Siyasar 2015: Yaudara da fitina!

Akwai wani abu da hukumar INEC ta kudurta za ta gudanar a wannan kakar zaben na bana, in har su Jonathan ba su samu damar dage zagen ba. Tsarin shi ne, hukumar ta samar da isassun akwatinan zabuka, ta yadda har ta ware akwatin ‘yan takarar shugabancin kasa daban, kana na ‘yan majalisu shi ma […]

Siyasar 2015: Yaudara da fitina!
Siyasar 2015: Yaudara da fitina!

Akwai wani abu da hukumar INEC ta kudurta za ta gudanar a wannan kakar zaben na bana, in har su Jonathan ba su samu damar dage zagen ba. Tsarin shi ne, hukumar ta samar da isassun akwatinan zabuka, ta yadda har ta ware akwatin ‘yan takarar shugabancin kasa daban, kana na ‘yan majalisu shi ma daban.

Wannan al’amari ya yi daidai, kuma na ji dadin hakan, saboda hakan zai taka wa rubabbun mutane burki, musamman masu fakewa da Baba Buhari suna cin zabe, kuma karshe idan sun ci zaben sai ka neme su, ka rasa, wato yanzu kowa tasa ta fissheshi.
Bakar azabar da PDP da gwamnatin Jonathan ke antaya wa ‘yan Najeriya, shi ne ya sa talakan yake karbar duk wani wanda ya fito takara daga wata jam’iyyar, ko da kuwa akwai wanda ya fi wannan din cancanta da dacewa, wato dai ma iya cewa PDP da Jonathan su ne matsalar siyasar Najeriya, idan na ce PDP, to ina nufin rankatakaf din hadiman da ke cikinta.
A bangare guda kuwa, PDP da Jonathan na ta yunkurin fito da sabuwar manhajar da za ta sa a kuma dage zabukan Najeriya, sabuwar manhajar kuwa ita ce, suna fakewa wai babu sunan sababbin jam’iyyun da PDP ta bude a cikin jerin takardun kada kuri’a,
A gefe daya kuma tuni shirye – shirye suna ta ci gaba da gudanuwa akan yadda za a hana Baba Buhari tsayawa takara, wai da sunan dai har yandu ba shi da takardun sakandire, a mako mai kamawa ne dai ake tunanin alkalin da aka bai wa cin hanci zai gabatar da hukuncin karshe na shari’ar da aka shigar a gaban kotunsa; a kan wai kotun ta hana Buharin tsayawa takara saboda rashin gamsassun takardun sakandire.
A nazarin da na yi sai na gano wani boyayyen al’amari, wanda ba zan iya furta shi ba, kai tsaye saboda wasu dalilai. Wato na fahimci cewa duk wannan matsin lamba da ake yi wa Buhari da sa hannun wasu da ke gindin Buharin, wato da saninsu kuma hakan yana yi musu dadi, kuma zama su yi farin ciki idan aka kwace takara, ko ba komai dai za a iya ba su takarar, tunda su ma ai suna tunanin wuyansu ya isa yanka a siyasar Najeriya.
Tuni masana fassara siyasar nigeria suka fara fashin baki akan hanyoyi da matakan da Jonathan ke bi na ganin ya yi ta-zama akan mulki, wasu da yawa suna ganin cewa Babangida ne ke kitsa masa komai, saboda kowa ya sani cewa, Babangida gwani ne a wajen iya kitsa yaudara da kuma gadar zare. Babangida shine mutumin da ya kwace mulki a hannun Buhari, kuma shi ne wanda ya azabtar da Buhari, shi ne ya kulle Buharin. Don haka masana fassara yadda siyasar Najeriya ke gudana, suke ganin ba yadda za a yi Babangidan ya aminta a ce yau Buhari ne akan gadon mulki. Babangidan zai yi duk mai yiwuwa don ganin bukatar Buhari da ta al’ummar Najeriya ba ta kai ga samun nasara ba.
Babangida gwani ne a wajen iya yaudara duba da yadda ya gudanar da mulkinsa a lokacin soja, ana ganin yana bai wa PDP da Jonathan umarni ne a kan hanyoyin da za su bi don ganin ana ta dage zaben, idan za a iya tunawa Babangidan dai shi ne ya rushe zabukan da aka yi a zamanin mulkinsa bayan da ya amince zai mika wa farar hula mulki. Da kyar ya amince zai ba da mulkin, kuma karshe da aka yi zaben sai ya rushe shi.
Ni a ra’ayi na, zan iya cewa, ‘Babangida shi ne matsalar Najeriya da kuma matsalar Arewa,’ sannan a gefe guda ga irinsu Kanar Sambo Dasuki, wadanda da su ne Babangidan ya shimfida mulkinsa, hasali ma shi wannan Kanar Sambo din ma guda ne cikin mutane ukun da Babangidan ya tura suka kwato masa mulkin daga hannun Buharin. Allah ya kyauta!
Usman dan-Gunduman jama’are 08163055770 [email protected]

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi