Siyasa: Hafizu Kawu ya shirya bita don tsaftace soshiyal midiya
Tsohon ɗan majalisar ya ce an shirya bitar ne domin tsaftace soshiyyal midiya a tsakanin ‘yan siyasa da magoya bayansu.
Tsohon Ɗan Majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Tarauni a Majalisar Tarayya, Alhaji Hafizu Kawu, ya shirya bita ta musamman kan hanyoyin tsaftace soshiyal midiya, a tsakanin ’yan siyasa da magoya bayansu.
Taron, wanda aka shirya ƙarƙashin “Hafizu Kawu Media Team” tare da haɗin gwiwar Majalisar Malamai ta Ƙasa, reshen Jihar Kano, ya samu halartar malamai, masana, da manyan mutane daga ɓangarorin siyasa daban-daban.
- Tinubu ya ba Ganduje da Gawuna shugabanci a Hukumar Filayen Jirage da Bankin gidaje
- Tsohon Ministan Abuja na zamanin Abacha, Janar Jeremiah Useni ya rasu
A wata hira da aka yi da shi, Hafizu Kawu ya bayyana manufar taron da amfaninsa ga al’umma.
Dalilin Shirya Bitar
Da yake magana kan dalilin shirya taron, Hafizu Kawu, ya bayyana cewa an gudanar da bitar ne domin tsaftace harkar soshiyal midiya tare da daƙile yaɗa fitina da cin zarafi.
Ya ce, “Mun yi nazari kan yadda ake amfani da soshiyal midiya wajen haddasa husuma, cin zarafi, da cin mutunci, wanda bai dace da addinin Musulunci ba.
“Don haka muka ga ya kamata mu shirya taro domin wayar da kai da kuma mu haɗa kan ‘yan siyasa da magoya bayansu.”
Hafizu ya ƙara da cewa sun gayyaci malamai irin su Sheikh Ibrahim Khalil, Dokta Aminu Ibrahim Daurawa, da Farfesa Abdallah Uba Adamu domin yin bayani kan amfanin soshiyal midiya da yadda za a yi amfani da ita cikin tsafta da fahimta.
Ra’ayin Jama’a Kan Taron
Bayan taron, Hafizu Kawu, ya bayyana farin cikin da jama’a suka yi game da bitar.
“Mutane sun nuna jin daɗinsu kan wannan tsari, kuma wasu ma sun ce da sun sani da sun halarta. Wannan ne karo na farko da aka yi irin wannan taro, inda malamai da ‘yan jam’iyyu daban-daban suka zauna tare,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa wasu sun bayar da shawarar cewa a faɗaɗa irin wannan taro a nan gaba ta hanyar gayyatar jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
Muhimmancin Taron
Hafizu ya bayyana cewa babbar nasarar taron ita ce samar da sabuwar fahimta da tsaftace harkar soshiyal midiya a tsakanin ’yan siyasa.
Ya ce, “An samu tsafta a harkar tsarin soshiyal midiya, an ƙara fahimtar juna, kuma an samu haɗin kai a tsakanin jam’iyyu daban-daban. Har ma wasu sun ce za su yi koyi da wannan a mazaɓunsu.”
Ya ƙara da cewa taron ya taimaka wajen nuna yadda za a yi adawa mai tsafta da amfani da soshiyal midiya wajen kawo gyara a mulki.
Tasirin Taron
Da yake magana kan tasirin taron a nan gaba, Hafizu Kawu, ya bayyana cewa soshiyal midiya ita ce makomar sadarwa.
“Yanzu matasa sun fi amfani da soshiyal midiya fiye da kallon talabijin. Saboda haka, dole ne a ci gaba da shirya irin wannan bita don wayar da kai da tsaftace wannan harka,” in ji shi.
Ya yi kira ga shugabanni da gidajen yaɗa labarai su haɗa kai don tabbatar da cewa ana amfani da soshiyal midiya wajen samar da fahimta da kawo ci gaba, ba wajen haddasa fitintinu ba.
Kira Ga ’Yan Siyasa Da Al’umma
Kawu, ya yi kira ga ’yan siyasa da al’umma baki ɗaya da su ci gaba da gudanar da muhawarori da taruka irin wannan domin tsaftace harkokin siyasa da sadarwa.
“Kullum samun mutane suke ƙara tsunduma a cikin harkar soshiyal midiya, don haka dole ne mu dage wajen wayar da kai,” a cewarsa.
Taron ya nuna tasirin haɗin kai da muhimmancin zumunci a tsakanin al’umma duk da bambancin siyasa, abin da zai iya zama darasi ga al’umma da shugabanni.