Siyasar Jihar Taraba ta dauki sabon salo -Yanzu an bar maganar rashin lafiyar Suntai
Hukunci da kotun koli da ke Abuja ta yanke a ranar jumu’ar da ta gabata inda ta bayar da umurin a rantsar da tsohon mataimakin gwamnan jihar Taraba Alhaji Sani Abubakar danladi a matsayin mataimakin gwamnan jihar shi ne ya kawo karshen mulkin Mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Garba Umar na shekaru biyu.Tun da Alhaji Garba […]

Hukunci da kotun koli da ke Abuja ta yanke a ranar jumu’ar da ta gabata inda ta bayar da umurin a rantsar da tsohon mataimakin gwamnan jihar Taraba Alhaji Sani Abubakar danladi a matsayin mataimakin gwamnan jihar shi ne ya kawo karshen mulkin Mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Garba Umar na shekaru biyu.
Tun da Alhaji Garba Umar ya zama mukaddashin gwamnan jhar shekaru biyu da suka wuce bai samu sakat ba daga wadansu gungun jami’an gwamnati da wadansu ‘yan siyasa wadanda saka ce sune suka fi kowa kusa da Gwamna danbaba Suntai
Alhaji Garba Umar ya fuskanci adawa da makirci dabam dabam, duk dai da nufin a sauke shi daga kan kujerar mulki, amma abun ya faskara.
Dalilan da ya sa wadannan gungun mutane suka sa Alhaji Garba Umar a gaba, inji wata majiya, shi ne, wadannan mutanen wadanda Janar T.Y. danjuma ke jagoranta ba sa son wani daga arewacin jihar ya zama Gwamnan jihar a shekarar 2015.
Wata majiya ta shidawa Aminiya cewa, tun kusan makonni biyu da suka gabara kotun koli ta Abuja ta nuna alamar za a maido da Alhaji Sani Abubakar danladi bisa mukaminsa, domin an ga ana nome harabar gida tsohon mataimakin gwamnan tare da yi wa cikin gidan kwaskwarima.
Alhaji Sani Abubakar danladi wanda kabilarsa daya ne da tsohon mukaddashin gwamna Alhaji Garba Umar, kuma garin su daya ne, shi Alhaji Sani danladi yana bacama shi kuma Alhaji Garba Umar yana sabon layi, duk dai a garin bacama.
Idan ba a manta ba Alhaji Sani danladi ya kai kara a babban kotu da ke Jalingo yana kalunbalantar tube shi daga mukaminsa da aka yi, amma bai samu nasara ba. Daga nan ne ya wuce zuwa kotun daukaka kara ta tarayya, nan ma bai samu nasara ba.
A cewar majiyar wanda ke kusa da Alhaji Sani danladi, kasancewar rashin samun nasara da na kusa da danbaba Suntai suka yi a yayin yunkurin kawar da Alhaji Garba Umar a lokuta dabam dabam, shi ya sa suka lallabo wajen Alhaji San danladi suka ja ra’ayinsa domin ya amince cewa idan suka taimake shi ya samu nasara a kotun koli shi kuma zai aiwatar musu da dukkan bukatunsu. Cikin irin bukatun shi ne ba zai yi takarar Gwamna ba, sannan kuma ya rushe duk abubuwan da shi Alhaji Garba Umar ya aiwatar a duk tsawon mulkinsa na shekara biyu.
Wadannan mutanen idan ba a manta ba, su ne a kan gaba wajen hura wutar tsige Alhaji Sani Abubakar danladi daga mukaminsa. Kuma majiyar tamu ta bayyana cewa ‘yan majalisar dokoki na kasa su uku su ma sun shiga cikin wannan lamari, inda suka yi ta kai kawo zuwa fadar shugaban kasa tare bayar da makudan kudi don ganin an cire mukaddashin Gwamna Alhaji Garba Umar daga mukaminsa
Aminiya ta gano cewa idan wadannan mutane suka kyale Garba Umar a kan mukaminsa har zuwa lokacin zabe kuma yana dan takara, to ba za su iya cim ma burinsu ba.
A cewar majiyar tamu, cire Garba Umar daga mukaminsa ta hanyar kotu ita ce kawai mafita, domin duk hanyoyin da suka bi su cire shi ba su samu nasara ba.
Majiyyar ta kara da cewa, an ciwo kan ‘yan majalisu shida daga cikin goma sha shida wadanda ke mara wa Alhaji Garba Umar baya ta hanyar sayensu da kudi masu yawan gaske.
Da isowar Alhaji Sani danladi ranar asabar, kwana daya kacal bayan hukuncin kotun koli, abun da ya fara aiwatar shi ne rushe majalisar zartawa ta jihar tare da soke nade-naden da Alhaji Garba Umar ya yi tun hawarsa mulki shekaru biyu da suka wuce. Sannan kuma ya nada Mista Timothy Katap a matsayin sakataren Gwamnatin jihar, sai kuma Malam Aminu Jika, wanda ya nada shi a matsayin shugaban ma’aikata a gidan Gwamnati.
Alhaji Sani Abubakar, wanda kotun koli ta maida shi a matsayin mukaminsa na mataimakin Gwamna, a yanzu majalisa ta amince ya hau matsayin mukaddashin Gwamnan jihar, hakan ya biyo bayan wata muhawara da majalisar dokokin jihar ta gudanar a yayin zaman da ta yi a ranar litinin da ta gabata, inda ‘yan malisar suka amince da ba shi wannan matsayi.
Wani batu da al’ummar jihar ke tambaya shi ne, yaya a yanzu ba a maganar Gwanna danbaba Suntai sai kawai gwagwarmayar neman mukami? Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa har yanzu shi Gwamna Suntai bai san abun da ke gudana a jihar ba, duk da kasancewa a gidan gwamnati yake zaune.
Kafin wannan zaman, inji wata majiya, an yi yunkurin tsige shugaban majalisar jiha, watau Mista Joshia Sabo Kente, amma da yake ya samu labarin shirin tsige shi, bai bata lokaci ba sai ya yi murabus, , wanda hakan ya sanya aka zabi Mista Mark Useni a matsayin sabon shugaban majalisa. Shi kuma Alhaji Tanko Maikarfi ya ci gaba da zama a matsayinsa na mataimakin shugaban majalisar.
Aminiya ta gano cewa wadannan mutane sun fahimci cewa muddin suka kyale Garba Umar a kan mukaminsa har zuwa lokacin zabe kuma yana dan takarar kujerar Gwamnan jihar to ba za su iya cim ma burinsu ba na ganin dan takararsu Mista Ishaku Darius ya zama Gwamnan jihar ba.
A cewar wata majiya da ke kusa da yaran Janar T.Y.danjuma, kafin a samu nasarara tunbuke Alhaji Garba Umar, Janar danjuma da mukarrabansa sun kashe miliyoyin naira.
Ga dukkan alamu dai sabon mukaddashin Gwamna Sani danladi ya soma aiwatar da bukatun Janar T.Y. danjuma na ganin dan takararsa Misata Ishaku Darius ne kawai zai tsaya a tutar jam’iyyar PDP. Wadannan alamun sun hada da lalata dukkan allunan da suke dauke da hotonan Alhaji Garba Umar wadanda aka kakkafa a gefen titunan jalingo , wadansu hotonan Garba Umar da aka lalata hade suke da hotonan shugaban kasa Jonathan. Kuma a yanzu haka motocin kamfen na dan takara Ishaku Darius suna ta karakaina a gida gwamnatin jihar da ke Jalingo.
Wani abu da kuma ya daure wa jama’a kai a jihar shi ne soke nade-naden da Garba Umar ya gudanar a lokacinsa, cikinsu kowa har na manyan sakatarori, lamarin da jama’a da dama suke ganin bai dace ba.
Kuma sabon mukaddashi gwamnan ya kafa wani kwamiti wanda zai binciki duk kwangilolin da Alhaji Garba Umar ya bayar tun hawansa, har da kudaden da gwamnatinsa ta kashe a tsawon shekaru biyu da suka wuce.