Siyasantar da tsaron rayukan jama’a a Jihar Taraba

Mako biyu da suka gabata ne tsohon Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya kuma tsohon Ministan Tsaro Laftana Janar Theophilus Yakubu danjuma ya fito ya yi wata katobara da bai kamata a ce dattijo irin sa ya yi ba, inda ya bukaci mutanen jihar da sauran ’yan Najeriya su daina dogaro da sojojin Najeriya wajen ba su […]

Siyasantar da tsaron rayukan jama’a a Jihar Taraba

Mako biyu da suka gabata ne tsohon Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya kuma tsohon Ministan Tsaro Laftana Janar Theophilus Yakubu danjuma ya fito ya yi wata katobara da bai kamata a ce dattijo irin sa ya yi ba, inda ya bukaci mutanen jihar da sauran ’yan Najeriya su daina dogaro da sojojin Najeriya wajen ba su kariya, maimakon haka su tashi tsaye su kare kansu.

Mun dauka Janar danjuma ya furta wannan kalami ne saboda fusata inda muka sa rai bayan ya huce zai fito ya nuna nadama, to amma maimakon haka, a ranar Juma’ar da ta gabata sai gwamnatin Jihar Taraba ta fito ta shaida wa duniya cewa ta yanke kauna daga hukumomin tsaron kasar nan, musamman sojoji don karfafa matsayin na Janar danjuma.

Takaddama a tsakanin gwamnatin Jihar Taraba da sojoji ta faro ne lokacin da Kwamandan Runduna ta Uku da ke Jos Manjo Janar Benjamin I. Ahanotu ya yi Allah wadai da kisan rashin imani da ’yan kabilar Mambila suka yi wa Fulani makiyaya da suke zaune a tsaunin Mambila. 

Tun daga wancan lokaci Gwamnatin Taraba ta fara takun-saka da sojojin tana zargin cewa suna daure wa Fulani makiyaya gindi a rikicin da ke tsakaninsu da manoma da suka fito daga kabilun yankin. 

Gaskiyar magana ita ce akasarin gwamnonin da suke mulki a jihohi irin su Taraba da ke da kabilu da yawa da addinai mabambanta sukan kasa gane cewa shugabanci ba wani abu ba ne, face iya magance sabani da rigingimun da ka iya tasowa a tsakanin kabilun da suke yi wa mulki. Ya kamata su sani da Allah zai mayar da daukacin kabilun Jihar Taraba su koma Jukun ko Kuteb ko Fulani zalla, ko Ya mayar da al’ummar Jihar Benuwai, Tibi ko Idoma ko Egede zalla, kai ko su zamo ’ya’yan mutum daya, uwa daya uba daya, tilas ne a samu sabani da rikici. Haka Allah Ya halicci dan Adam, haka dan Adam yake rayuwa, haka zai ci gaba da rayuwa. Don haka abin da ya kamata kowane shugaba ya yi shi magance wannan sabani ta hanyar sasantawa da sulhuntawa har a kai ga tabbatar da zaman lafiya da kiyaye doka. 

Batun shugaba ya karkata ga wata kabila ko wani addini a lokacin takaddama da rikicin da ke tasowa a tsakanin kabilu da mabiya addinan da suke jiharsa, alama ce ta rauni da rashin hikima da rashin iya shugabanci.

Kuma wannan gazawa ta gwamnonin irin wadannan jihohi ne suke so su dauko su dora ta a kan hukumomin tsaro wadanda suka fi kowace hukuma gudanar da ayyukansu bisa dacewa da cancanta ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba, musamman sojoji. Soja babu ruwansa da kabila ko addini ko dangantakarsa da mai jawo rikici ko zubar da jini. Yakan gudanar da aikinsa ne ba sani ba sabo.

Abin kunya ne a ce wata gwamnatin jiha ta fito ta shaida wa duniya cewa wai ta fitar da rai daga samun tsaro daga sojojin Najeriya. Idan gwamnati ko wani babban mutum kamar Janar danjuma na da korafi ba ta hanyar surutai a kafafen watsa labarai za su kai korafi kan wanda ake zargi da laifi ba. Shi kansa Janar danjuma ya san ya ajiye rigar dattako ce ya dauki ta ’yan daba ya sanya lokacin da ya yi wadancan kalamai. Domin idan hukumomin sojin Najeriya sun ki daukar matakin ladabtar da wani jami’insu da yake da tabbacin ya aikata ba daidai ba, ai tsakaninsa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari babu shamaki, ko dare ko rana zai iya ganinsa ya koka masa, me ya hana ya same shi ya shaida masa halin da ake ciki don daukar mataki a kai? Sai da ya bari jama’a sun taru wajen saukar karatu, masu hankali da marasa hankali sannan zai ce, mutane su dauki makami su kare kansu? Ina dattako a nan? Wannan hali ne na ’yan daba da bai kamata ya fito daga bakin koda mai unguwa ba, balle mutumin da ya rike mukamin Hafsan Hafsoshin Sojin kasar nan kuma ya yi Ministan Tsaro.

A bara ma Janar T.Y. danjuma yana cikin wadanda ba kunya ba tsoron Allah suka fito a karkashin kungiyar ‘Dattawan’ Kiristoci ta Najeriya suka ce wai an kaddamar da jihadin Musuluntar da kasar nan a karkashin gwamnatin Buhari.   

kila dai akwai wata boyayyiyar manufa da mutane irin su Janar danjuma suke da ita ta ganin an wargaza Arewa da Najeriya baki daya domin cimma wata muguwar manufa tasu.

Yanzu da gwamnatin Taraba ta fadi wadannan kalamai, so take a janye sojoji daga jihar domin ta ba kabilu manoma damar ci gaba da karkashe Fulani makiyaya da suke zaune a cikin dazuzzuka ba tare da suna morar komai daga gwamnatin jihar ba, balle ta tarayya?

Maitar gwamnatin Taraba ya kuma fito fili da ta nemi a cire kwamandan sojojin da ke yankin, shin kwamandan ne yake aikata laifin da gwamnatin ke zargi ko kananan sojoji da suka kunshi Kirista da Musulmi? A fahimtata idan kwamandan yana da laifi bai wuce kasancewarsa Musulmi ba, wato ana so a sallame shi daga yankin a ba kabilun jihar wadanda akasarinsu Kiristoci ne lasisin cin karensu babu babbaka a kan wadanda ake ganin abokan gaba ne wadanda akasarinsu Musulmi ne wato Fulani. Irin wannan kamfe na bata kwamandojin soji Musulmi a jihohi irin su Taraba ba sabo ba ne, an yi haka a Filato aka tilasta Shugaba Goodluck Jonathan ya cire Janar Maina daga shugabancin Runduna ta Uku da ke Jos duk da cewa shi ba Bahaushe ba ne, amma tunda Musulmi ne duk daya yake da Bahaushe. Shi ma kwamandan na yankin su danjuma ba Bahaushen ba ne, Bayarbe ne amma tunda yake Musulmi ne duk daya ne! 

Bai kamata a siyasantar da batun tsaron rayuka da lafiyar jama’a ba, balle a sanya kabilanci da nuna bambancin addini! Lokaci ya yi da gwamnonin jihohi za su daina haddasa rikice-rikice ko su rika ruruta su domin fakewa da haka suna boye gazawarsu wajen sauke nauyin da al’ummar jihohinsu suka dora musu. Kowa na sane da yadda wadannan jihohi suke gaza biyan albashi ko fansho ko garatuti ga ma’aikata da tsofaffin ma’aikatansu. Su tsaya su mangance wadannan matsaloli maimakon karfafa rikici a tsakanin talakwansu domin karkatar da hankalin jama’a daga gazawarsu. Ga al’ummar wadannan jihohi, lokaci ya yi da za su fahimci rikici da kashe-kashen rayukan da wadansu suke zuga su suke yi ba komai za su jawo musu ba, face komabaya da dada talaucewa, yayin da shugabannin da suke zuga su ke ci gaba da amfani da hakan wajen sace dukiyar jihohin nasu.