Siyasa da ’yan siyasar zamani

Masallacin Badar, Kubwa, Abuja Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman Ya tsare mu daga sharrukan kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Ina shaidawa Annabi Muhammad (SAW) bawan Allah ne kuma ManzonSa ne. Bayan haka, ya bayin Allah masu girma! Ku ji […]

Siyasa da ’yan siyasar zamani

Masallacin Sayyidina Ali da ke Afghanistan

Masallacin Badar, Kubwa, Abuja

Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman Ya tsare mu daga sharrukan kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Ina shaidawa Annabi Muhammad (SAW) bawan Allah ne kuma ManzonSa ne.

Bayan haka, ya bayin Allah masu girma! Ku ji tsoron Allah (SWT) ku sani cewa, yana daga sharuddan imanin Musulmi ya yarda cewa duk abin da yake yi mala’iku suna rubutawa. Kuma za a yi masa hisabi. Duk wanda bai yarda da haka ba, shi ba Musulmi ba ne.

 

Ma’anar siyasa a Musulunci

Abin da ake nufi da siyasa a Musulunci shi ne, tsarin shugabantar jama’a domin a kyautata halayensu, a daidaita sahunsu a kan hanyar da ta dace. Kuma a yi musu adalci, a ba kowa hakkinsa. A iya karbar hakkin mai rauni daga mai karfi mai­ zalunci. Har kowa ya fahimci cewa yin gaskiya da adalci ne yake kawo zaman lafiya.

 

’Yan siyasar zamani

Su ’yan siyasarmu na zamani suna cewa su ’yan siyasar dimokuradiyya ne ba ’yan siyasar Musulunci ba, wannan ba mafita ba ce. ldan ka yarda cewa kai Musulmi ne, kana son ka rike dukiyar jama’a ko ka shugabance su, dole ne ka yi a kan karantarwar Musulunci. Koda da wane suna ka kira siyasarka.

 

Siffofin dan takara

Asali a siyasar Musulunci ba mutum ne yake fitowa ya ce yana neman shugabancin jama’a ba. Annabi (SAW) ya hana haka. Yahudawa ne suka kawo mana wannan sharri. Yadda abin yake a Musulunci, ana zabar mutane dattijai masu kamala kamar mutum bakwai, sai su zabi wanda ya dace ya rike amanar jama’a daga nan sun gama aikinsu.

 

Siffofin wanda ya kamata ya jagoranci mutane su ne:

  1. Karfi. Dole ne shugaban jama’a ya zama mai karfi mai iya tabbatar da adalci a kan kowa. Ta yadda babu wanda zai ce ya fi karfin doka. Lokacin da aka zabi Abubakar (RA) ya shugabanci jama’a, ya yi jawabi ya ce:

“Ya ku jama’a! Ku yi min biyayya idan na bi Allah da ManzonSa…. Mai rauni a wurinku, mai karfi ne a wurina har sai na karbo masa hakkinsa. Mai karfi a wurinku mai rauni ne a wurina, har sai na karbi hakkin mai hakki daga wurinsa.”

  1. Amintacce. Dole ne mai son shugabancin jama’a ya zama amintacce a kan dukiya da rayuka da mutuncin jama’a. Domin dukiya ita ce ginshikin rayuwar jama’a. Idan aka zabi shugaban da zai yi almubazzaranci da dukiyar jama’a, lallai jama’a za su fada cikin wahala. Ko kasashen kafirai ku dubi yadda suke hukunta shugaban da suka samu ya yi almubazzaranci ko almundahana da dukiyar jama’a.

Allah (SWT) Ya fada game da siffofin wanda ya dace ya yi shugabanci.

“ ….. Lallai ne mafi alherin wanda ya kamata a dauka aiki (shi ne) mai karfi, amintacce.” (Alkasas: 26).

Matsayin shugaba a Musulunci matsayi ne na dan kwadago, mai yi wa jama’a hidima. Annabi (SAW) ya ce: “Shugaban jama’a a shi ne mai yi musu hidima.” Hakim ya ruwaito.

Mutane a Madina sun ji alamomin tashin hankali daga bayan gari. Amma a lokacin da suka fito sai suka gamu da Annabi (SAW) (a matsayinsa na shugaba) har ya je ya gano yana dawowa, ya ce musu su koma gidajensu babu komai.

Abu Muslim Alkhaulaniy ya shigo ga Mu’awiyya dan Abu Sufyan (RA) sai ya ce: “Assalamu alaikum ya kai dan kwadago!” Sai mutane suka ce masa, abin da ya kamata ka ce, “ya kai shugaba!” Sai ya ki, ya sake maimaita abin da ya fada da farko. Sai Mu’awiyya ya ce: “Ku rabu da shi. Ya fi ku fahimtar abin da yake cewa.”

Sai Abu Muslim ya ce: “Kai fa matsayinka kamar mai kiwon dabbobi ne. Idan ka kula da su da kyau, yunwa da rashin lafiya ba za su galabaitar da su ba, mai su ya ba ka lada. Idan kuma ka bari suka lalace, mai su ya yi maka ukuba.”

A duba Assiyasatus Shar’iyyah: 17

 

Hakkin mai jefa kuri’a

Wajibi ne mai jefa kuri’a ya ji tsoron Allah, ya san cewa kuri’arsa za ta iya jawo wa al’umma alheri, kuma za ta iya jawo musu sharri. Domin haka Annabi (SAW) ya yi wa aI’ummarsa bayanin wanda ya kamata su zaba. Ya ce: “Duk wanda ya sanya wani a kan al’amuran Musulmi alhali akwai wanda zai fi shi kyautata wa Musulmi. lallai ya ha’inci Allah da ManzonSa.” Hakim ya ruwaito

Ku dubi abin da sahabban Annabi (SAW) suka yi a kan zaben halifarsa. Sai da suka yi kwana uku suna darjewa. AIhali duk wanda aka zaba daga cikinsu zai iya, saboda dukansu mutanen kirki ne. Kuma da suka taru kowa na duba wa al’umma wanda zai rike amanarsu ne, ba wai shi ya samu shugabanci ba. Abubakar (RA) ya gabatar da Umar (RA) ya bayyana siffofinsa na kirki domin a fahinci lallai ya dace ya shugabanci jama’a. Shi kuma da ya mike sai ya nuna cewa babu wanda ya dace irin Abubakar (RA). Ya gabatar da hujjojin da suka gamsar dajama’a, sai suka shugabantar da shi. Sun yi iyakar kokarinsu su ga ba su ha’inci Allah da ManzonSa (SAW)ba, wajen shugabantar da wanda bai dace ba a kan Musulmi.

 

Ya dan uwa mai jefa kuri’a! Kai ma ka yi iyakar kokarinka ka kubutar da kanka wurin Allah, ta hanyar ganin ka zabi wanda ya fi kowa cancanta ga rike amanar al’umma daga cikin ’yan takara. Kada ka ha’inci Allah da ManzonSa (SAW). Koda dukansu mutane kirki ne sai ka yi kokarin gano wanda ya fi kirki.

 

Hakkin shugaban da aka zaba

Wajibi ne a kan shugaban da aka zaba ya rike amanar al’umma gaba daya. Wadanda suka zabe shi da wadanda ba su zabe shi ba, ba tare da nuna bambanci ba. Idan dai yana son Allah Ya taimake shi. Idan kuwa ya tauye hakkin wadansu saboda ba su zabe shi ba, wallahi Allah zai karya shi. Domin kujerar da ya hau da dukiyar gwamnati da ke hannunsa hakkin jama’ar ne gaba daya. Saboda haka ya ji tsoron Allah, ya yi musu adalci.

Annabi (SAW) ya ce: “Duk wanda Allah Ya ba shi kiwo (na jama’a) yana tauye musu hakkokinsu har ranar da zai mutu, wannan ko kanshin Aljanna ba zai ji ba.” Muslim ya ruwaito.

Abu Sa’id (RA) ya ruwaito Annabi (SAW) yana cewa: “Bawan da Allah Ya fi so shi ne shugaba mai adalci. Wanda Ya fi ki kuma shi ne shugaba ja’iri. (mai tauye hakkin jama’a).” Tirmizi ya ruwaito.

 

Abin da ya kamata jama’a su yi bayan zabe

Ya ’yan uwa Musulmi! Idan aka tabbatar da shugaban da bai dace ba abin da shari’a ­ta ce ku yi shi ne:

(1) Ku gabatar da ayyukan da ya wajaba a kanku na ci gaban kasa da samun zaman lafiya. Ba kone-kone da kashe-kashe da zanga-zanga ba.

(2) Ku nemi Allah (SWT) Ya karba muku hakkokinku a kansa. Allah Shi Ya san ta inda zai karya shi.

Annabi (SA W) ya ce: “Musulmin kirki shi ne wanda Musulmi suka kubuta daga sharrin harshensa da hannuwansa.” Buhari ya ruwaito.

Idan kuma an tabbatar da wanda ya dace, sai ku yi masa addu’a da fatar Allah Ya ba shi ikon sauke nauyin da aka dora masa. Sa’annan ku ba shi hadin kai, kuma a yi ta hakuri, domin babu wanda zai iya warware matsalolin jama’a gaba daya. Wadansu ayyukan ku za ku yi da kanku. Da yawa za ka ga mutane sun share kofar gida kuma sun zubar da shara a magudanar ruwa, sauro ya yi ta kyankyashe ’ya’yansa yana addabarsu, ya sanya musu cuta, kuma su yi ta zargin shugabanni.

Abdullahi dan Mas’ud (RA) ya ruwaito Annabi (SAW) yana cewa: “Lallai za ku wadansu irin shugabanni a bayana. Za su yi ta aikata abubuwan da ba ku so. Sai suka ce, ya Ma’aikin Allah! To mene ne ya kamata mu yi? Sai ya ce: “Ku ba su hakkokinsu (na biyayya), kuma ku roki Allah Ya fitar muku naku hakkokin da ke kansu.” Buhari da Musulim suka ruwaito.

A wani Hadisin Annabi (SAW) ya ce: “… Kada ka ha’inci wanda ya ha’ince ka.” Abu Dauda ya ruwaito.

 

Allah Ya daukaka Musulunci da Musulmi kuma Ya kaskantar da kafirci da kafirai, amin!