Siyasar Almajirai
Akan dauki hoton al’umma daga yara, idan aka gansu a makarantu an san an hau hanyar neman ilimi da samun wayewa, amma idan aka gansu suna gararamba, su kan gagari al’umma. Yayin da yara kan zama abin da suka zama ta yadda manya suka nuna musu, da farko iyaye kan taka rawar gani a rayuwar […]
Akan dauki hoton al’umma daga yara, idan aka gansu a makarantu an san an hau hanyar neman ilimi da samun wayewa, amma idan aka gansu suna gararamba, su kan gagari al’umma. Yayin da yara kan zama abin da suka zama ta yadda manya suka nuna musu, da farko iyaye kan taka rawar gani a rayuwar ‘ya’yansu daga bisani sai malamai su shiga gaba wajen bada saiti ga al’umma baki daya, musamman malaman addini.
Tabbas hakkin iyaye ne a matakin farko su ciyar, tufatar da ba ‘ya’yan da suka haifa wajen kwana. Kafin wasu shekaru wasu ‘yaran kan dogara da kansu ko su sami makafa a wajen makwafta, inda ake kwana a sauro ko zaure.
Daga iyaye sai mutanen gari, musamman makwafta wajen sa ido da kula da yara, na karshe itace hukuma babu inda za a je sai hallaka. Wasu magabata kan nemi taimako ko shawara a wajen malamai domin darajarsu. A kwana a tashi, yaran da ake kaiwa almajirci suka koma mabarata, ba a karatun sun dogara da sa’ar tsuntsu wajen ci da sha, yayin da aka bar karatun sai rayuwar birni ta kallon fim zuwa gidajen kallo, kwallo, rike wayoyin zamani suka dauke gurbin allo a wasu lokutan, Basu da jari sai bola, nan suke samun shakatawa. Sannan su kan ci karo da kazuwa da kirci ga cuttutuka birjik. Ita kalmar almajiri a Larabci watau Al-Muhajir na nufin wadanda suka yi hijira don daukaka kalmar Allah.
Kowa yana ganin yara, kananan ba takalma a cikin tsuma ga dauda, tare da kwanuka suna bara a Arewacin kasar nan, sai su yini suna yawo da leka gidajen mutane, balle idan ka je gidan abinci, inda ake sayar da shayi, ko tsire zaka ga suna jira su suke ka ajiye kwano su dirar masa, mutum ya zama kamar angulu. Babu tabbataciyar kididdiga game da yara nawa ne suke bara, amma yaran sun wuce miliyan ashirin, daga kauyuka suka taho ci rani birane, suna nan a warwatse da sunan neman ilimi, musamman karatun allo wani tsari da aka yi karnoni ana yi, wanda aka yi watsi da tasirinsa a zamanance.
A yau akan turo yara birane don a sami saukin rayuwa, wato an mayar da tsarin kamar tsarin haihuwa, ka haifi ‘ya’ya ka turo su birni, idan sun zama mutanen kirki zasu nemi iyayensu, idan suka bujure duniya ta mallakesu.
Su zama ‘yan ga ruwa, wasu ma su zama barayi, ‘yan fashi, masu garkuwa da malamai, tsabar ba a damu da rayuwarsu ba, ana samun wasu cikin dare a masu luwadi, a sawa wasu mari. Yayin da ake zargin wasu malaman da ‘ya’yansu na yin zina da ‘yan Islamiyya da yi wa almajiransu masu kiba luwadi ko dauresu idan sun ki, a bi su da sharrin sun haukace.
Tun suna kanana sun rasa soyayya, kulawa ko shiriyar iyaye, kuma a haka zasu fuskanci wulakancin kare dangi, inda idan sun yi bara sai wanda ya ga dama zai basu dan abin da baya da amfani, kwado, kanzo, kuli-kuli ko dumame, ba abin da basu ci, kuma basu tsoron tumbinsu ya yi bindiga.
Basu da aiki sai yankan farce, shara, tallan ruwa, hidima a gidan alarama, garada basu da kima.
Zuwan demokuradiyya ya bada damar dawo da martabar almajirai kasar nan, inda da zasu hada kai su sami kamun kafar ‘yan siyasa, da sun taimake juna. Gwamnatocin da suka gabata sun agaza. Amma a halin yanzu almajirai sun kara shiga wani hali na wahala, domin sai an samu a basu, ga kasa a kanjame, me na sama ya samu da zai ba na kasa.
Amma abin dubawa shi ne su kansu massalatai an mayar da su wasu wuraren neman kudi, inda limamai sun zama manajoji, ta nan suke samun nasu, har su samu tikitin Hajji da Umara a nan. Masallatai basu zaman kansu, balle masallata. An siyasantar da addinin, ta fuskar tattalin arziki a Arewa kusan fiye da rabin mutanen sun zama mabarata, inda masu lafiya da ma’aikatan sai ka iske suna roke-roke.
Duk da haramcin bara ko maula, idan ba dole ba, wanda ya tambaya yana da hakki da wanda bai tambaya ba, matsalar ita ce idan ka yi shiru za a tsinci gawa.
Wannan tsarin na almajirci ya sami daurin gindin goyon bayan malamai da ha’incin mahukunta domin da malamai sun fito a zahiri kan cewa tsarin bara ya ci karo da tsarin Musulunci da ba haka ba.
Haka gwamnati zata iya kara kasafi don kula da dauke dawainiyyar almajirai a zamanantar da almajirci ta hanyoyi da dama. Abin tambaya shi ne wai me malaman da suke da ilimi da wayewa suka yi wajen kawo karshen wannan al’ada ta mabarata da almajirci.
Tun asali akwai malamai attajirai, wanda har yau akwai irin wadannan, sannan akwai wanda abin duniya bai dame su ba, a haka nake gani akwai malaman da zasu iya tsayawa kan gaskiya da bin duk hanyar da za a bi domin tabbatar da adalci tsakanin mutane. Don haka bai kamata a bar mabiya, sarakuna da ‘yan siyasa na yin abin da suka ga dama ba, a matsayinsu na jagororin al’umma, zasu iya bada shawara da baki, a rubuce, a radiyo da telebishin ko ma a aikace, har gobe mumbari na tasiri.
Duk da irin kudaden da ake kashewa wajen shagulgulan biki, daurin aure, bukukuwa nadin sarauta ko tura ‘ya’yan ‘yan siyasa kasashen waje don su samo ilimi. Tabbas ba abin da ya fi muhimmanci kamar a gina al’umma a tashi tare a fadi tare, almajiran suna da amfani idan da za a kafa kamfani, kuma su kansu almajiran da suka yi nasara zasu iya kafa gidauniya don ceto ‘yan uwan da suka makale a wannan tsarin na tsangaya. Takobin almajirai addu’a, kuma Allah na karbar addu’ar almajirai.
Sai an ga alama mutum zai mutu, za a iya taimaka masa da abinci ko magani, na wani lokaci, amma don ya rayu yau da gobe watau a tabbatar da ‘ya’yan talakawa na zuwa makarantu, suna samun kullawa a asibitoci yadda ya kamata, halin muhalinsu, shin suna samun tsaftaccen ruwan sha da wutar lantarki, ba a damu ba. Idan mutum ya mutu sai a zo jana’iza, a rika nuna an so a taimaka, amma rai ya yi halinsa.
Su kansu iyayen masu ilimi da jahilan ba wanda ya damu da cewa ta hanyar yakar jahilci da wayewar kai ne ake samun ingantacciyar rayuwa. Zama cikin jahilai ya mayar da masananmu jahilai, sun gaza warware matsalolin al’umma, Sannan akan tsaya kan muguwar al’ada duk da ci gaba da ya same mu. An ki a sauya, don iyaye da kakanni sun yi haka a zamaninsu, yanzu ana maganar karni na ashirin da daya fa, Tabbas iyaye, malamai, sarakuna da shugabannin siyasa sun ci amana, sun zallunci almajirai.
Komai ya faru a al’umma ya shafi iyaye, a haka ina goyon bayan a kafa dokar kula da rayuwar yara, kuma a hukunta iyaye da wakilin mutanen idan ya bar mutanen mazaba a wulakance, domin idan ba a yi haka ba wata rana almajiran nan na iya zama barazana ga dimokuradiyya ko su yi zanga-zanga gama jiha. Idan talakawa suka rasa abinci, zasu ci attajirai.
Ya wajaba a basu ilimin zamani, wasu kuma a horar dasu kan sana’o’i mabanbanta, tabbas akwai almajirai masu baiwa. Kuma idan muka lura Allah yake kula dasu shi yasa zasu kwana cikin sanyi da ruwan sama, su sha tabo da ruwan kwata, su ci garau-garau su tashi lafiya.
Abin tambaya a nan shi ne, me ya hana ‘yan majalisar da ake son su yi doka, su ka ki taimakawa da makarantu ko muhalli da kamfanoni don yaye talauci da bude masana’antu don koyawa mutane su tsaya da kafafuwansu, ai gara a koya wa mutanen kamun kifi.
Ina maganar zakka, wani abu ne da a ce ana yi yadda ya kamata, da ba haka ba, wato fitarwa yadda ya kamata da ba wanda suka dace, ba a rika kaiwa ‘yan uwa ba, ko attajirai suna sauyawa tsakanin ‘ya’yansu. Kuma ina asusun almajirai da gidauniyar marayu? Su kansu marayu da zaurawa ya kamata a basu hakkokinsu na tafiyarwa da rabon gadonsu, tare da kula da marayu ta hanyar basu shawara ta gari da dorasu a kan hanyar ilimi kafin su balaga da aurar da matan ga mazajen da zasu rike su da amana.
Rashin kula ya sa ake tunanin a gayyato wasu hukumomi masu zaman kansu ko a nemi taimakon Majalisar Dinkin Duniya duk hakan ba zai kawo gamsashiyar maslaha ba, musamman a Najeriya, inda ake cinye abincin ‘yan gudun hijira.
Mahukunta na tsoron daukar mataki don rowa da shakkar zabbubuka, masu son a haramta na ganin idan an yi haka an rasa zabe, wadanda suke son a zamanantar da almajirci sai a fake da cewa ‘yan bidi’a ne, a kowane mizani muka dauki almajirci, lokaci ya yi da zamu nemi wadanda zasu gina Arewa domin ci gaban Najeriya.
Dole malamai da ‘yan siyasa su sa baki, musamman domin iko na neman kwacewa daga mahukunta, mutane suna gab da daukar dokoki a hannayensu, inda ba ruwansu da caji ofis ko fada, maimakon a sasanta sai a dauki makami, babban makamin almajirai addu’a.
Ba zamu sami ci gaba ba sai mun rike hannayen juna mun tashi tare, mu tsira tare, mu shiryar gwargadon iko sai Allah ya shir da mu.
Buhari Daure
[email protected] Kofar Kaura, Katsina.