinsu dan siyasa ya fi malamin addinin da yake jagorantar mutane zuwa ga Allah. Allah Ya kare mu daga bata Ya gafarta mana zunubanmu da kura-kuranmu, amin.