Siyasa ta sa aka dora wa Ewuga laifi kan rikicin Ombatse – Alumaga

A kwanakin baya ne gwamnatin Jihar Nasarawa ta fitar da takardar gwamnati kan kwamitin binciken kisan jami’an tsaro da ake zargin ’yan kungiyar Ombatse da aikatawa a jihar inda ta ambaci sunayen Sanata Solomon Ewuga da dan majalisa Joseph Kigbu da Kakakin kungiyar Zakariya Alumaga da hannu a cikin rikicin. Wakilinmu ya tauttauna da Zakariya […]

Siyasa ta sa aka dora wa Ewuga laifi kan rikicin Ombatse – Alumaga

A kwanakin baya ne gwamnatin Jihar Nasarawa ta fitar da takardar gwamnati kan kwamitin binciken kisan jami’an tsaro da ake zargin ’yan kungiyar Ombatse da aikatawa a jihar inda ta ambaci sunayen Sanata Solomon Ewuga da dan majalisa Joseph Kigbu da Kakakin kungiyar Zakariya Alumaga da hannu a cikin rikicin. Wakilinmu ya tauttauna da Zakariya Alumaga game da batun, inda ya ce siyasa ta sa aka dora wa Ewuga da Kigbu laifi:

Lokacin da aka ce kana daya daga cikin wadanda ke da hannu a cikin rikicin Ombatse yaya ka ji?
Alumaga: Kafin a fito da wannan sakamakon binciken mun riga mun san cewa za a ambaci sunayenmu don wannan shi ne niyyar Gwamna Al-Makura. Ya nuna haka ne tunda aka soma zaman saurarar koke-koken. Saboda haka bai zame mana abin mamaki ba da muka ga sunayenmu a cikin takardar sakamakon binciken. Abin da ya rage kawai mu yi yanzu shi ne mu wanke kanmu daga wannan zargi.
Ta yaya za ku wanke kanku?
Alumaga: Ba shakka ya zame mana dole mu je kotu don kamar yadda ka sani tafiya kotu ne kadai zai ba mu damar wanke kanmu daga wannan zargi da bai da tushe da gwamnatin jihar nan tare da hadin kan kwamitin binciken suka yi mana.
Me za ka ce kan zargin da sakamakon binciken ya yi muku?
Alumaga: Daga cikin zargin an ce mu muke daukar nauyin kungiyar Ombatse muna kuma ba su shawarwari. An kuma bayyana a sakamakon binciken cewa a lokacin zaman sauraren koke-koken da kwamitin binciken ya gudanar ba mu gaya wa kwamitin gaskiya ba, wai duk abin da muka bayyana a gaban kwamitin karya ne. Kuma a cewarsu an tabbatar cewa ’yan kungiyar Ombatse ne suka kashe wadannan jami’an tsaro a kauyen Alakyo.  Akwai abubuwa da dama da takardar sakamakon ke zargin mun aikata da suka ingiza rigirgimun da mu kuma muke so mu karya ta a kotu don ba gaskiya a ciki.
Kowannenku zai ji da kansa ne ko dukanku ne za ku kai karar?
Alumaga: Kamar yadda ka sani ni mai magana da yawun kungiyar Ombatse wanda ita ma ana zarginta da aikata laifin kisa, ni ne kuma har yanzu babban lauyan kungiyar. Saboda haka zan je kotu ne don wanke kaina da kungiyar Ombatse. Idan sauran wadanda ake zargi sun bukaci in tsaya musu wato Sanata Solomon Ewuga da Honorabul Joseph Kigbu, zan yi haka.
Ka ce zargin da ake yi muku cewa kuna da hannu a cikin lamarin Gwamna Al-Makura ne ke hura wutar. Me kake gani ya sa ya yi haka?
Alumaga: Kamar yadda ka sani Sanata Ewuga a halin yanzu shi ne fitaccen dan siyasa a kabilar Eggon a jihar nan. An ambaci sunansa a wannan sakamakon bincike, shi kuma honorabul Joseph Kigbu dan Majalisar Tarayya ne shi ma dan kabilar Eggon ne, a kwanakin nan ne ya canja sheka daga Jam’iyyar APC zuwa PDP. Ka ga wadannan dalilai da wasu da dama ciki har da maganar kungiyar Ombatse ta kabilar Eggon, ya sa Gwamnan ya tsaya ka’in da na’in sai da aka ambaci sunayen mu mutanen Eggon a sakamakon binciken don ya bata mana suna. Ya ki jinin al’ummar Eggon a jihar nan da kuma bambancin siyasa da sauransu ne suka sa ya aikata wannan abu. Kuma mu mutanen Eggon ne muka ba shi kuri’a mafi yawa da ya lashe zaben shekarar 2011. Na biyu kuma shi ne yadda Gwamnan ya ki ambatar sunan yayansa Mai martaba Sarkin Kwandare Alhaji Ahmadu Al-Makura a sakamakon binciken duk da cewa Fulani mayaka da aka gayyato su zo su kashe mutanen Eggon, Sarkin Kwandare ya karbe su ya ba su wurin zama inda daga nan suke tafiya kauyukan Eggon suna kashe mutane.
To me ya sa ba a ambaci sunan Ministan Watsa Labarai Mista Labaran Maku a sakamakon ba alhali dan kabilar Eggon ne?
Alumaga: Kamar yadda ka sani ba kowane mutumin Eggon ne dan kungiyar Ombatse ba, don na taba sanar da haka ga ku manema labarai a baya. Mista Labaran Maku kodayake mutumin Eggon a nan Jihar Nasarawa amma ba dan Ombatse ba ne. Bai da wata alaka da kungiyar kuma harkarsa bai shafi jihar nan sosai ba. Shi ya sa ba ka ga sunansa a wannan sakamakon binciken ba. Kuma shi mutum ne wanda bai damu da harkar kabilarsa Eggon ba, haka ya sa a koyaushe muna masa fada mu jawo hankalinsa ya san bukatar yin haka. Kuma a yanzu Allah Ya sa ya gane kuskurensa ya dawo yana kula da mutanensa.
A karshe wane kira kake da shi ga al’ummar Eggon da jihar nan baki daya?
Alumaga: Kiran da nake da shi ga al’ummar Eggon ’yan uwana shi ne kada su razana da wannan sakamakon bincike. Su yi watsi da shi don ba gaskiya a cikinsa, kuma za mu tafi kotu mu wanke kanmu nan ba da jimawa ba. Al’ummar jihar nan kuma a zauna lafiya da juna a daina fadace-fadace a kuma zabi Jam’iyyar PDP a zububbuka masu zuwa don ita ce kawai za ta iya samar musu da shugabanci nagari.  

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno