Siyasar Kano za ta iya ruguza Tinubu — Buba Galadima

Ya kamata Gwamnatin Tarayya da Shugaba Bola Tinubu su yi taka-tsan-tsan da siyasar Kano.

Siyasar Kano za ta iya ruguza Tinubu — Buba Galadima

Buba Galadima

Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya gargaɗi Shugaba Bola Tinubu kan tsoma baki a lamarin siyasar Jihar Kano.

A wata tattaunawa da ya yi a Tashar Talabijin na ARISE Galadima ya yi gargaɗin cewa idan shugaban ƙasa bai yi taka-tsan-tsan ba siyasar Kano za ta iya ruguza shi.

Buba Galadima ya ce: “Ya kamata gwamnatin tarayya da shugaban ƙasa, Bola Tinubu su yi taka-tsan-tsan da siyasar Kano domin zan iya janyo masa matsala ta fannin siyasa a jihar Kano

“Ina so in gaya wa gwamnatin tarayya, ciki har da abokina, Bola Tinubu, cewa ya kamata ya tsame hannunsa daga rikicin Masarautar Kano, idan ba haka ba zai ruguza siyasarsa.

“Ba za mu taɓa yarda da wani batu ba game da siyasar jihar kuma ina da masaniyar yadda muka yi da batun siyasar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar NPN a lokacin da nake riƙe da muƙamin shugaban matasa.

“Na san wasu jiga-jigan ‘yan siyasa a Kano ciki har da wasu attajirai da suka gana da shugaban ƙasa suna neman tsige Gwamna Abba Yusuf daga kujerarsa.

“Mutumin da na sani ya kamata a ce wayonsa ya fi haka da cewa babu abin da zai faru, ka tambaye su ta yaya aka yi ba ka ci zabe ba tunda farko.”

Galadima na wannan furuci ne bayan tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya zargi Gwamnatin Tarayya da sauraron “maƙiyan Kano” kan rikicin Masarautar jihar.

Kwankwaso ya ce suna neman rigima domin samun damar sanya dokar ta-ɓaci a jihar saboda ƙwace mulkin NNPP.

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Najeriya

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji