Siyasa da matsayin malamai a Musulunci (4)
Daga Hudubar: Imam Murtada Muhammad Gusau,Masallacin Juma’a na Nagazi, Okene, Jihar Kogi Huduba ta Biyu: Ya ku bayin Allah! A hudubar farko idan za ku iya tunawa mun tsaya a kan gabar da nake cewa lallai mu sani, malamai mutane ne, ’yan Adam ne, ba Annabawa ba ne, ba mala’iku ba ne, ba Manzanni ba […]
Daga Hudubar: Imam Murtada Muhammad Gusau,
Masallacin Juma’a na Nagazi, Okene, Jihar Kogi
Huduba ta Biyu:
Ya ku bayin Allah! A hudubar farko idan za ku iya tunawa mun tsaya a kan gabar da nake cewa lallai mu sani, malamai mutane ne, ’yan Adam ne, ba Annabawa ba ne, ba mala’iku ba ne, ba Manzanni ba ne, ba ma’asumai ba ne. Hakika suna iya yin kuskure a magana ko aikinsu. Amma inda gizo ke sakar shi ne; wane ne zai iya gano cewa malam ya yi kuskure ko bai yi ba? Idan an tabbatar da kuskuren malami wace hanya ce ingantacciya ya kamata a fuskanci kuskuren? To, ga kadan daga cikin bayanai na shari’a:
1 – Wasu daga cikin mutane, Allah Ya shirye su tare da mu baki daya, har jikinsu rawa yake, suna gaggawa wajen kokarin bincike da gano kuskuren malami domin su yada shi. Kuma wasu maganganun da ake dangantawa ga malami ko malamai, za a tarar wani lokacin karya ce. Wani lokacin, za a tarar an yi karin gishiri a cikin zancensa. Za ka ji mutum ya fito a kafafen watsa labarai yana cin mutuncin malamin addini ba kunya ba tsoron Allah. Na yi imani da Allah, Dokta Ahmad Gumi a sanin da na yi masa, ya yi nasiharsa ce tsakaninsa da Allah, ba don komai ba sai don maslahar al’umma. Kuma abin haushi, mafi yawan wadanda suke maganganun banza ga malam, ba su karanta abin da ya rubuta ba. Kama daga rubutun da ya yi na farko a kan Buhari da Jonathan, zuwa na biyu, wato wasikarsa zuwa ga Buhari, har zuwa ta uku da ya yi wasika zuwa ga Jonathan.
2 – Shin a cikin al’umma wane ne zai iya gano cewa maganar da malam wane ya fada kuskure ce ko daidai ce? Shin ko wane kare ne da doki da jaki ne zai iya wannan? Wanda har zai kai ga maganganun banza da cin mutuncin malami?
Ya ku ’yan uwa a Musulunci! Lallai Allah Mai tsarki ya fadi a cikin LittafinSa Mai girma cewa:
“…Sai ku tambayi ma’abota ambato (malamai, masana) idan kun kasance ba ku sani ba.” (k:16:43)
Lallai a cikin wannan aya akwai hujja da dalili cewa, lallai wanda ya dace a tambaya, wanda ya dace a koma gare shi a cikin mas’aloli na shari’a da mas’aloli na addinin Musulunci su ne malamai masana. Lallai idan aka ce za a iya sauraron kowa da kowa, idan aka ce kowa na iya yin sharhi da tsokaci a cikin al’amura irin wadannan, to mafi yawan sharhi da tsokacin mutane za su kasance ne a kan kuskure da jahilci. Misali, idan kai ba likita ba ne to ka bar ilimin likitanci ga likitoci. Sai fa idan ana neman fatawa ne ko matsayin shari’a a kan wani aikin likita ko wani magani na likita, to a nan ana iya dora wannan aiki ko magani a kan mizanin shari’ar Musulunci. Haka, aikin injiniyanci dole a bar wa injiniyoyi, aikin malaman addini dole a bar musu in dai har gaskiya ake so a cikin al’umma.
Abin bakin ciki, sai aka wayigari idan malamin addini ya yi magana ko aiki da ke kunshe da ilimi da hangen nesa, sai ka ga kowa yana kokarin yin sharhi da tsokaci a kai. Sai a yi amfani da wannan a ci mutuncin malami magaji Annabi Muhammadu (SAW). Kuma sanannen ne cewa addinin Musulunci ba addini ne da yake kara-zube ba, addini ne mai cike da tsari. Kuma nau’o’in ilmin shari’a suna da asalinsu da hukunce-hukuncensu da hujjojinsu da ke bukatar sai masanin hukunce-hukuncen shari’a da ya fahimci manufofinsu (makasid), wanda za ya iya ciro hukunci daga nassoshi ko maganganun malamai ne kadai ke da ta cewa.
3 – Abin da yake wajibi a Musulunci da hukunce-hukuncen shari’a idan an samu sabani a kowane wani al’amar, ibada ce, tattalin arziki ne, siyasa ce, sai a koma zuwa ga dalili da hujjar da mutum ya kawo, sai a mai da shi zuwa ga Allah da ManzonSa. Domin ta wannan ne kadai za a gane gaskiya a fahimce ta.
Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi da’a ga Allah, kuma ku yi da’a ga ManzonSa da ma’abota al’amari daga cikinku (shugabanni da malamai). Idan kun yi jayayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance kuna imani da Allah da Ranar Lahira. Wannan ne mafi alheri, kuma mafi kyau ga fassara.” (k:4:59).
Kuma Allah Ya ce: “Kuma abin da kuka saba wa juna a cikinsa, ko mene ne, to, hukuncinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan shi ne Allah Ubangijina, a gare shi na dogara, kuma zuwa gare shi nake mayar da al’amarina.” (k: 42:10)
Manzon Allah (SAW) ya ce: “…Kuma lallai duk wanda ya yi tsawon rai daga cikinku to zai ga sabani (jayayya) mai yawa, to, ina gargadinku da ku rike sunnata (tafarkina) da sunnar halifofina shiryayyu masu shiryarwa a bayana.”
Ya ku bayin Allah! Don Allah mu ajiye son zuciya a gefe, mu tsaya a kan duk abin da za mu yi mu dubi Allah. Mu san cewa za mu tsaya gaban Allah gobe kiyama. Shin mene ne laifin Dokta Ahmad Gumi a cikin wasikunsa zuwa ga Janar Buhari da Shugaba Jonathan? Yanzu a cikinmu akwai wanda yake kaunar ya ga abin da ya faru a zaben 2011 a Arewa ya sake maimaituw, don Jonathan ya fadi zabe ko Buhari ya ci zabe? Ko don Jonathan ya ci zabe Buhari ya fadi zabe? Ku tuna fa a yau irin halin da muke ciki na matsalar tsaro a Najeriya musamman a Arewa? Mene ne dalilin da ya sa mu ’yan Arewa kadai ne ke yin wannan? Mu yi ta tada hankali da kashe-kashe da kone-kone saboda siyasa? Shin za mu yi hankali mu ji tsoron Allah mu daina abin da muke yi kuwa?
Ku sani, za mu iya gwagwarmaya mu kwaci hakkinmu, mu kwato ’yancinmu ba tare da mun yi kowane irin tashin hankali ba. Ba tare da mun kone gidaje da dukiyoyin ’yan uwanmu ba. Domin a kullum wadannan tashe-tashen hankula da fittinu ba sa kara mana komai sai ci baya da tabarbarewar al’amurra. Don haka mu ji tsoron Allah, mu shiga taitayinmu.
4 – Lallai yana daga koyarwar Musulunci da karantarwar shari’a, kowa ya mika wuya ba tare da sabani ba, shi ne tsayuwa a kan hujjoji da dalilai na shari’a a kan kowane al’amari daga cikin al’amurranmu.
Allah Madaukaki Ya ce:
“Ina rantsuwa da Ubangijinka (ya Muhammad), ba za su yi imani ba, har sai sun yarda da hukuncinka a cikin abin da suka yi sabani a tsakaninsu, sannan kuma ba su samu wani kunci a cikin zukatansu ba daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamawa! (k:4:65).
Ya ku Musulmi! Yana iya yiwuwa Allah (SWT) Ya boye hikimar da ke tare da wani hukunci ko wani al’amari ga wani, amma ya bayyana wa wani. Sanadiyyar haka sai ka ga wancan ya fahimci hukuncin ko al’amarin wannan kuwa bai gane ba. To a kowane hali mumini ya samu kansa, ya wajiba gare shi ya mika wuya zuwa ga hukuncin Allah da ManzonSa. Ya fahimci hikimar ko bai fahimta ba, in dai har an ce Allah Ya ce ko Manzon Allah (SAW) ne ya ce, to shi Musulmin kwarai zai mika wuya ne ko hukuncin ya yi masa dadi ko bai yi ba. Idonsa ba zai rufe ba saboda son da yake yi wa wani abu ko wani mutum ko wasu mutane ya ki karbar wani hukuncin da ya zo domin tabbatar da abin da yake shi ne mafi zama maslaha ga al’umma. Duk wanda ya yi haka, wallahi son zuciyarsa yake bi.
Lallai muna mutukar son Janar Buhari don gaskiyarsa da amanarsa, kuma dan uwanmu ne. To, amma za mu fi fifita abin da yake shi ne mafi zama maslaha ga wannan al’umma, koda kuwa za a zage mu, za a ki mu a kan wannan babu komai, Allah Ya san manufarmu kuma zai yi hukunci tsakaninmu. Ba ma kin Janar Buhari, a’a, muna duba me zai fi zama maslaha a kasarmu ne. Idan har Janar Buhari ne mafi zama maslaha ga wannan al’umma, ga addininmu, ga kasarmu, ga rayuwarmu da zama lafiyarmu da hadin kanmu da cigabanmu, to, Allah Ya tabbatar mana da shi. Idan kuwa ba shi ne ba, to Allah Ya canja mana shi da mafi alherinsa, amin.
5 – Ya ku matsanmu! Ya ku masoya ’yan siyasa! Ina hada ku da Allah, ku dora sonku da kaunarku a kan mizanin shari’ar Allah, idan ba haka ba za ku yi da na sani duniya da Lahira. Dole ne idan har kuna son cin nasara, kuna fatan samun kyakkyawan sakamako a siyasarku, to dole ne ku saurari shawarwarin malamanku. Kada ku yarda son zuciya da son abin duniya su rude ku daga barin malamanku. Ku sani, malami dai malami ne, dan siyasa dan siyasa ne. duk al’ummar da ke fatan tsira duniya da Lahira, dole ta girmama malamanta, ba tare da fifita ’yan siyasa a kansu ba.
6 – Su kuma malamai suji tsoron Allah su kauce wa bin son zuciya sai Allah Ya taimake su a al’amurransu, koda mutane suna adawa da su. Kuma su sani, runguma tare da isar da ilimin wahayi da sakon Allah da fadin gaskiya, wajibi ne kuma amana ce a wuyansu. Allah Ya yi alkawarin gwaggwabar lada da sakamako mai girma ga wanda ke karantar da al’umma alheri.
Imam Murtadha Muhammad Gusau
Masallacin Juma’a na Nagazi Ubete, Okene, Jihar Kogi.
08038289761, imel: [email protected]