Siyasa yanzu babu wata guguwa – Magajin Rafi

Wani jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna, Alhaji Shu’aibu Rabi’u, Magajin Rafin Hayin Banki, ya yi kira ga jama’a su zabi cancanta domin guguwar siyasa ba abin da take debowa face bola. Magajin Rafin ya fadi haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya a wannan makon a Kaduna. “Game da siyasar […]

Siyasa yanzu babu wata guguwa – Magajin Rafi

Wani jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna, Alhaji Shu’aibu Rabi’u, Magajin Rafin Hayin Banki, ya yi kira ga jama’a su zabi cancanta domin guguwar siyasa ba abin da take debowa face bola. Magajin Rafin ya fadi haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya a wannan makon a Kaduna.

“Game da siyasar Kaduna wanda ga shi za mu yi zaben kananan hukomomi, muna addu’ar yadda aka fara lafiya, Allah Ya sa a gama lafiya. Kuma babban abin da zan ce shi ne mutane su duba su ga wa za su zaba da ya fi cancanta ba wai jam’iyya ba. Misali PDP ta tsayar da Alhaji Sabo Babayaro a matsayin dan takarar Shugaban karamar Hukuma wanda tsohon dan majalisa ne da aka sani sosai, kuma uba ne ga marayu. Sannan a mazabata ta Hayin Banki da ke nan Kaduna ta Arewa, PDP ta tsayar da Suleiman Khalid, kuma kowa ya san wane ne shi, mutum ne mai mutunta jama’a kuma mutum ne da zai je ya yi aikinsa na gini, ya dawo ya ga wani waje ya lalace a unguwa ya gyara da kudinsa tun kafin ya fara tunanin zai yi takara. Don haka jama’a su duba cancanta,” inji shi.

Game da zaben sak kuwa, Shu’aibu cewa ya yi, “Ko Shugaban kasa yanzu bai yarda da ita ba. Kiranmu ga jama’a shi ne a duba cancanta, cancanta ce ta sa wadansu ’yan APC suke cewa za su zabi Babayaro da Suleiman Khalid.  Maganar guguwa kuma ai babu ita yanzu. Al’umma na ji a jiki, yau man fetur ya yi tsada, abinci ya yi tsada, kudin makaranta ya kara tsada. Guguwar dama ana yi ne sakamakon ba a sani ba, yanzu kowa na yin da na sani. Ai ita dama guguwa tana debo datti ne, kuma ta debo din. Don haka mutane su natsu su zabi cancanta kawai.”

A karshe ya yi kira ga Shugaban kasa ya sani cewa alkawarin da ya yi na adalci fa Allah zai tambaye shi. “Amma a nan Jihar Kaduna ba a cewa komai. Halin da al’umma suka tsinci kansu sai dai Allah Ya kyauta tun daga ma’aikata da sarakuna da ’yan siyasa da suka yi masa wahala da masu zaben. Ina addu’ar Allah Ya nuna ranar da za mu canja wannan gwamnatin ta Jihar Kaduna da hannunmu domin al’ummar Kaduna sun gaji,” inji shi.